30/08/2026
Kwamitin Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), mai Cibiyar Gudanarwa ta ƙasa a Birnin Jos, Reshen Jihar Sakkwato, Ƙarƙashin Jagorancin Jameel Ibrahim Shugaban Kwamitin na jahar Sakkwato, ya gudanar da taron bita a Aliyu Magatakarda Wamakko ICT Center da ke Sakkwato.
An gudanar da taron ne domin ƙara wa mambobin kwamitin ilimi da ƙwarewa kan yadda ya kamata a riƙa yaɗa sahihan bayanai, tare da jaddada muhimmancin gaskiya da amana wajen isar da saƙonni ga al’umma.
Adam M Darhela
Deputy Chairman Jibwis Internet Media Committee Bodinga Local Government