Jaridar Sokoto

Jaridar Sokoto Jaridar Sokoto, Muryar Al'umma. Mun kiyaye dukkan haƙƙoƙin mallaka.

Wannan shafin da sauran abubuwan da ke cikin sa waɗanda Jaridar Sokoto ta tattaro baza'a iya sake buga su, watsa su, sake rubuta su, ko sake rarraba su gabaɗaya ko ɓangarorin su, ba tare da an bayyana daga wajen mu a ka samo su ba, ko rubutaccen izini daga Jaridar Sokoto. Jaridar Sokoto na maraba da ku, ku cigaba da kasancewa tared a mu a ko yaushe dan Sanin halin da jahar Sakkwato da sauransu sassan kasar nan suke ciki.

HOTUNAN: Yadda dandazon al'umma s**a tarbi tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Sanata Aminu Waziri Tambuwal a yau juma'a, Bayan ...
14/08/2025

HOTUNAN: Yadda dandazon al'umma s**a tarbi tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Sanata Aminu Waziri Tambuwal a yau juma'a, Bayan da hukumar EFCC ta bayarda belinsa bisa zarginsa da yin sama da fadi da Naira biliyan 189.

‎A Tarihin Jihar Sokoto Ba A Taba Samun Sanatan Da Ya Yi Abinda Sanata Ibrahim Lamido Ya Yi A Shekaru Biyunsa Na Farko B...
14/08/2025

‎A Tarihin Jihar Sokoto Ba A Taba Samun Sanatan Da Ya Yi Abinda Sanata Ibrahim Lamido Ya Yi A Shekaru Biyunsa Na Farko Ba Ta Fannin Taimakon Jama'a Da Cigaban Al'ummarsa

Ra'ayin Shamsu Ibrahim

14/08/2025

KARATUN LITTAFIN KITABU ASHSHIFAH

TARE DA

SHIEKH DAWUD MUHAMMED ILLELA
(HAFIZAHULLAHU)

TSAFAR DAY:
20/02/1447.Ah
14/08/2025M

👇👇👇👇👇👇

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta damƙe tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanatan kudancin Sokoto a yanzu A...
11/08/2025

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta damƙe tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanatan kudancin Sokoto a yanzu Aminu Waziri Tambuwal bisa zargin almundahanar Naira biliyan 189bn.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yana hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) a birnin Abuja.

Tambuwal, wanda yanzu haka yake matsayin Sanata a majalisar dattawa, na fuskantar tambayoyi kan zargin fitar da kuɗaɗe daga baitul-mali ba bisa ka’ida ba, waɗanda rahotanni ke cewa sun kai kimanin Naira biliyan 189.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa EFCC ta tsare shi domin gudanar da bincike kan wannan zargi, yayin da ake ci gaba da samun ƙarin bayanai kan lamarin.

Da Dumi-DumiRahotannin dake fito mana daga Garin Marnona da ke ƙaramar hukumar Wurno anan jihar Sokoto na cewa 'yan bind...
09/08/2025

Da Dumi-Dumi

Rahotannin dake fito mana daga Garin Marnona da ke ƙaramar hukumar Wurno anan jihar Sokoto na cewa 'yan bindiga sun afkawa Garin a cikin wannan dare.

Duk da dai kawo yanzu Jaridar Sokoto bata gama tattara rahotan halin da ake ciki ba a yankin, amma dai wasu majiyoyi na cewa yan bindiga sun afkama Garin cikin daren nan.

Ku dakace mu domin samun karin bayani.

09/08/2025
Gwamnatin Najeriya ta yi hasashen za a shafe kwana biyar ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ka iya janyo afkuwar am...
06/08/2025

Gwamnatin Najeriya ta yi hasashen za a shafe kwana biyar ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ka iya janyo afkuwar ambaliyar ruwa a sassan jihohi 19 da kuma wasu wurare 76 a ƙasar ciki har da Sokoto.

Gargaɗin da aka fitar daga ma'aikatar muhalli ta ƙasar, ya buƙaci masu ruwa da tsaki da kuma mazauna yankunan da lamarin ka iya shafa da su ɗauki matakan kariya.

Hakan na zuwa ne yayin da mummunar ambaliya ta afku a jihohin Ogun da Gombe yayin da wasu jihohin da s**a haɗa da Legas da Filato da Anambra da Delta suma matsalar ta shafe su.

A cewar sanarwar, ana hasashen yankunan za su samu mamakon ruwan sama a yankunan da zai iya haifar da ambaliya daga 5 zuwa 9 ga watan nan na Agusta.

Jihohin da hasashen ya shafa sun haɗa da Akwa Ibom da Bauchi da Ebonyi da Cross River da Nasarawa da Benue da Kaduna da Katsina.

Sauran jihohin sun haɗa da Kebbi da Kano da Neja da Filato da Taraba da Jigawa da Yobe da Zamfara da Sokoto da Borno da Gombe.

Matsalar ambaliya a Najeriya ta zama ruwan dare kowace shekara wadda ke janyo asarar rayuka da salwantar dukiyoyi mai yawa.

A bara, jihohi 31 rahotanni s**a bayyana sun yi fama da bala'in ambaliya da ta shafi mutum miliyan 1.2.

HOTUNA | Sanata Imai wakiltar yankin Sokoto ta Gabas, Sanata Ibrahim Lamido ya rabawa manoman yankin sa na Gabascin Soko...
01/08/2025

HOTUNA | Sanata Imai wakiltar yankin Sokoto ta Gabas, Sanata Ibrahim Lamido ya rabawa manoman yankin sa na Gabascin Sokoto takin zamani kyauta a jiya Alhamis.

Bayanai na cewa Sanatan ya rabawa al’ummar yankin takin zamanin kyauta ne jimillar babban buhun taki Dubu biyar da dari daya ga manoman yankin na Sokoto ta Gabas.

Shin ko Sanatan yayi kokari kuwa a wannan gaɓar?

Kusa muna a comments section.

25/07/2025

MUHADARA DAKE GUDANA YANZU HAKA A GARIN ILLELA
TAREDA
SHEIKH DR. ABDULLAH YUNUS SOKOTO
DA
ALARAMMA AUWAL ADAM SOKOTO

30/01/1447
25/07/2025

25/07/2025

KARATUN LITTAFIN FIQHUL MUYASSAR
Darasi 261 Tareda
Sheikh Zakariya Suleman Illela Sokoto State Hafizahullah

Address

Sokoto

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Sokoto posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Sokoto:

Share