Lafazin so

Lafazin so Lafazin so shafine Wanda ya Sahara Wajen kawo muku zafafan littafan hausa novels da Kuma kalaman Soyayya masu nisha Dan tarwa fadakarwa hadi da Baku Nisha

15/09/2025

Maha Na Danfo

04/09/2025

Big shout-out to my newest top fans! Sani Nike Sani Nike

Gidan mu Part 16Baba Manu ne da abokinsa  Alh.Sadi s**a Faka Motarsu a kofar gidan Alhaji Alhassan, Da misalin karfe 11a...
02/09/2025

Gidan mu Part 16

Baba Manu ne da abokinsa Alh.Sadi s**a Faka Motarsu a kofar gidan Alhaji Alhassan, Da misalin karfe 11am na safe Daman yasan gidan Saboda Zama anguwa Daya da s**ayi da yayansa marigayi Mahaifin Sagir.Motar ba tashi bace ta abokinsa ne Alhaji Sadi,ba kuma Domin kawu Manu ya rasa kudin da zai sai Mota ba sai dai shi Mutum ne da baya son yana Bayyana Samunsa kudi ne dashi sosai Donin gareji na kansa gareshi da yara kuma ba Laifi yana samun Rufin asiri,sai dai kuma yana da Zuciya mai kyau ko karatun Sagir Rabinsa shike Tallafe dashi kuma Lokaci bayan lokaci yana zuwa Gidan da kuma abun Arziki ko bakomai ba zai manta da Abunda Mahaifin Sagir yayi masa Ba Duk ya kasance Yaya garesa ya kafashi shine Sanadiyar daya mallaki Garejin Dayake Tak**a dashi.Shi ya kira Alh.Sadi abokinsa ya gayamai komai ya kuma nemi Daya Rakashi,Shine ya bada kudi aka saka mai s**a Shiga kasuwa s**a Siya Kwalayrn Minti da Dabino da goro,Kawu Manu ya Rike dubu dari da Hamsi Dubu Talatin kudin nagani ina so sauran kuma na Sadaki ne.Kawu Manu ne ya Fara Fitowa Daga Motan yana gyara Zaman Babban Rigar Shaddan Dake jikinsa Saboda zuwa neman auran nan bai Fita gareji ba haka kurum yake so ya Taimaki Imran bai san Dalili ba.Wajen megadi ya nufa Yayinda Alhaji Sadi ya tsaya kulle Mota shima ya Biyo bayansa yana gyara Babban Rigar yadin Boyel Dake jikinsa,k**ar yau ne Daurin auran.Buga get din kawu Manu yayi yana kwada Sallama Megadi ya taso da gudu ya Bude karamar Kofar ya leko yana kallon su kawu Manu Cikin Alamun Rashin Sani.Ganin haka yasa kawu manu yace"Kai Megida nan yana nan..?Megadi yace"Eh yanzu ya shigo..!Kawu Manu yace"Alhamdulillah..Shiga ciki ka Sanar dashi magabata Ne masu Neman auran yarsa s**a zo..!Yafada Cikin Tabbatarwa Megadi bai yi gaddama ba ya Juya Zuwa Cikin Gidan Cikin Sauri k**ar zai kifa aransa kuma yana ayyana Daman Dalilin Dawowar Alhaji da wuri kenan..?Haba ko daga gani.!Yana wannan Zencen Zuccin ya Shiga Babban Falon gidan yana Rafka sallama Daidai Lokacin da Hajiya Mero ta Fito Daga Dakinta ta Chaba ado zata Haura sama wajen Alhaji.Sai ta Dakata jin sallaman megadi Har kasa ya Duka yana gaisheta ta amsa tana Fadin"buba ya akayi ne..?Kansa na kasa yace"Hajiya Alhaji ne yayi baki..Sunce ace mai masu neman auran yarsa ne..,!.Kuri Hajiya mero Tayi mai da ido kafin tace"Kenan daman da gaske zasu zo din..? Tafada cikin Bayyana mamakinta itafa ta Zata Kawai Fade sukeyi kuma data gayama Alhajin bai wani Damu ba ita azaton ta ya Shiryama hakan ne shiyasa bata Damu kanta ba.Megadi ne yaji Tana mgana yace"Na"am Hajiya me kikace..?.Kai ta girgiza kafin tace"Ka shigo Dasu Falon bakin Alhaji na waje..bari na Shiga na gayamai..!Da sauri ya mike k**ar ya Kifa yana amsawa da Toh ya Fice ta Bishi da kallon kafin ta kada kai ta Fara Haura Steps tsakani ga Allah Auran Safiya da yaron nan bai kwanta mata,Ya za"ayi ace Mutum ba"asan danginsa ba kuma abashi Aure aka sani ko wani mugu ne..?bari dai ta samu Alhajin Tagayamai taji me zai ce..?Ta isa Falon nashi Cikin wani yanayi ta iskeshi Yana karantar Jaridar Dailytrust,ta yau da bai samu karantawa ba Hajiya Mero ta Shigo ganinta da yanayinta yaasa ya gane ba lafiya ya ijiye Jaridan yana kallonta Lokaci Daya yana Fadin"Mero...Meron Alhassan Me ya faru ne naganki wani iri..?Gefensa ta Zauna Tana Fadin"Uhm.megadi ne ya shigo yace kana da baki..!Cikin Sauri yace"Wasu baki ne..? Allah yasa dai bakin da nake zaman Dakon jira ne...?Hajiya Mero tace"Wai Magabatan yaron nan mara asali ne wanda Safiye ke so Kamar ta mutu.Ni ban Dauka da gaske bane zasu zo..!Da sauri ya mike yana Gyara Hulan kansa yace"Daman su nake jira..Saboda su yasa na dawo da Wuri..!Galala ta kallesa kafin tace"Alhaji yanzu da gaske auran yarmu zaka bama wanda bamu san komai game dashi ba?Ko kallomta bai yi ba ya Nufi Hanyar Fita yana Fadin"Nidai ba wannan mganar ba..Ina Fatan kin saka an Shiga da baki na ciki dai ko..?Cikin Daure Fuska tace"Eh nace ya kaisu Dakin bakin ka na waje..!Kada kai yayi yana Fadin"Dakyau ina ita Safiyan.?Hajiya Mero tace"Tana cikin Dakinta mana..!Bai kara cewa komai ba ya sakai ya Fice ta Bisa da kallon mamaki tana Tunanin me ya sauya Ra"ayin Alhajin..? Wanda ta sani da kansa ya kori yusuf kuma yamai iyaka da gidan nan sai dai kuma Ta hasaso Faruwan wani bu..Da kalaman da Imran yazo yayi Tun Lokacin ne taga Alhaji ya Sauya Ra"ayi..? Me ke Faruwa ne wanda Ita bata sani ba kuma Alhaji baya sota tasani din.Cikin saurinsa da Sassafar ya Fito Megadi na gaisheshi Hannu kawai ya Dagamai ya Nufi Falon bakinsa na Haraban gidan Lokaci Daya da sallama Kawu manu da Alh.sadi dake zaune s**a mimmike tsaye da mamaki Alhaji Alhassan ya kariso yana kallon kawu Manu Domin yasansa,Farin sani Tunda Yawanci Gyaran Motarsa ko na yara garejinsa akeyimai kuma ya sanshi Dalilin yayan marigayi.Cikin mamaki ya mika musu Hannu s**ayi musabaha kafin su koma su Zauna s**a Fara gaisuwa Bayan sun gama gaisawa ne Alhaji Alhassan ya Fito da wayarsa Daga Cikin Aljihu ya kira Hajiya Mero tana Dagawa yace"Ki aiko da lemu da Ruwa na bakina..!Daga haka ya yanke kiran ya juya ga kawu Manu yana Fadin"Ikon Allah Mallam Manu..?kardai kace min kasan wannan yaron dake neman yata..?Kawu manu yayi Dariya Kafin yace"Eh to..Banace A"a ba..Sai dai kanin yaron mai neman auran ne abokin Dana Sagir dan wajem marigayi yayana Tasi"u da s**a Zauna nan kusa daku..!Alhaji Alhassan yace"ikon Allah..Ko da naji..Domin yaron da kansa ya gayamin basu da kowa kuma nima nasaka am bincikamin..!Kawu manu ya gyara Zama yana Fadin"Alhaji Aure ba mgNar wasa bane..Shiyasa zan gayamaka gaskiya..maganar gaskiya yaron nan bazamu ce basu da kowa ba sai dai muce haka muka gansu Rana tsaka abunda na Fahimta akwai wani Boyayyen al"amari a Rayuwar gidansu,Bazan ce ka bashi Auran yarka ba sai dai kada ka Duba wannan ka Duba Nagartan shi yaron in har kana ganin ba mtsala to ni kuma na yarda na Shige gaba kan al"amarin auran nan da yardan Allah..!Alhaji Alhassan yayi Shuru kafin yace"Wannan bai Dameni ba..Ita taji ta gani Saboda haka Tunda nace mata A"a kuma ta Dage sai shi Zan aura mata wanda take so Taje Tunda ita ta gani ta kuma Zabi a gidan da bai Dace da ita ba..!Kawu manu zai yi mgana ya Dagamai hannu yana Fadin"kunzo da Sadaki ne..?S**a kalli juna shi da Alh.sadi kafin Kawu manu yace"Kwarai..Harda kudin nagani ina so da Mintin da Dabinom mu na Ganin iri..!Alhaji Alhassan yace"Gud..Yanzu abunda za"ayi ku Dauko Dabinom da Sauran kayan..Kawo Sadakin ai bazaku koma ba sai da Amaryarku..!Cikin mamaki suke kallonsa Alhaji Sadi ne yayi karfin Halin cewa"Amarya kuma?Yace"Eh to me zan jira..? Tunda kunzo da komai naku..Kuma ai da Shirin Auran kuka zo Tunda kuka ci Manyan Riguna..!Mamaki bai barsu sun kara mgana ba ganin ya mike ya Fita ya yafito megadi yana zuwa ya Tasa sa s**a Dawo Cikin Falon mamaki bai barsu Kawu manu ba sai da s**a ga ya zauna ya kalli megadinsa Dake durkushe yace"Zauna Dakyau Buba..Shaida Zak**a Auran Safiya zan Daura yanzu..Ku miko sadakin kada ku damu ko nawa ne kuka zo dashi ku kawo..!Ba megadin ba hatta su kawu manu Sai da s**a Daskare Jiki ba Laka Alh.sadi da kudin ke hannunsa ya mik**a kawu Manu Shi kuma ya mik**a Alhaji Alhassan ya karba yana Fadin"Na wa ne anan..?Kawu manu yace"Dubu dari da Hamsin ne..Sadaki da kudin gaisuwa..!Alhaji Alhassan bai tsaya sauraransu ba ya kirga Dubu Dari ya Cire ya maida ma Kawu Manu Dubu Hamsin yana Fadin"Sadaki kadai nake Bukata..Don shima ya zama Dole ne..Ku matso mu Daura auran Ni zan yi ma yata Walicci Megadina zai zama Shaida Cikin ku wazai Wakilci Yusuf din..?Nan da Kawu manu yaji ya muzanta Domin bai ma san Cikakken sunan Yusuf din ba,Sai ya Nemi adagamai kafa ya koma Gefe ya kira Sagir sai da yayi mai kira uku ya Daga Cikin Sauri ya Tambayesa Cikakken sunan Yayan Imu Batare da wani Tunani ba Sagir ya Fadamai Yusuf Abubakar Malami shi a Tunaninsa zasu tafi Neman auran ne..Abun mamaki baya karewa Cikin Abunda bai fi Minti goma ba aka Tabbatar da Auran Safiyya Alhassan Buhari da angonta Yusuf Abubakar malami kan Sadaki mafi Daraja adaidai Lokacin ne yar aikin Hajiya Mero ta Shigo da Farantin Ruwa da Lemo ba wanda ma ya kalleshi Kowa yana ta mamakin wannan lamarin Alh.Sadi ne yaje waje Cikin Mota Megadi ya Taimaka s**a Dauko Kwalayen Minti da Dabino s**a Shigo Dasu.Alhaji Alhassan ya basu Hannu s**ayi musabaha kafin ya Umarci megadi Daya Dauka zuwa Falon Cikin gida ya Rufamai Baya,bayan ya cema su kawu Manu su jira Amarya ta Fito su tafi da ita..Kawu manu yaji kansa yayi Nauyi yace"Duk wannan gaggawar na menene Alhaji..?Mirmishi yayi yana ji k**ar an sauke mai wani kaya Yana matukar Tsoron Furucin Tsegerun Yaron nan Daya barsa ya Tona mai asiri gwara yayi ya Sallama musu Safiyan ita taji ta gani..Cikin Dariyan sa yace"To me zamu jira Tunda an Daura..? Kawai ku wuce da ita Daga baya zamu sauke hakkin mu na iyaye akanta zamu muyi mata kayan Daki Yanzu dai ta Farayin gaba Kafin komai ya Biyo Baya..!Daga haka ya Fice Daga Falon yana Rike da Sadakin a Hannunsa..Kawu manu ya Cire Hula yana Fifita Alh.sadi ya kallesa yana Fadin"Manu wannan wani irin Auran kaddara ne..?meke damun Alhaji Alhassan ne..,?Shidai kawu manu bai samu zarafin mgana ba Tunanin ya tafi kan yanzu ina zai kai yarinyar mutane..? Shidai baisan gidansu Imran ba koma ya sani baya je musu kai tsaye ba Dole dai ta Inda aka Hau ta nan za"a sauka..!

GIDANMU Part 15"Asalin sunanta *MARYAM MUSTAPHA HAMISU DUKKU*  ne Saboda taci sunan Mahaifiyar Babanta Daada yasa ake ki...
02/09/2025

GIDANMU Part 15

"Asalin sunanta *MARYAM MUSTAPHA HAMISU DUKKU* ne Saboda taci sunan Mahaifiyar Babanta Daada yasa ake kiranta da INTEESAR.Alhaji Mustpaha Hamisu Dukku Haifaffan garin Dukku ne na Jahar Gombe,ya kasance d'a na uku a jerin ya"yan Daada Maryam da Mahaifinsu Alkalin Kotun Musulunci Alhaji Hamisu Dukku.Hajiya Maryam(Daada) Haifaffiyar garin Dukku ce ta uwa Data Uba Bafullatanan Dukku Ta gaba da Baya,Auran Zumunci ne tsakaninta da Megidanta marigayi Alkali Hamisu Dukku,Domin alokacin Makoci Tamkar Dan"uwa yake wajen makocinsa iyayen Daada da iyayen Hamisu Dukku sun yi Zaman makota shekaru masu yawa wanda Sanadin haka yasa s**a Zama Tamkar yan"uwa wannan Dalilin ne yasa s**a Hada auran ya"yansu Wato Maryam(Daada) da Alkali Hamisu Dukku.Maryam(Daada) bata yi Zurfi a Karatun Boko ba iyakarta Sencondary Alokacin ma agidan Mijinta Alkali Hamisu Dukku Tayi Candy,Tayi aure da kananan Shekarunta,Saboda Tana da Shekara Goma sha Shida ne alokacin.Alkali Hamisu Dukku,yayi karatun Zamani Dana Boko ya tafi Jami"ar Abu dake Zaria inda ya karanci Shari"a Low,Bayanan yayi Degree dinsa na Farko sai ya Dora bayan haka ya Hallaci Courses masu yawa akan Abunda ya Shafi karatunsa agidansu Shi kadai ne yayi karatun Boko mai Zurfi Duk da basu da yawa shi ne kuma Babba.Yayi aiki a mtsayinsa na Cikakken Lauya ya taka mataki mataki na Rayuwa sun Fara zama da Daada a garin Dukku agidan iyayensa inda ya gada Tunda Lokacin Allah yayi ma Mahafinssa Rasuwa kafin ya samu aiki a babbar katun Jahar Gombe ya mallaki gida da Motar Hawa ya Dauki matarsa s**a koma Chan da Zama..Sun koma ba Dadewa Daada ta samu Ciki,kuma yana bata Wahala sosai Dalilin dayasa Alkali yasa aka nema mata yar aiki kenan Allah ya Hadasu zama da Baba Asabe Tun tana da Danyen Shekarunta Ita take Taimakon Maryam(Daada)da abubuwan Cikin gida,Alkali Hamisu Dukku da Matarsa Maryam(Daada) s**a Rike Asabe Tamkar wata jininsu ko nace Yar"uwansu.zuwa Lokacin duka sun rasa iyayensu saidai yan"uwa da abokan arzuka.Kabir shine Babban Dansu sai Abubakar,sai Mustpaha sai Fatima (Bintalo) sai auta Maimunatu,azuwa Lokacin da daya Tara ya"yansa Biyar ya samu Dukkan Cigaban Rayuwa,Asalin Komawarsu Dukku samun Alkalin alkalai na Babban Kotun musulunci Dake Dukku ne yasa yayi Ginin Zamani ya Tattaro Duka iyalansa s**a Dawo nan da Zama Dindin Daman shi Alkali Hamisu yana da Kishim kansa yafi Sha"awar Zama a Kauyensu Fiye da Ko"ina To itama Maryam(Daada) domin duk inda zasu je basu da k**ar Dukku.Alkali Hamisu Dukku bai bar Gidan Duniya ba sai da ya kwafa ya"yansa s**a samu Wadattacen ilimin Zamani Dana Boko,Kabir Shine ya gado sa shi ya karanci Harkan Shariya,Abubakar kuma ya kasance Malamin makaranta ne kowa yasan Burinsa Tun yana karami Shiyasa Alkali Hamisu yake mai Lakabi da MALAMI..!Bai kuma bar gidan Duniya ba sai da ya aurar da duka ya"yansa Daga matan har mazanBintalo Tana aure anan cikin garin Gombe,Tana auran wani ma"ikacin Fire service na Jahar Gombe kuma agidansa tacigaba da karatunta ayanzu haka Lacture ce itama anan Jami"ar Gombe Yayanta Uku Dayake bata cika yawan Haihuwa ba saboda Karatunta,Siyama da Hamida sai Hauwa"u Duka matane kuma Suna Gijajen mazajensu sunyi aure suma sun Haiyayyafa.Sai Maimunatu Tana chan Garin Bauchin yakubu Tana auran wani Soja ne,Ita tana da ya"ya sun kai bakwai,Manyan ya"yanta itama mata ne sai Mazan Sa"id da sadam.Sai kabir wanda ke Zaune a chan Birnin Tarayyah Abuja Yana mtsayin Cikakkem Lauyan gwannati ne,yana da mata Daya Asma"u wacce ta kasance Diyar Masu kudi ce Diya ce ga Alkalin akalai na kasa gabadaya,Sun hadu ne a wani Course Dayaje karanta a Washington,Itama taje Dukkansu Lauyoyi ne s**a Fara Soyayah har takai su ga aure duk da Mtsayinta da Nasabarta Barrister Asma"u taga Barrister Kabir Hamisu Dukku kuma tayi na'am Dashi Mahaifinta bai hanata abunda take so ba Tunda su yan Boko ne abunda duk kake so Shi zakayi.Dagashi har matarsa Lauyoyi ne masu Zaman kansa,Tsarin Gidansu tsarin Gidan yan Boko ne gaba da Baya Gabadaya Haka s**a Tsara Rayuwarsu Shiyasa ko a tsarin Haihuwa ya"yansu Uku ne Biyu mata daya Namiji Babba ne Namiji mai suna Hamisu wanda yaci sunan Marigayi Alkali Hamisu Dukku suna Kiransa Khamis,Yana Chan Anambra inda yake aiki a mtsayin Sojan Ruwa Navy.Sai kannensa Guda Biyu Sajida da Umaima wadanda Tazara ne mai Nisa a tsakaninsu dashi..Hak**a Tsakanin Sajida da Umaima akwai Tazaran shekaru k**ar Hudu haka.Sai Abubakar wanda Shima yayi aure kuma shima yana da ya"ya,Sai Lokaci Daya aka Nemehi aka Rasa Shi da iyalansa Wadanda suke a Rayuwa a lagos,Tunda Shi Abubakar din Malamin Philosopy ne a University of Lagos achan baya kafin wata kaddara ta Gitta musu wacce Tayi Sanadiyar Faruwar duk abunda ya Faru.sai Mustapah wanda ya kasance Dan kasuwa ne,kasuwanci ya karanta Domin Shine Burinsa,yana kasuwancin sai da kayan Mota,sai kuma yana Kiwo Harda gidan gona gareshi achan kaduna matarsa Salaha itama yar kaduna ce a Badarawa,Ita yar Talakawa ne ba masu Hali ba Inno da Mallam Babba,wanda yake sana"ar sai da Hatsi,su Biyar ne agidansu Yaya bala ne Babba,sai Yaya Salisu,sai yaya Amina sai Salaha(Umma)kenan sai karamin kaninsu Mudanssir.Auran Soyayya s**ayi Tsakanin Shi da Salaha Allah ya Hada auransu yana Zaune anan garin kaduna anguwan Sarki inda ya Gina katon gida,Allah ya sak**a Kasuwancinsa albarka Shima din za"a sakasa Cikin Jerin masu Dashi.Ya"yansa Biyu ne rak aduniya Basheer shine Babba wanda Bayan Haihuwarsa har sun Fidda rai da Haihuwa bayan Shekara Goma kana s**a samu Haihuwan Inteesar wacce taci sunan Daada Maryam.Atsarin Rayuwarsu Suna da Hadin kai da Zumunci a tsakaninsu kuma suna Girmama junansu Bayan Rasuwar Alkali Hamisu dukku wanda Ciwon Hakoribyayi sanadin Mutuwarsa Daga Dare zuwa safe,Su s**a Cigaba da kula da Daada da kuma Baba Asabe da s**a Taso s**a ganta agidansu,Kabir yaso ya Dauke Daada Daga Dukku ta koma Wajensa a Abuja ammh Taki yarda tace Yarda Alkali ya Mutu acikin gidanan itama nan Zata mutu Domin ya rasu bazata Ki Burinsa na son Ta Rayuwa ita da ya"yansu a garin na Dukku ba sai dai bata da yarda Zatayi ne Tunda aiki ya Raba kowannesu Inda yake ammh Ita kam ba inda Zataje Tana Tare da Baba Asabe a garin na Dukku agidan marigayi Alkali Muddum rai.Dole ya kyaleta Tunda ta kafe sai da yasa aka gyara gidan aka Maidashi na Zamani kowani Lokaci suna zuwa ganinta in s**a samu dama.Kayan alatun More Rayuwa kuwa da jin Dadi Daada sai dai ta bama wasu Komai na Rayuwa ya"yanta sun Dauke mata shi Taje ta Sauke Farali bata san iyaka ba bayan wanda marigayi Alkali ya kaita kuma s**a je Tare,Hatta Baba Asabe taje ta sauke Farali Sau Biyu Adalilin Daada da YayantaDaada Tayi kokarin Hada kan ya"yanta da Jikokinta waje Daya suna zuwa mata Hutun karshen Shekara Duka matan da Mazan Domin kara Shakuwa tsakanin iyayen da kuma yaran sun san junansu da yan"uwansu gabadaya,ammh abun ya ki faskara sai da ya"yan nata su zo,ammh Ya"yansu basa zuwa sai Dai dai,in tayi mgana sai su kawo uzurin makaranta da aiki da sauransu.Barrister Asma"u matar Kabir itace bata Shiga Mutane,Tana da Dagawa da Tak**a sai dai Tana da Fara"a in ta saba da Mutum,Taso tazo Daya da Umma Salaha,Suna dasawa sosai Ko Saboda yadda wata kakkarfan Shakuwa ke tsakanin mazajen nasu ne ohoCikin ya"yanta Sajida ce kadai ta gado Duka Hallayarta Har ma ta fita sosai.Sajida akwai Dagawa ga Tak**a ga Raini,Tana ganin tafi kowa Domin iyayenta sun tsaya mata sun kuma taka wani abu a Rayuwa,Yar gatace ta gaba da baya,agidansu basu san suyi aiki ba komai yan aiki keyi musu hatta da Girki kuwa,Inda Asma"u tayi kuskure kenan ko ita batace ta iya wani Girki ba Tun farkom auransu ta sakarma yan aiki Duka Ragamar Gidanta Har yau har gobe Abincin yan aiki yake ci kuma bai Taba Korafi ba saboda sun Tsara hakan Daman tun Kafin suyi auranKhamis ne ya Debo kaf Hallayan Babansa,kuma ya Debo Hallayan Marigayi Alkali wanda yaci sunansa yaro ne matashi mai Hankali da natsuwa yana Bala"in son Tsohuwa Daada,Musamman Daga Anambara yake zuwa ganinta in ya samu Lokaci Waya kuwa Lokaci bayan Lokaci Tana jinsa kudi kuwa makudai haka yake Turomata,Duk Shekara sai ya Sauya mata Furniture din gidanta Shiyasa itama take matukar ji Dashi,Sai dai duk yadda take ji Dashi ba kai Soyayyar Datake ma kwara Daya Cikin Jikokinta ba Dukda ya kasance mai Budadden Hali da kowa baya jin Dadin mu"amala Dashi ita ahakan take matukar sonsa,sai dai Bata nunawa ba..Tunda bai Cika yawan Tako kafarsa Dukku ba sai da wani Babban Dalili Shima din sai Mahaifinsa ya Mtsamasa ne ya Tarosa s**a Taho Tare,bawai bai Damu da kowa bane a"a yana Damu da Ahalinsa sai dai shiyanayin Rayuwarsa marasa son Doguwar mu"amala ce mara son Hayaniya da Zama Cikin Mutane, yana da Bambacin Ra"ayi da Mutame Koda kuwa yan"uwansa ne Shiyasa bai Cika Shiga Cikin yan"uwa ba,adangi ba wanda zai ce ya taba Doguwar mu'amala Dashi,ko da yan"uwansa da s**a Fito Ciki Daya suna kuka da Hallayarsa masu Tsauri da Wuyar Fahimta.Wannan kaunar ta samo asali ne da kaunar Datake yi ma Mahaifinsa ne saboda ya kasance mai sanyi Rai ladabi Biyayyah ko baya son Abu indai Daaada ta Ce abu kaza ne sai yayi shi Biyayyarsa da wannan Sanyin nasa yasa Daada ke matukar sonsa uwa uba kuma ta wanke Diyar kanwaarta Data Zama k**ar itace komai nata ta Riketa ta bashi kuma ya karbs ya aura ya Zauna da ita Har Mai Rabawa ta Rabawa Duk da Ya kawo mata wacce yake so.Shiyasa har Yau har gobe Daada bata daina kukan Rashinsa baTa kamu da Ciwom Hawan jini Saboda Damuwa ya"yanta suke Wahala kan lafiyarta Musamman Kabir ya Daukan mata Likita wacce take zuwa har Gida Tana kula da ita Dr.Zubaida Cikakkiyar Likita a babban asibiti dake garin na Dukku.Koda Daada ta tsufa Girma ya zo mata bata da Lalaci,kowa ya sani mace ce mai tsayawa akan kafarta Shiyasa bata Shiri da Sanganta da kiyuwa Sajida na yawan zuwa Hutu gidan Daada sai dai Rabuwa sukeyi ba Dadi Tun Kafin ma Hutun Sajidan ya kare.Umaima kanwarta ta fita sanin ya k**ata gata bata kiyiwa in tazo Shara gyaran Daki har girki Take Taya Baba Asabe,gidan ta koyi wasu girken girken Data koma Abuja ta gwada Ranar Diyar Lauyoyi Taga Fada k**ar su Daketa suna Fadin kada ta kara Wannan kwarambanin Hannunta bai yi kwarin da Zata yi Girki ba kada ta koneItakuma Sajida Fadi take Tana Diyar Lauyoyin gwannati Jikar Alkalin akalai na kasa Duk da yayi Ritere,Kudi da jin Dadi sun gama Dabaibaye Rayuwa komai take kudi zasu yi mata Allah ya Tsareta da aganta tana aiki indai akwai yan aiki da kudi zasu yi mata komai Shiyasa basa Shiri da Yayanta Khamis Shima a tsaye yake a kullum yana tsawatar mata Da cewa ita macece Watarana Zatayi aure ammh Sai mahaifiyarsu da suke kira Mami ta Shiga mganar tana Fadin ya Daina Takura ma yarta yadda ta Samu jin Dadi agidan Mijinta itama Zata samu,Shidai kawai Shiru yake domin yasan Watan Watarana Zasu yi Nadaman wannan Rayuwar Bokom da Sakewan da s**a Daukan ma kansu Shi Allah ya Taimakeshi Gombe yayi karatun Secondary Dinsa Bording in ya sami Hutu bai cika zuwa Abuja ba yana gaban Daada Shiyasa ya zama DabamYar tsamar Dake tsakanin Inteesar da Daada kuwa bawata maiyawa bane..Duk da tafi kowa Murna da Akayi mata takwara sai dai basa Shiri saboda irin gatan da Alhaji Mustpaha yayi ma Inteesar saboda Samunta Lokacin da s**a Fidda rai.Inteesar ta shaku da Mahaifinta Fiye da kowa aduniya ko Mahaifiyarta bata Shaku da ita ba irinsa ba,Dalilin haka yasa bata da Sakin jiki da Mutane bata san kowa ba sai Daddynta sai Ummanta da yayanta Basheer sai kuwa Gidan kakaninta ta Bangaran Uwa gidan su Inno,Su da suke Biyema Sangartanta.Inteesar bata san kowa a Dangi ba Domin bata zuwa ko"ina gwara Dukku ma in Alhaji Mustapha zai je takan Biyosa suzo Tare,Bata yarda ta kwana Kafarsa kafarta Duk kuwa da Mitan da Daada ke yi na bata son Shiga Cikin yan"uwanta.ita kuwa bata son Rabuwa da Babanta ne kuma tafi sabawa dashi Fiye da kowa.Rabon Inteesar da Zuwa Dukku har ta manta saboda Korafin Daada akanta,Tayi ta cewa ta Cika Sangarta tayi ta ma Daddynta Fada kan ya Sangartata ita kuma abun Haushi yake bata yasa Daga Baya ta Daina Biyosa sai ta Fake saboda makaranta.Ko Duka gidan Za"aje sai dai taje gidan Inno ko gidan Kawu Salisu Saboda yarsa Nasara sa"ar Intee ce kuma tasu tazoDayaShiyasa bata san kowa ba adangi su Inna Bintalo da Inna Maimuna sun gaji da mita sun Hakura Inteesar bata taba zuwa Gidan Daya Daga Cikinsu ba ko Za"aje bata zuwa bata son Abun mgana.Tuni ta Dauke kafa Daga Dukku Tun Tana karamarta har saida taGirma Lokacin Data gama Candy Tana jiran Sak**ako Daada ta matsa Umma ta Ce sai taje tayi Kwana Biyu achan,Daddy shi ya Lallasheta yakai ta da kansa Aranar Dataje Washegari Sajida ta iso Daga Abuja.Inteesar bata ji Dadin Zaman Gidan Daada ba,Shiyasa Dukkun ta fita kanta Zaman da s**ayi da Sajida Zama ne na kowa na Har kan gabansa Sajida girman kai da Dagawa..da nuna isa ita kuma Inteesar rashin Tsoro,itama tana ji Da gata sosai Shiyasa basu ga maciji,Daada ta Dinga Fada ita Sajida Kiyuwa da son jiki ita kuma Inteesar Da an fara mgana sai kuka Daada Tayi musu Fatata ta kira iyayansu s**a zo s**a Tarkasu,kowacce ta koma Gidansu da jin Haushin yar"uwanta,Sajida tana ganin k**ar ita yar gata gaba da baya Diyar lauyoyi,yayanta Soja jikar Alkalin alkalai har wata adangi Zata Rainata Ina batazata yarda da wannan ba ita kuma Inteesar tana ganin ai Sajida bata fita gata ba bata isa ta taka ta ba.Haka kowacce ta koma Gida da Korafin yar"uwanta Umma dai ta tsawata ma Inteesar din Ta nuna mata yar"uwanta ce ayayinda Mami bata tsawatarma Sajida ba sai ma Nuna ma Datake tafi Inteesar din gata nesa ba kusa ba Duk kuwa da suna Dasawa da Umma sai dai ita akwai son kanta Tana so a ko"ina akomai Ita da ya"yanta su fi kowa a Dangi Ba kuma iya Zuru"ar Hamisu Dukku ba Harta Daga Bangaranta Tana da wannan Dagawan.Daga Lokacin kowacce ta ijiye yar"uwan nata awani muhalli na ban san kina Rayuwa ba,Basheer ne dan Dangi kowa ya sanshi kuma ba inda Kafarsa bai taka ba Tun yana Saurayinsa ma kafin yayi aure Dayake Jami"ar Bauchi yayi ya Zauna gidan Inna Maimuna Sosai yake da mu"amala mai kyau da kowa..Inteesar kuwa bata taka kafarta Ko"ina ko Abuja gidansu Sajida Sau Daya taje Lokacin Tana karama da Tabi Daddy,daga wannan zuwan kuwa bata kara marmari ba,Lagos kuwa bata taba Zuwa ba tasan dai Tana da wani Uban achan lagos din inda yake Zaune shi da iyalansa ba kuma Tataba ganinsa ba sai Sau Daya sanda s**aje Dukku ita da Daddy Shima yazo shi da dansa bata dai san ko waye ba,Ta gansa alokacin ammh Tana karama bazata iya Shaidasa ba yanzu.Lokacin kuma da akayi Rasuwa anan Dukku aka Dawo aka karbi gaisuwa Lokacin Basu da Hutun makaranta Gidan Kawu Salisu tatafi abunta tayi Zamanta Saboda Nasara Domin aduniya Inteesar Bata da wata wacce ta Shaku da ita Kamar na Nasara kuma tasu tazo Daya daga ita sai Inno da Malam Babba Saboda yadda suke ji da ita sai kawunta Muda,shima akwai Biye ma Shiriritanta...Sajida Ta fara karatun Jami"a a Base University Abuja a wannan Shekara yar Jarida take son Zama,Journalist itama Inteesar Tana so ta karanci Fanni Tsumi da Tanadi Wato Economics,Ta lula kano Inda Zata Fara Sabuwar Rayuwa.

02/09/2025

D Jay Braheemy

31/08/2025

Abdul Director

Gareka saurayi ga irin tambayar da ya k**a ka rika yiwa budurwar ka:-Ina son ki kasance Mai fadamin gaskiya Koda zata ba...
30/08/2025

Gareka saurayi ga irin tambayar da ya k**a ka rika yiwa budurwar ka:-
Ina son ki kasance Mai fadamin gaskiya Koda zata batamin rai! (Domin tabbatar da gaskiya da dogaro)

Want to learn how to create mobile apps using only your phone?No laptop, no coding experience – just your mobile phone πŸ“±...
30/08/2025

Want to learn how to create mobile apps using only your phone?
No laptop, no coding experience – just your mobile phone πŸ“±.

πŸ”₯ Join my Online App Development Class and discover step-by-step how to:
βœ… Design beautiful apps
βœ… Add real features
βœ… Launch your own projects
βœ… Build apps without stress

✨ Why Join?

Learn anytime, anywhere (just your phone)

Easy-to-follow lessons

Practical, hands-on training

πŸŽ‚ Because it’s my birthday month, I’m giving you an exclusive 60% discount 🎁.
πŸ‘‰ Limited spots available – don’t miss this chance!

πŸ“© Register now and start building your own mobile apps today!

Click the link below to join our WhatsApp group πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/BCVKBTjTi4yICgOzV1Mr9X?mode=ems_copy_t

Shawara game da Soyayya
29/08/2025

Shawara game da Soyayya

29/08/2025
29/08/2025

GIDANMU Part 14

Bude Idanuwanta Tayi Cike da Barci Ta saukesu kan Umma Data Dauro alwala ga Ruwa nan na Diga,kan Fuskarta Hararanta Umma Tayi Tana Fadin"Kinga irin Halin naki ko..? Sai ki tashi kiyi Sallah..!Tafada lokaci Daya Tana kokarin Sanya Hijabi ta tada Salla kan Darduman da Mama ta Shinfida mata.Dakyar Inteesar ta iya mike Jikinta duk ya Mutu ga kasalan Data k**ata ta Shiga Tiolet tayo alwala Tazo gefen Umma Ta Tada Sallah bayan ta Bude karamar akwatinta Data Jera Sabbin Hijabanta da mayafanta ta Dauki Daya cikin wanda Anty Hauwa ta bata ta saka ta tada Sallah.Nan itama Mama ta Shigo Tayi alwalan Tayi sallah Bayan ta idaar ne ta juya tana kallon Inteesar tace"Maryam bazaki ci abincin bane..?Inteesar taji abun wani bambarakwai Domin bamai kiranta da asalin sunanta sai Inteesar,Kai ta gyada kafin tace"Kila sai anjuma Inna Cikina ya cika..!Umma ta karbe da Fadin"gatanan sai kin mata da gaske..Bata son Cin Abinci shiyasa kullum Zaki ganta jiya iyau Sillen kara k**ar a Hureta ta Fadi..!Umma ta karishe Fade Tana yar Dariya ganin yadda Inteesar din Ta Zumbura baki tana Dakuna Fuska ganin haka yasa Mama Jawota Jikinta ta Rumgume Tana Fadin"Kyale Sahala..In kika Tashi Zuwa Hutu na Tabbata bazasu ganeki ba..In ita bata son yar Dake ni ina so..Daman Daga Sagir sai ni agidanan naji matukar Dadin zuwan yata..!Tafada Cikin nuna Murnanta Sai Ta bama Inteesar Tsausayi Sai ta kara Lafewa ajikinta Tana Fadin"Yauwa Mamata..Daman Umma bata sona..Nima na samu Mamata yanzu..!Umma ta kyabe baki Tana Fadin"Kuje kuyi ta kaya..Indai wannan ne zaki dawo min ne..!Mama tace"Insha Allahu bazamu Taba Dawowa ba sai adawowar alkhairi..!Inteesar sai Mirmishi take Na jin Dadi Bazatace batasan Inna Amina ba,sai bata taba Zama da ita sosai haka ba wani lokacin in tazo tana makaranta sanda zata Dawo kuma Sai tatafi Gidan Inno ranar data kwana gidansu kuma Tana Dakin Umma ba wani Shakuwa Tsakaninsu sosai...Hira s**a Cigaba da yi sama Sama Inteesar an samu Abunda ake so sai ta kara lafewa Jikin Mama Kamar wata mage har tana lumshe ido,Abunda bata samu wajen Umma ita bata yarda da wannan Sakarcin ba.Suna cikin Hiran ne sai ga Sagir ya Shigo bayan yayi sallama S**a amsa mai ya Shigo Ciki ya Duka yana gaishesu da yammah s**a amsa mai sai yake fadamusu Daddy ne zai wuce masauki sai Gobe zai Dawo.Mama ta Mike Ita da Inteeaar Dataji Zencen Tafiyan Daddy.Umma ma ta mike,Mama ce tace"Bazai kwana anan ba Salaha..? Tunda ga Dakin Sagir zai Ishesu sai shi ya barmai katifar Shi kuma sai ya kwanta kasa..!Umma tace"Haka kawai Yaya Amina shi da Dakinsa yayi kwanan kasa..? Barshi yaje masauki Koma kinyi mgana bazai Zauna ba..!Mama bataji dadi ba tace Shikenan Dukkansu s**a Fita Tsakar Gida Inda Daddy ke Tsaye da Gudu Inteesar ta isa gareshi ta Rungume Tana Fadin"Daddy na..!Shima riketa yayi yana Fadin"Intee ta..Uwata ta kaina..!Yafada Lokaci Daya yana Shafa kanta,Kara lafewa tayi ajikinsa k**ar wata mage Sagir Dake gefe aransa yace"Yarinyar nan akwai Shagwaba..!Mama ce tace"Alhaji bazaka kwana anan ba..? Naga ai duk gida ne..?Daddy yace"A"a Yaya Amina bari naje masauku da safe zan dawo mu wuce in Allah ya yarda..!Bata da tacewa illah ta Bishi da Allah ya kiyayewa ya Fice Yana Rike da Inteesar Umma da Sagir s**a Bi bayansu Har zaure Inteesar ta Raka Daddy tana ta mai Shagwaban gobe bazata iya Shiga makaranta ita kadai ba WahalaUmma tayi karamin Tsaki Tana Fadin"Kada Allah yasa Ki iya..gobe da wuri Insha Allahu muna kaduna in zaki warware wannan Son Jikin naki da Rangwantanki kiyi karatu..Daman Daada ta kira waya tace abaki kina bacci tace na Fadamiki ki Dage da karatu banda Sangarta da Sakarci..!Kafin Umma ta gama mgana Inteesar ta kusa saka kuka Ta kalli Daddy tana Fadin"Daddy kaji Umma ko..? Daman Daada nan itama bata sona.Koda yaushe tayi ta min Fada..Taci ka Fadan Tsiya..!Umma tayi mata Dakuwa Tana Fadin"Kinga naki nan..? Wato Tacika Fada ko..? Ai Mai Biye mikin ma ta isa dashi kuma Fada take yi mai a zauna Lafiya ballatana ke..!Ai sai Inteesar tayi kokarin saka kuka Tana Dira Kafa Daddy ya Dafa kanta yana Fadin"Kada ki bata Hawayenki Inteen Daddy..Gobe da safe ki Shirya da Wuri in xamu Wuce sai mu Biya ta makaranta inkingama Komai kin Fara Shiga lacture sai mu wuce..Ga Dan"uwaki nan sai muje Dashi sai ki samo abokin Dawowa Tare..!Sai alokacin Ta saki Ranta Daddy ya kalli Umma yana Fadin"Sahala bana jin Dadin yadda k**e Hantaran yarinyar nan fa..? Duka nawa Intee take da zaki bi ki Rika mata Fada k**ar wata Babba..?Ba Umma bace take mamaki ba Domin ita saba gani Sagir ne yake kallon Inteesar yana auna mganar Daddy wai duka Duka nawa take..? Wannan gansamemiyar Budurwance yarinya..?lalle yau yana ganin Abu xai so Imran yana wajen nan ya Tabbata da ya kusa Mutuwa saboda Takaichi.Umma bata tsaya bata bakinta ba ta Juya tana Fadin sai Allah ya kaimu ta shige Cikin gidan Ta bar Daddy na Fadama Sagir gobe tare zasu shiga makaranta Dashi Sagir yace ba mtsala Dayake Shima yana da Lacran safe.Shidai yana gefe yana kallon Sangarta irin ta Inteesar Dakyar ta Saki Daddy ya Fita Sagir ya Rakashi Wajen Mota s**ayi ssllama kana ya wuce Shagonsa yana kara mamakin Inteesar afili ya Furta.."Mama zata sha Fama..!Inteesar da Wuri Tayi barcin Tana idar da Sallar Isha"i Ta ci Danbun namanta da Umma Tayi mata,Ta hada da Lemo har mamana mganar bazai taso mata da Daddare ba..?Umma tace"Wannan ki kyaleta inda kika barta Shan zaki da kayan Kwadayi nan tafi auki babu abunda yake mata..!Mama tana Dariya tace muna da lafiya ne,Inta dai Intee Kayan Barcinta ta saka ta Bi Lafiyan gado sai barci,ta bar Umma da Inna Amina suna ta Hira Sama sama take jin suna waya da Inni da Mallam Babba,Sai kuma taji Ya Bashir ya kira ta wayarta Data Manta da ita saboda gajiya Umma ta Dauka s**ayi mgana har tabama Inna Amina s**a gaisa.Kusan Raba Dare s**ayi suna Hira kafin su kwanta Umma kusa da Inteesar ta kwanta,Ita kuma Mama ta yada katifa ta kwanta.Da asuban Fari s**a tashi..Mama ta Fita waje ta saka musu Ruwan wanka kana tazo tayi sallah Bayan ta idar s**a gaiggaisa ta kara Fita Bayan Fitantane,Umma ta karayima Inteesar fada tana Nuna mata ta Rika Taimakon Mama da wasu ayyukan Inteesar tace Insha Allahu.Mama tayi musu abun karyawa bayan ta juyo musu Ruwan wanka Umma ta Farayi kana Inteesar,suna gama Shirya s**a iske kayan Karyawansu tea da Buredi da Soyayyah kwai sai Umma datace Kosai take so da koko s**a zauna s**a karya atare,Suna Hira cikin Sha'awa Inteesar bata wani ci Abun kirki ba Bata iya cika Cikinta in Zata Fita wani waje ta Dade,Umma ta matsa mata sai da ta saka wata Sabuwar amtafa da Ummanta Ta Dink**ata Doguwar riga Chiganvi mai kalan green ssi tayi amfani da green din mayafi da Takalmi da Jaka.Sagir ma yayi wanka yana Dakinsa yana karyawa sanda Daddy ya karisowa shi ya Fita yayi mai Jagora zuwa Cikin gidan s**a gaisa da Mama Da Umma lokacin sun gama s**a Tashi s**a Fara Shirin Tafiya.Daddy ya duka har kasa yana Damka Amanar Inteesar wajen Mama tace ta karba Tayi alkawarin Zata kula da ita k**ar yadda Zata kula da Sagir.Yaji Dadin haka ya Dire mata kudi 30k tace bazata karba ba ya Fice bai Dauka ba.Umma ta Dauka ta bata bayan ta Hada mata da 10k tace ta Rike ahannunta Mama nata Godiya Inteesar kuma sai Hawaye k**ar sallaman kenan bata Dauka haka abun yake ba da bata Zabi Karatu a Kano ba.Har waje Mama ta rakasu tana Godiya Tana Daga musu Hannu.Umma ta shiga Gaba Inteesar da Sagir abaya wacce ke ta Sharan kwallah Daddy na gaba yana Tuki hankalinsa na kanta k**ar shima ya saki kukan.Daganan basu Dire ko"ina ba sai Cikin Jami"ar Bayero,Sagir bai Rabu dasu ba sai da komai na Inteesar ya k**allah Zata Fara Daukan karatu Daddy har bakin Hall din inda yan Department din su ke karatu s**a Rakota Wato Itama Zata karanta Fanni Tsumi da Tanadi wato Economics.Inteesar Tayi kuka k**ar Ranta zai Fita ta makalkale Daddy taki sakinsa Harta Umma sai da ta sakata kwallah,dalibai suna ta wucewa suna ganin abun mamaki kuka a jami"a..? Kamar wata yar sakandiri.Dakyar ta saki Daddy,bayan ya Share mata Hawaye,Ya lallasheta kana ta juya ta shiga Hall din Tana Daga musu hannu.Bayan ta Shige ne Sagir s**ayi sallama yace shima zai Shiga karatu ne,Daddy ya kara Damka Amanar inteesar a hannunsa yace bakomai yanzu hak**a Umma ta bashi Lambarta zai jirata su gama karatu su koma Gida Tare kafin ta saba Daddy yaji Dadin haka 10k ya bama Sagir ya karba yana ta Godiya Daganan s**ayi sallama s**a Shiga Mota s**a k**a Hanyar kaduna shi kuma ya wuce Department dinsu yana ta Sauri Tunda yasan an Shiga Tun Dazu!Wayarsa ya Fito da ita yana Dubawa yana tafiya,karamin tsaki yaja ganin har yanzu bai ga kiran Imran ba alhalin tun safe yake kiransa bai Daga wayarsa ba Jiya kwata kwata basu hadu ba yadai kirasa yace ya Turamai lambar Baba Manu ya tabbata ya kai mai kudin Da s**ayi mgana ne,Yasan waye Imran in yace zai yi abu baya saba alkawari zai yi din ne yana so yaji yau su Baba Manun zasu je neman auran..? Ammh bai Daga kiransa ba Shiyasa har ya karisa cikin ajin yana ta sskin tsaki.!Abunda Sagir bai sani ba jiyan Banki Imran yaje ya Ciro kudi a Bankinsa wanda baya amfani DashivSai Lokaci bayan Lokaci,Sai kuma yaje Banki ya Cike Form yake iya Fidda kudi Gabadaya kudin bankin nashi Dubu Dari uki s**a Rage bai yi mamaki ba yau da gobe bai bar komai ba yana Cire kudi Lokaci Bayan Lokaci yayi Hidimansa kanar siyan takalma,Kaya da Sauran abubuwan da baza"a rasa ba!Sauran dawaniyar Yusuf ke gudanarsu da albashinsa in ya gagara sai ya taba kudin Dake Bankin Abba ko na Marigayi Yayansu Nura saboda Dawaniyar Abba da Likitan Dake zuwa Gida Dubashi da kuma Dawaniyar mganguna,Ammh shi baya karba ko Naira Biyar wajen Yusuf da kudinsa Daya tara lokacin Daya fara aiki a inda s**a zauna yake amfani.Bashi da Zabi Dubu dari Biyu 200k,ya ciro ya Dawo Gida a kuma Lokacin ya kira wayar Yusuf yace ya sanar ma Safiya ta Fadama Babanta mgabatansa suna tafe gobe,ya kashe nan take kuma ya kira Sagir yace ya bashi Lambar Baba Manu yana Turomai ya kirashi yafadamai sunansa yace ga kudin nan zai kawomai shi kuma yace ya bari zuwa anjuma yanzu yana gareji ne.Haka kuwa bayan Isha"i Imran yaje yakai ma Baba Manu kudin yau ko Rakiyar Sagir bai nema ba.Yusuf kuwa bai yi mamaki ba Sanin Halin kaninsa Duk Abunda yace zai aikata baya Runtsawa sai ya Tabbatar dashi..Safiya ya kira ya Fadamawa,Sai taji abun k**ar wasa Cikin Tsoro Ta sanar ma da Mahaifiyarsu Hajiya Mero ita kuma ta sanar ma da Alhaji Alhassan bayan ya Dawo ya Cije a lebe a Fili ya Furta."Allah ya kawo su lafiya..!Domin ya gama Shirya abunda zai yi goben da Zarar sun zo..Shi da kimarsa da mutumcinsa agari bazai bari saboda Dalilin Safiya wannan Shegen yaron Mara kunya ya Zubarmai da Daraja ba.!*Ba na fara saka Lokacin Posting bane k**ar yadda wasu ke Tunani ba,Ni bana Ware wasu ranakun Lokacin Posting,Ina yi duk rana alokacin da na samu dama da Lokaci sai dai in Rashin Lafiya ko ciwo ko wani Uzuri,Domin daman kana naka ne Allah yana nashi na Allah kuma shine Daidai Jiyan nan na wayi gari bani da Lafiya shiya kawo Tsaikun Rashin posting dina ajiyan..Ina ganin Comments dinku ina matukar godiya Yan Wattpaddian Voting dinku yayi kasa fa ya k**ata ku kara kaimu nayi muku alkawarin Bazan baku kunya ba Insha Allahu*

Address

Sokoto
Sokoto
840212

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lafazin so posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Lafazin so:

Share