Nagarta News Hausa

Nagarta News Hausa Wannan shafin zai rika wallafa labaru sahihai daga wakilan mu dake jihohi daban daban

04/09/2022

GWAMNATIN JAMA'ARE TABADA DAMAR FITOWA TAKARAR KANAN HUKUMOMINTA GOMA

Amadadin ni Hayatu Nasiru Ala-burwa Gwamnan Jama'are ina sanar da kafin ka tsaya takara yak**ata kasan Dokokin zabe k**ar haka:-

-Ranar fitowa takara daga 4st Sep, 2022 zuwa 10th Sept, 2022 da kuma kamfen (na neman alummar da zasu zabeka).

-Za'ayi zaben a facebook zamu saka tabbatacin kuma chancantar yan takara ranar 11th September, 2022.

-Ranar zabe 12th September, 2022 zaayi fara zabe karfe 8 na dare, kuma a sanar da wanda yayyi nasara.

-Zaben zamu gudanar dashi local government by local government duk bayan awa daya, sai mucigaba da zabe daya bayan daya. Ko wace k**ar hukuma nada awa daya na zabe.

-Sunan partyn gwamnatyn jama'are shine JAMA'ARE FANS PARTY (JFP) GreaterJamaare. Party din mu baida alaka da wasu parties da ake siyasa dasu yanxu.

-Kowace karamar hukuma nada awa daya (1HOUR) na zabe, idan masu kula da zabe s**ayi comment da ELECTION CLOSED to ko kayi comment baya cikin lisafi sabida an riga an rufe zabe.

-Mutum zaiyi zabe tahanyar aje comment insa da A ko B.

-Idan mutum yayi comments biyu ga posting na zabe tho yazama invalid zamu soke shi cikin wa'inda s**ayi zabe.

-Idan kafito takara baka samu ba a karamar hukumar da kafito baka sake fitowa wata (one chance).

-Idan yan takara s**a wuce 2 akaramar hukuma gwamnaty zatayi sulhu tsakaninsu,

-Idan kafito takara sau biyu a wata karamar hukuma za'a dakatar da kai baki daya.

-Bandasa ra'ayin siyasa ta PDP ko APC kokuma wani party, kowa nada damar fitowa ga mai ra'ayi.

-Idan mutum yasa chin zarafi ko abinda ba dai dai ba zamu dakatar da shi daga lamarin da duk ya shafe Jamaare baki daya.

-Duk wani mai mukami na gwamnatyn jama'are tho takara ta haramta gareshi sabida yana cikin state executive council.

Kananan hukomomin sune
1. Jama'are South Local Government
2. Jama'are North Local Government
3. Sambarka Local Government
4. Birnin Hutu Local Government
5. Dorawa Local Government
6. Unguwar Kowa Local Government
7. Kofar Barka Local Government
8. Yan-Zango Local Government
9. Farin Dutse Local Government
10. Majawa Local Government

Sahannun shugaban kwamitin zabe
Mallam. Nuradeen Adam
(Hon. Commissioner Min. Of Higher Jama'are)

Wannan daya daga cikin hoton ziyayar da shugaban kasar Chadi ya kawo najeriya ne!Jim kadan Bayan rasuwar shugaban aka ay...
21/04/2021

Wannan daya daga cikin hoton ziyayar da shugaban kasar Chadi ya kawo najeriya ne!

Jim kadan Bayan rasuwar shugaban aka ayyana Dan sa a matsayin shugaban rikon kwarya da zai riqi kasar har na Tsawon watanni 18.

Me ya k**ata Sabon shugaba ya mayarwa hankali??

Har yanzu Babu Wata kwakkwarar hujja dake Nuna cewa anyi juyin mulki a kasar chadi Jim Kadan Bayan rasuwar shugaban kasa...
21/04/2021

Har yanzu Babu Wata kwakkwarar hujja dake Nuna cewa anyi juyin mulki a kasar chadi Jim Kadan Bayan rasuwar shugaban kasar Idris Derby Itno wasu ke yawo da wani faifan video na Harbin bindiga!

Zamu ci gaba da bibiyar lamarin tare da kawo muku hakikanin bayanai

Gwamnatin Jhar Kano Karkashin Jagoranci Gwamnan jahar Dr Abdullahi Umar Ganduje ta aminta da yin mukabala wato tattaunaw...
07/02/2021

Gwamnatin Jhar Kano Karkashin Jagoranci Gwamnan jahar Dr Abdullahi Umar Ganduje ta aminta da yin mukabala wato tattaunawar keke da jeke tsakanin Abduljabbar da sauran Malaman Addinin Islama

sai dai ya zuwa yanzu gwamnatin jahar bata sanarda ranar yin mukabalar ba.

Kuci gaba da bibiyar wannan shafin domin jin labarai da dumu duminsu

A yau ne aka daura auren matashin nan dan jahar Kano da baturiyar Amaryarsa!Menene Ra, ayinku akan wannan Aure
13/12/2020

A yau ne aka daura auren matashin nan dan jahar Kano da baturiyar Amaryarsa!

Menene Ra, ayinku akan wannan Aure

Kotun sauraron ƙararrakin zabe a Jihar Neja, ta soke zaben kujerar ɗan majalisar wakilai na tarayya a yankin ƙananan huk...
22/09/2020

Kotun sauraron ƙararrakin zabe a Jihar Neja, ta soke zaben kujerar ɗan majalisar wakilai na tarayya a yankin ƙananan hukumomin Magama da Rijau.

Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a B.F Zubairu ta yanke hukuncin ne a jiya litilin a Minna babban birnin Jihar ta Neja, sak**akon ƙarar da ɗan takarar jam'iyar PDP Hon. Ema Alamu ya shigar inda yake ƙalubalantar ɗan majalisar ƙarƙashin jam'iyar APC Hon. Kasimu Ɗanjuma Majas. Da gabatar da takardun bogi ga hukumar zabe.

Kotun wacce ta zartas da hukuncin, tare da baiwa hukumar zabe ta ƙasa umarnin sake zaben cikin kwanaki 90. Ta kuma haramtawa jam'iyar APC da ɗan takarar ta shiga zaben.

Saidai jam'iyar ta APC ta nuna rashin gamsuwar ta, inda tace baza ta sabu ba, domin ta na da ja dangane da hukuncin, wacce ta ce zata ɗaukaka ƙara a kotu na gaba.

Minene Ra, ayinku akan wannan Auren na Malam Ali na cikin shirin Kwana Casa, in????
12/04/2020

Minene Ra, ayinku akan wannan Auren na Malam Ali na cikin shirin Kwana Casa, in????

A sanyin safiyar ranar Laraban data gabata ne mazauna unguwar Galdimari dake karamar hukumar Akko a Jihar Gombe, s**a wa...
03/04/2020

A sanyin safiyar ranar Laraban data gabata ne mazauna unguwar Galdimari dake karamar hukumar Akko a Jihar Gombe, s**a wayi gari cikin rudani sak**akon gawar wata mata da aka gani a gefen t**i.

Matar wadda ba a gano musabbabin mutuwarta ba, an gano gawar ce a bayan wani shagon langalanga na kafinta a dab ta t**in ratse da akafi sani da bye-pass na jihar Gombe.

Daga Sam'an Ibrahim

Rundunar 'yan sandan Sokoto da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 22 ranar Lar...
02/04/2020

Rundunar 'yan sandan Sokoto da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 22 ranar Laraba a harin da s**a kai a wani kauye da ke jihar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mohammed Abubakar Sadiq, wanda ya shaida wa BBC wannan labari, ya kara da cewa 'yan bindiga, wadanda s**a kai harin a kauyen Gangara da ke karamar hukumar Sabon Birni, sun kuma jikkata mutane da dama.
Ya kara da cewa 'yan bindigar sun yi kokarin yi wa dakarun soji da jami'an 'yan sandan da s**a je kauyen domin fafarar su, ko da yake ba a kashe jami'in tsaro ko da daya ba.

Madogara BBC HAUSA

Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce wasu mutum hudu sun sake kamuwa da coronavirus a kasar.A cikin wani ...
24/03/2020

Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce wasu mutum hudu sun sake kamuwa da coronavirus a kasar.
A cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter, NCDC, ta ce uku daga cikin mutum hudun a birnin Legas suke gudan kuma a Abuja babban birnin tarayyar Najeriyar.
Kazalika mutum daga cikin mutum hudun sun dawo Najeriya ne daga tafiyar da s**a yi zuwa kasashen waje.
Ya zuwa yanzu dai wadanda s**a kamu da annobar ta coronavirus sun kai arba'in a Najeriya.

Madogara BBCHAUSA

Rundunar sojin kasa ta 7 division ta ce tagano wassu mutane guda 10 wadanda ke safaran kayayyakin abinci dana masarufi d...
23/03/2020

Rundunar sojin kasa ta 7 division ta ce tagano wassu mutane guda 10 wadanda ke safaran kayayyakin abinci dana masarufi daga Maiduguri zuwa ga 'yan kungiyar BokoHaram dake a dajin Sambisa.
Babban komandan rundunar sojin kasa ta 7 division kuma shugaban rukuni na 1 na rundunar operation lafiya dole, brigediya janar Abdul Khalifa Ibrahim ne ya bayyana hakan a yayinda rundunar ke kona wassu motoci guda 6 data k**a na masu taimakawa 'yan BH din da kayayyaki daban-daban wanda zasu kaiwa 'yan BH din a maboyarsu.

A Jihar katsina ma'aikar lafiya ta jihar ta tabbatar da cewa babu cutar coronavirus da ake zargi ta k**a wani mutum a ji...
19/03/2020

A Jihar katsina ma'aikar lafiya ta jihar ta tabbatar da cewa babu cutar coronavirus da ake zargi ta k**a wani mutum a jihar.

Kamar yadda kwamishinan ma'aikatar Yakubu Nuhu Danja ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da manema labarai a ofishin sa.

Kwamishinan lafiya na jihar Katsina kenan yayin da yake musanta samun cutar coronavirus a Katsina.

Governor Aminu Waziri Tambuwal ya bayarda umurnin rufe daukacin Makarantun dake jihar nan na tsawon kwanakki 30. Daga Mu...
19/03/2020

Governor Aminu Waziri Tambuwal ya bayarda umurnin rufe daukacin Makarantun dake jihar nan na tsawon kwanakki 30.

Daga Musa Yusuf Sanyinna

Rufe Makarantun dai zai soma ne tun daga ranar litinin ta makon gobe.

Matakin rufe Makarantun ya biyo bayan wani taro da gwamnonin arewa s**a gudanar jiya a kaduna
inda aka amince a rufe Makarantu a jihohi tara na arewa da s**a hada da sokoto, da Kebbi da Zamfara da kano da katsina da kaduna da jigawa da kwara da Kuma kogi.

Kwamishinan ilimin furamare da sakandare na jihar nan Bello Abubakar Guiwa wanda ya sanarda umurnin rufe Makarantun, yace matakin nada manufar hana yaduwar cutar Corona dake cigaba da yin barazana a duk fadin duniya.

Address

Runjin Sambo
Sokoto

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nagarta News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share