21/07/2025
A Arewa ne Naira dubu biyar ta Uniform ko Hijabi zai hana mace zuwa makarantar Boko ko na Addini, duk 'yan uwan Mahaifin ta babu wanda zai iya bayar da dubu 5,000 din, amma zai iya kawo Naira dubu 50,000 a matsayin gudummuwar sa idan za'a hada mata kayan 'daki na Aure na Naira dubu 600,000.
~ A Arewa ne Kudin wata ko Kudin PTA Naira 300 ko 400 zai ajiye Yaro a gida na tsawon watanni biyar, yayin da Mahaifin sa zai iya saka Recharge card na Naira 500 a wayar sa a kowane Sati.
A Arewa ne mutum zai gagara koyon sana'a (Skill) saboda lokacin koyarwar da safe ne bayan Asubah, shi Kuma sai karfe 8 yake tashi daga bacci, yana son wajen da ake koyarwa da karfe 10 ko 11 na safe, ba zai iya yin wannan sammakon karfe 5:30 ko 6 ba.
Da yamma ba zai iya zuwa ba saboda yana Filin Kwallo.
~ A Arewa ne Saurayi zai gagara Sayan Littafin Naira dubu 15,000 yaje gaban Malamai saboda baya da Kudi, amma yana rike da wayar Naira dubu 80,000 duk wata yana kashe mata Naira dubu 8,000 a Caji da Data.
A Arewa ne zaka nunawa mutane business ko wata harka ta samun Kudi amma da kyar ka samu mutum 10 cikin Dari 200 da zasu shiga su koya har suyi, sauran mutane 190 din gaba daya sun tafi da tunanin cewa ba zasu iya shiga harkar da basu gani da Idon su ba.
~ Cikin mutanen Arewa ne mutum zai gagara zuwa makaranta saboda baya da Kudin Registration amma a the same year zai iya hada Kudin aure da buge bugen rayuwa.
A Arewa ne mutum ba zai iya tashi daga Bauchi ko Kano yaje Kaduna, Sokoto ko Maiduguri koyon karatun Addini ko na Boko ko Sana'a ba saboda garuruwan sunyi masa nisa, amma zai iya tafiya Lagos ko Ibadan ko Abuja neman Kudi, aikin Kudi zai kai shi Kudu.
~ A Arewa ne mutum zai fara tambayar ka Naira nawa zai samu idan zai koyi ilimin wani abu, abinda zai samun shine babban abinda yake kallo ba ilimin ba.
Cikin mutanen Arewa ne Yaro zai dawo daga Makaranta babu wanda ya tambaye shi me aka koya musu, me aka ce suyi idan sun zo gida, Amma ana iya tambayar sa Naira nawa ya samo 😪