27/02/2024
ππππππ
WANNAN SHI AKE KIRA DA KHADIMUL ISLAMA.
Ko shakka babu wannan bawan Allah HON NASIRU SHEHU BODINGA (Bobo) ya chanchanchi a kira shi da Khadimul Islama, duba da yadda yake hidima ga addinin Allah babu dare babu rana, a duk lokachin da aka sanarda shi wani aikin Allah to hakika sai inda karfin shi ya kare,
Kadan daga cikin abinda zan iya tunawa shine
β Ya bayarda gudunmuwa sabuwar mota ta 6 Million ga Kungiyar IZALA reshen Kaduna da kuma #500,000 na shan Mai domin a isar da sakon Allah.
β Ya sake bada gudunmuwa sabuwar mota ta 6 Million ga Kungiyar IZALA reshen JOS karamar hukumar mulkin Bodinga da kudin Mai #500,000 domin su isar da sakon Allah.
β Ga bayarda gudunmuwa kudi #500'000 da daukar nauyin taron maulidi da zawiyyar Malam Lawali Danchadi, reshen Darikar Tijjaniyya ta Bodinga local government.
β Ya bayarda gudunmuwa kudi #500,000 da daukar nauyin taron Qadirawa Kungiyar Darikar Qadiriyya ta Bodinga local government ta shirya.
β Akwai rana daya umurchi kwamitin shi da su zagaya makarantun Islamiyya su bayarda tallafi.
β Hon Nasiru Shehu ya gina makarantar Islamiyya ta Malam Musa M Kada.
β Hon Nasiru Shehu ya gina masallachin Khasu salawat a shiyar Sama road sokoto.
β Hon Nasiru Shehu ya gina ma tsofaffi da yawa dakunan kwana bayanda ruwan damina s**ayi musu banna.
Wani abin sha'awa shine wasu lokutan baya son a asan yayi Alkhairi, yakan che shi domin Allah yayyi.
Ina da yakinin babu Dan Majalisar tarayya a jihar Sokoto da zai rika kafarsa wurin imfaqi fisabilillahi.
Hakika Bodinga Dange Shuni da Tureta munyi dachen Wakili, muna kara addu'a Allah ka kara ma bawa naka, zuciyar taimakon addini, da ma al'umma baki daya
Amin.