11/12/2021
BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNA TAMBUWAL NA SAKKWATO:
Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai!
Yabo da godiya su kara tabbata zuwa ga Baban Kasim Muhammadu Rasulullah S.A.W.
Na jima banyi rubuta kan Jihar mu ta sakkwato ba, amma yau kam abin ya zama dole.
Yau Kam, tsumangiyar ta kan hanya ce...
Ina son Magana kan kasawar Gwamna Tambuwal ga daukar matakin da ya dace kan Matsalar tsaron da sokoto ke fama da ita.
Wato su dai yaran PDP a sakkwato, da zaran aka ce musu Gwamna Tambuwal na da laifi na kin daukar mataki kan matsalar tsaron da sokoto take fuskanta kawai sai su taso suna habshi.
Wallahi, wallahi, ko ku yi habshi ko kuma mak**ancin haka, Matawalle shi ne Gwamna, kuma dole a laka masa laifin kin daukar matakin da ya dace.
Yau shekaru biyu da ya je fadar gwamnatin Nijeriya neman taimakon a taimaka Masa kan matsalar tsaro, amma bai sake take kafar sa can ba da sunan wannan maganar ba, tunda a koda yaushe muna kallo TVs.
Shin, baya dubin sauran takwarorin sa irin su, zulum, Matawallen Maradun, Hope uzodinma, Wili Obiano da sauran su?
Da zarar aka taba jihohin su wallahi sun k**a safa da marawa ke nan har Sai shugaban kasa Buhari ya dauki matakin da ya dace.
To amma shi Gwamnan sakkwato saboda Sheri da adawar da yake yi da Gwamnatin tarayya sai ya dawo sakkwato ya tobake yana gurnanin banza da wofi!
To ka Sani ko ka tashi tsaye ka yi abinda ya dace ko kuma ka kara fuskantar matsalar Cikin gida wallahi dole kasan ta yi.
Ka je sabon Birni jiya Alhamis ka ce wai ka rabawa Jami'an tsaro Motoci Dari biyar da babura Dari biyar, Dan Allah sakkwatawa Ina son sanin gaskiyar wannan lamarin, idan ba cuta cikin Wannan maganar?
Shin wadannan Motoci da ya ce ya raba, sun Kai Dari biyar? Sanann Anya ba gyara ne ba? Gyararrun Motoci na aikin Samar da tsaro ingantaccen?
Sai ka ce wai baka da control ga Jami'an tsaro, Amma jiya waya baka damar tara su gaba daya kuka je sabon Birni?
Shi zulum dake fita tare da Buhari ne ya sauka Borno ya jagoranci sojoji zuwa d
BRT MEDIA