AlameZone

AlameZone Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AlameZone, Digital creator, Amarawa Illela, Sokoto.

Akwai alamun ango ya manta bai yi brush 🪥 ba kafin yazo bikin nan🤔
26/04/2026

Akwai alamun ango ya manta bai yi brush 🪥 ba kafin yazo bikin nan🤔

26/04/2026

Ka dena ba wa kanka haƙuri. Daina faɗa wa mutane dalilin da ya sa ba ka fara ba. Tashi ka fara da abin da yake hannunka! Idan ba za ka iya gudu ba, yi tafiya. Idan ba za ka iya tafiya ba, rarrafa. Amma ko me za ka yi, kar ka bari shekara ta sake zagayowa ta tarar da kai a wurin da kake kana ba da uzurin da kowa ya riga ya sani.

26/04/2026

Duniya budurwar wawa🤔

25/04/2026

A matsayin ki na mace mai hankali, wajibi ne ki san ta inda mijin ki ke samo kudin da yake ci dake kada watarana kiyi nadamar aurensa.

Kada ki ce ke a kawo kawai ki rika tunani.

25/04/2026

Ka yi hankali da irin mutanen da kake kusa da su, domin su ne za su iya tasiri a rayuwarka ko dai su gina ka, ko su ja ka baya.

Allah sa mu dace.

25/04/2026

Imani a zuciya yake haka ne, a ku sani alamar sa a gaɓoɓi take.

25/04/2026

Allah sarki Rayuwar Mata 🥺

Zawarci abu ne marar daÉ—i dake illata rayuwar mata a wannan zamanin da muke ciki.

Dan Allah maza aji tsoron Allah, ku kuma Mata a rika kai zuciya nesa aure ibada ne ba gidan hutu ba.

25/04/2026

Ku kiyaye zama da mace uku.

1. Mace Mai yawan rantsuwa.
2. Mace Mai yawan hayaniya.
3. Mace Mai yawan gadara da buga kirji.

Turanci ba Ilimi bane🛞Babu yadda za a yi mu tashi muddin muna amfani da fika-fikan da ba namu ba.Iƙirarin kwarewa a hars...
24/04/2026

Turanci ba Ilimi bane🛞

Babu yadda za a yi mu tashi muddin muna amfani da fika-fikan da ba namu ba.

Iƙirarin kwarewa a harshen Turanci ya zama sarka dake daure mana tunani, alhali gaskiyar ita ce Turanci harshe ne kawai na sadarwa, ba ma'aunin INTELLIGENCE ba. Idan har kana tunanin cewa sai ka iya Turanci ne sannan kake da ilimi, to ka fada cikin babban tarkon da aka dana wa Afirka tun shekarar 1884 a taron da akayi a Berlin; tarkon da aka sanya don mutum ya raina asalinsa, ya watsar da harshen mahafiyarsa, sannan ya rungumi ilimin da yake koya masa yadda zai yi wa wasu aiki, maimakon yadda zai gina kansa.

Je ƙasar Denmark, za ka ga ana koyarwa da yaren Danish; je Norway, Norwaygian ake amfani da shi; haka Japan, je india, spain da China, kowannensu da harshensa yake kera fasaha da kimiyya. Amma mu a nan Afirka, musamman a Arewacin Najeriya, an koya mana cewa muddin baka iya Turanci ba, to baka da wayo, koda kuwa kana da basirar da zata iya sauya duniya. Wannan shi ne babban kuskuren da ya sanya muke da injiniyoyin da ba za su iya gina mana hanya ba, sai chinawa sun zo, muna da likitocin da idan s**a kamu da rashin lafiya sai dai a kaisu Dubai ko Jamus, domin ba su amince da tsarin da s**a karantu akai ba. Ilimin da aka bamu ba na kirkira ba ne; ilimi ne na samar da ma'aikata (Clerks) bayi wadanda za su rinka mara wa daular mulkin mallaka baya.

Babban abin mamakin ma shi ne yadda muke alfahari da digiri a fannin aikin gona, amma bamu iya banbance tsakanin akuya da tunkiya a aikace ba. Muna da furofesoshi a fannin likitanci, amma lokacin da annobar COVID ta zo, daukacin Afirka kuka muke yi muna roƙon Moderna dq Pfizer daga Amurka, ko Sputnik daga Rasha; wannan yana nuna cewa iliminmu ba shi da asali a cikin bukatar al'ummarmu. An dasa mana kiyayya da kanmu ta yadda idan yaro ya yi magana da Hausa ko wani harshe na asali a makaranta, sai a kira shi Vernacular a sanya masa tara, alhali a nan ne asalin tunaninsa da basirarsa suke. Mafi girman hankali shi ne Metacognition, ikon lura da yadda kake tunani; amma mu an mayar da mu Autopilot, muna maimaita abin da aka gaya mana ba tare da mun tantance amfaninsa ba.

Gaskiyar dake boye ita ce, matuƙar ɗan Afirka bai gane cewa wayewa ba ita ce sanya kwat da riga a cikin zafin da ya kai digiri 40 ba, to har yanzu yana cikin sarka. Ilimi na gaske shi ne wanda yake magance matsalolin al'ummarka ta hanyar amfani da abin dake ƙasa, ba wanda yake sanya ka zama mabaracin ra'ayin wasu ba. Lokacin da kuka ga mutum yana takama da Turanci yana raina harshensa, shi ba san cewa har yanzu yana cikin barcin da aka sa shi tun karni na 19 ba.

Lokaci ya yi da za mu farka, mu gane cewa babu yadda za a yi mu tashi muddin muna amfani da fika-fikan da ba namu ba.

Karshen Rashin Kunya da Rashin Tsoron Allah Mace Musulma ta Daga Pant a T**i da Sunan Siyasa.A wajen mata a Arewa, wanna...
24/04/2026

Karshen Rashin Kunya da Rashin Tsoron Allah Mace Musulma ta Daga Pant a T**i da Sunan Siyasa.

A wajen mata a Arewa, wannan lamari ana kallonsa a matsayin kololuwar rashin kunya da barin al’ada.

A shekarun baya ba masu nisa ba, duk wata mace a ƙasar Hausa tana yin iya ƙoƙarinta wajen ɓoye kamfai. Hatta wankinsa a sirri ake yi, haka nan wajen siyansa ma a ɓoye ake yi. Wannan ba don tsoro ba ne, sai don mutunci, kunya da tarbiyya da aka gada tun daga iyaye da kakanni.

Yau kuwa, abin ya sauya. Abin da a da ake ɓoyewa, yanzu wasu suna fito da shi a fili, har ma suna nunawa a matsayin wata alama ko saƙo. Wannan sauyi yana tayar da tambaya mai girma: shin ci gaba ne, ko kuwa kaucewa daga al’ada?

Tabbas wannan abu bakon lamari ne a al’ummar Hausa, kuma mutane da dama na kallonsa a matsayin rashin tarbiyya da karya dokokin al’ada. Wasu ma na ganin hakan na iya jefa mace cikin mummunan fahimta a idon jama’a.

Idan har siyasa ko wani yanayi ya kai ga haka, to akwai buƙatar a tsaya a yi tunani. Domin al’ada da mutunci su ne ginshiƙan al’umma. Idan aka fara wasa da su, sakamakon zai iya zama mai tsanani ga tarbiyyar gaba.

24/04/2026

Babban bankin Najeriya (CBN) ya ƙara kuɗin karbar katin ATM (debit/credit) da kaso 50%, daga ₦1,000 zuwa ₦1,500.

A cikin sabon daftarin ƙa’idojin cajin bankuna na shekarar 2026, CBN ya kuma soke cajin kula da katin naira na ₦50 duk wata. Sai dai masu amfani da katin kuɗin waje za su ci gaba da biyan kuɗin kulawa na dala $10 a shekara.

Haka kuma, CBN ya bayyana cewa kwastomomi ba za su ƙara biyan kuɗin amfani da na’urar PoS ba, domin duk cajin zai koma kan ‘yan kasuwa. An saita cajin Merchant Service Charge (MSC) a kashi 0.5%, tare da iyaka na ₦10,000.

CBN ya ce wannan sauyi yana da nufin ƙarfafa amfani da hanyoyin biyan kuɗi na zamani, bunƙasa sabbin ayyukan kuɗi, da kuma faɗaɗa shigar jama’a cikin harkar banki a Najeriya.

24/04/2026

Aure da dadi, yanzu shagwaba ma na cikin soyayya fa.
Wadanda basu yi ba Allah Ya kawo lokacin you are missing alot😅

Haka zan rubuta a status dina a daren farko🥰😂

Address

Amarawa Illela
Sokoto
843101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AlameZone posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to AlameZone:

Share