Tijjaniya Media Bodinga

Tijjaniya Media Bodinga Fadakarwa

11/08/2023

Duk da sunsan cewa Kafirta musulmi/Cin mutuncin sa ba koyarwar Annabi ﷺ bane, Amma haka suke Kafirta mutane da sunan Ahlus sunnah

04/08/2023

Kafin ka yi wata magana, ya k**ata ka yi wa kanka tambayoyi akan abin da za ka fada: shin yaya gaskiya da ingancin wannan magana da za ka yi? Shin ma wai akwai bukatar ka yi wannan maganar? Kuma mene ne amfaninta? Idan har ka gaza samun amsa mai kyau game da wadannan tambayoyi, to bai k**ata ka yi maganar ba tun farko..

Sheikh sale kaura

03/08/2023
AlhamdulillahSheikh Tijjani  Sani Auwal  Ya Zama Sabon Kwamishinar Addinai na jihar kano  Dan Sayyida Aisha jikan Shekh ...
03/08/2023

Alhamdulillah

Sheikh Tijjani Sani Auwal Ya Zama Sabon Kwamishinar Addinai na jihar kano Dan Sayyida Aisha jikan Shekh Ibrahim Nyass RTA.
Allah ya taya riko yasa a gama lafiya amin.

Maulana Prof. Ibrahim Maqari  yana cewa;Bidi'a ta farko a tarihin Musulunci ita ce bidi'ar khawarij ta kafirta Musulmi, ...
02/08/2023

Maulana Prof. Ibrahim Maqari yana cewa;
Bidi'a ta farko a tarihin Musulunci ita ce bidi'ar khawarij ta kafirta Musulmi, kuma dalilinta shine shagala da ibada da wofintar da ilmi..

Al'umma bata taɓa wofintar da ilmi da safe ba, face kafin maraice gidajenta sun koma kufai.

02/08/2023
31/07/2023

Mun barran ta ga Makasan Imamu Hussain A.s da Masu Mara Musu Baya, Ya Allah Ka shaida!

Sheihk Nasir Sheikh Ado Musa

29/07/2023
29/07/2023
TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYASS RA....Babban Malamin Musulunci Sheikh Ibrahim Inyass RA Ya Cika Shekaru 47 Da Rasuwa.Sheik...
26/07/2023

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYASS RA.
...Babban Malamin Musulunci Sheikh Ibrahim Inyass RA Ya Cika Shekaru 47 Da Rasuwa.

Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq an haife shi a ranar (26/07/1900) a kasar Senegal, mahaifin sa Alhaji Abdullahi Tijjani, Sheikh Ibrahim ya kasance shugaba kuma jagoran sufanci da darikar Tijjaniyya a Senegal da yammacin Africa.

Ya tashi bisa kularwar mahaifinsa, ya haddace Alkur’ani mai girma a hannun mahaifinsa A cikin kananan shekaru Yafa wallafa littafi yana da shekaru 21 a duniya.

Sheikh Ibrahim Inyass yana da mabiya masu dumbin yawa a duniya, mabiya darikar Tijjaniya ya kasance mutun mai muhimmancin a cikin rayuwar mabiyan sa wurin koyi da halayensa da dabi'unsa a cikin rayuwar su. Anyi masa shaida da soyayyan Annabi ﷺ. Da kuma riko da sunnar Manzon Allah SAW.

Sheikh Ibrahim Inyass shi ne dan Afirka ta Yamma na farko da ya jagoranci sallar a babban Masallacin Al-Azhar a Masar , bayan da aka yi masa lakabi da "Sheikh al-Islam". Kuma malami na farko da Sarki Faisal na Saudiyya ya ziyarta a kauyen sa (Kaolack) a Senegal.

Sheikh Ibrahim Inyass mutumin Afirka ne, ya kasance dan gwagwarmayar neman ƴanci a Afirka ta Yamma, saboda gudummawar da ya bayar don samun' Ƴanci a Ƙasashen Afirka. Ya kasance aboki kuma mai ba da shawara ga Shugaban Ghana na farko, Kwame Nkrumah, da aboko Ga Gamal Abdel Nasser da Sarki Faisal na Saudi Arabia. Kuma Sheikh Ibrahim kasance Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya tare da Faisal a matsayin Shugaba.

A shekarar 1937 lokacin da s**a haɗu da Shaykh Ibrahim a lokacin aikin Hajj a Makkah, Sarkin Kano, A Najeriya, Alhaji 'Abdullahi Bayero ya yi mubaya'a ga shehin kuma ya bayyana kansa a matsayin almajirin Sheikh Ibrahim. Wannan lamarin ya sa Sheikh Ibrahim ya sami amincewar da yawa daga fitattun shugabannin Tijānīyyah A Arewacin Najeriya da ma wasu da dama wadanda ba Yan Darikar ba.

Alhaji Abdulmalik Atta basarake ne daga Okene kuma Babban Kwamishina na farko a Najeriya A Kasar Ingila, yana daya daga cikin manyan almajiran Sheikh Ibrahim da kuma surukin shehin ta hanyar ‘yarsa Sayyida Bilkisu. Shaykh Ibrahim ya zama sanannen kuma jagoran darikun sufaye) a ko'ina cikin yankunan Kasar Hausa na Yammacin Afirka. Yana da miliyoyin Almajirai a duniya, yayi rubuce-rubuce da dama kusan sama da 75 a rayuwar sa.

Sanadiyar Shehu Ibrahim Inyass RTA Ne Gwamnatin Najeriya Ta Sanya Hutun Maulidi Ya Zamo Doka A Kasa, Bayan Shehu Ya Zo Taya Najeriya Murnan Samun 'Yanci A Shekarar lokacin ya gana da Firar minista na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, sai Shehu ya bashi shawara cewa tunda kai Musulmi ne, ya k**ata ka sanya ranar Maulidi ya zamo ranar hutu a Najeriya.

Sheikh Ibrahim Inyass mabiyin addinin Islama, Mazhabar Maliki, Akida Ash'ariyya, Darikar Tijjaniyya. Sheikh Ibrahim Inyass ya rasu ranar 26 Yuli 1975 (shekaru 74) a wani asibitin St Thomas' Hospital, London, dake kasar United Kingdom.

Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa ya jaddada rahma a gare shi Albarkacin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaili Wasallam. Amiin

Rubutawa Da Tattarawa;
Babangida Alhaji Maina (Tijjaniyya Media News
25/07/2023 - 7/Muharram/1445.

Makarantun Gyaran Zuciya Hanyoyi Ne Na K**ala Da Ƙarin Kusanci Amma Sharadin Aljannah, Shine Bin Shari'ar Manzon Allah S...
25/07/2023

Makarantun Gyaran Zuciya Hanyoyi Ne Na K**ala Da Ƙarin Kusanci

Amma Sharadin Aljannah, Shine Bin Shari'ar Manzon Allah Sau Da Ƙafa

Sababin Aljannah Kuma Shine Cikawa Da Imani

👉Maulana Prof. Ibrahim Maqarii

KABARIN IMAMU BUSIRI (Mai Kasidar Al Burdah, Mawlaya Sali Wa Salim Da'iman)Wannan ita ce kabarin IMAMU BUSIRI (Imam Shar...
22/07/2023

KABARIN IMAMU BUSIRI (Mai Kasidar Al Burdah, Mawlaya Sali Wa Salim Da'iman)

Wannan ita ce kabarin IMAMU BUSIRI (Imam Sharaf al-Din al-Busiri) mai kasidar Al Burdah a Masar. Watarana Imam Busiri yana barci sai ya ga Manzon Allah SAW yace masa ka karanta abinda ka rubuta. Daya farka daga barci sai ya fara wakar Mawlaya Sali Wa Salim Da'iman, yanzu yana daya daga cikin fitattun wakoki a duniya.

Imam Busiri an haife shi a garin Beli Suef shekara 1213, yayi wafati a shekara 1294, an masa makwancin a Alexandria dake kasar Epgyt.

Allah ya jaddada masa rahma ya gafarta masa Allah ya sadashi da Manzon Allah SAW. Amiin

Babangida A Maina
Tijjaniyya Media News

Innalillahi Wa'inna Ilahir Raji'un Babban malamin Islama kuma dan Tijjaniyya Shaykh Abdulbaki El-Hüseyni ya rasu a Turke...
17/07/2023

Innalillahi Wa'inna Ilahir Raji'un

Babban malamin Islama kuma dan Tijjaniyya Shaykh Abdulbaki El-Hüseyni ya rasu a Turkey.

Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa, ya yafe masa kura - kuran sa. Amiiiin Yaa Allah

YANZU-YANZU: Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA Ya Bayyana Cewa Yana Bukatan Kowa Ya Yafe Masa Albarkacin Alkur'a...
13/07/2023

YANZU-YANZU: Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA Ya Bayyana Cewa Yana Bukatan Kowa Ya Yafe Masa Albarkacin Alkur'ani Mai Girma, Shima Ya Yafe Wa Kowa.

Shehin Malamin Musulunci Kuma Babban Jagoran Darikar Tijjaniyya A Duniya Ya Bayyana Hakan Ne A Birnin Tarayya Abuja Yau Alhamis 13/07/2023.

Allah Ya Kara Wa Maulana Sheikh Dahiru Lafiya Da Nisan Kwana Albarkacin Annabi ﷺ. Amiin

Tijjaniyya Media News

FIQHUN DARIQA 001Dariqa wata hanya ce ta saduwa da qarin neman kusanci da Allah, ta hanyar yawaita nafilfili bayan cika ...
13/07/2023

FIQHUN DARIQA 001

Dariqa wata hanya ce ta saduwa da qarin neman kusanci da Allah, ta hanyar yawaita nafilfili bayan cika farillai.
Yin Dariqah ba dole ba ne, domin Allah Ta'ala Ya ce

فمن شاء اتخذ إلى ربه سبيلا
(المزمل ١٩/الإنسان ٢٩)

Ma'ana (Duk wanda ya so -bisa radin kan shi- sai ya k**a hanyar da za ta sada shi zuwa ga Ubangijin shi) Surah ta 73:19 da kuma 76:29

At Morocco Sheikh Prof Ibrahim Ahmad maqariTareda Sheikh Siraj Muhammad kauora
12/07/2023

At Morocco Sheikh Prof Ibrahim Ahmad maqari
Tareda Sheikh Siraj Muhammad kauora

Wannan shine dan'uwan Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass wato Sheikh Muhammad Khalifa, tarihi ya tabbatar mana da haka. Alla...
09/07/2023

Wannan shine dan'uwan Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass wato Sheikh Muhammad Khalifa, tarihi ya tabbatar mana da haka. Allah ya kara kusanci ga Manzon rahma Annabi ﷺ.

Tijjaniyya Media News

29/06/2023
A KARSHE DAI NESA TA ZO KUSA.  Gagarumin yunkurin da muka dauko karkashin inuwar Ahlullahi Global Service, na kokarin sa...
23/06/2023

A KARSHE DAI NESA TA ZO KUSA.

Gagarumin yunkurin da muka dauko karkashin inuwar Ahlullahi Global Service, na kokarin samar da wata hanya da zai sawwake mana cimma muradunmu (Tijjanawa) cikin abinda ya shafi maslahar duniyarmu, k**ar samar da makarantu, da kuma samar da ayyukan yi ga jama'armu masu karamin karfi, samar da gidajen marayu da sauransu ya dauko hanyar tabbata sak**akon wani irin namijin kokari da da wani dan uwa mai yawan himma yayi da ya k**ata mu yunkura wajen dafawa namijin gwagwarmayar da yayi.

Dama ce wacce manyan Kungiyoyi dadama s**a jima suna yunkurin samu, wasunsu sun yi dacen samu, a yayin da mu kuma ALLAH ya kawo mana shi cikin himma da jajircewar Sayyadi Babangida Alhaji Maina .

1- Yadda tsarin yake shi ne Akwai tsari da kamfanin MTN suke da shi mai suna "Postcom ko kuma Closed User Group (CUG)" yadda al'amarin yake, akwai wani tsari na layi da samarwa wanda suke sayar da shi N800 (Dari Takwas), amfanin layin shi ne, idan ka mallake shi, to zaka kira duk wanda yake da irin wannan layi tsawon wata guda a sub na N800, wato idan ka mallaki guda ka Mallakawa Mahaifi, ko Mahaifiya, Saurayi ko Budurwa, Amini ko Aboki, to za kuyi ta waya har na tsawon wata guda a sub da ake N800, idan muka duba yawan kudade da muke kashewa kullum a kira, lallai wannan rahusa ce ga kowannenmu. Bugu da kari idan kana da layinka na MTN da kake amfani da shi, to za'a saita maka shi zuwa wannan tsari ba tare da wani matsala ba.

2- Amfaninsa wajen cimma manufar da muka dauko, idan akace kowannemu zai ke bayar da Naira 50 a sati, duk da za'a iya to amma abune mai gajiyarwa, amma shi wannan tsarin shi ne akwai yarjejeniya da kamfanin MTN, duk wanda ya mallaki wannan layi ta wasidar wannan Gidauniya, to zai zamo zasu ke ware wani Percentage zuwa asusunta da kuma asusun ainashin kamfanin Postcom ko kuma Closed User Group (CUG), wanda idan aka samu mutane dayawa, to lallai ne da yardar ALLAH mafarkanmu zasu gaskata kwarai da gaske.

3- Idan tsarin ya tabbata, za'a yi kokarin samar da tsayayyun wakilai a cikin kowacce jiha, za'a biya kowa ladar kokarinsa cikin abinda ya sawwaka (Domin a karfafi himmarsa), za'a ke bayyana ababen da aka samu a wasu lokuta kayyadaddu, sannan kuma za'a ke bayyana ababen da ake son aikatawa bayan an bi hanyar da ta dace , za'a aiwatar da komai a bude, za'a baiwa kowa amsa da zai gamsar da shi gwargwadon tambayarsa, sannan kuma muna kyautatawa ALLAH zato zai dafa mana wajen kaiwa zuwa ga nasara.

4- Lallai wannan al'amari idan ya tabbata to zai kasance cikin taka-tsan-tsan matuka, duk wasu matakai na hukuma za'a tabbatar an bi su, tare da matukar kiyayewa, a gefe guda za'a aikatu tukuru domin tabbatar da manufa.

5- Lallai duk wani aikin Alkairi bai rasa fuskantar kalubale, amma domin saukaka daukar alhakin bayin ALLAH da bukatar mutum yayi tambaya cikin abinda bai fahimta ba, a bashi amsa, yaso idan ma zai kalubalanta sai yayi yana mai yakini ba bisa rashin sani ba.

Muna rokon ALLAH, ya yassare mana nasararori a hannuwanmu, ko a hannunwan yan uwanmu, ya bude mana hanyoyin riskarsu alfarmar MANZON ALLAH (S.A.W).

ALHAMDULILLAH.
✍️ Sufi Media Connect

Masha AllahSheikh Abulfathi Assani AttijjanyZakin Faira of Africa
17/06/2023

Masha Allah
Sheikh Abulfathi Assani Attijjany
Zakin Faira of Africa

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!GAGARUMIN TARON DA FURSANUL FAIDHA ZATA GUDANAR GOBE A GARIN BAUCHI.MAUDU'I:🟠 Bada kariya g...
14/06/2023

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

GAGARUMIN TARON DA FURSANUL FAIDHA ZATA GUDANAR GOBE A GARIN BAUCHI.

MAUDU'I:
🟠 Bada kariya ga janabin Annabi S.A.W daga masu kai masa hari.
🟠 Shin girmama Annabi S.A.W yana cin karo da Tauhidi?

MALAMAI MASU GABATARWA:
👉🏽 Khalifa Sheikh Abubakar Madatai.
👉🏽 Sheikh Shehi Mai Jama'a.
👉🏽 Sheikh Munir Adam Koza.
👉🏽 Sheikh Mustapha Adinga.
👉🏽 Sheikh Arabi Sheikh Mudi Salga.
👉🏽 Sheikh Ahmad Isa Jaja.
👉🏽 Sheikh Abulfathi Sani Attijany.
👉🏽 Sheikh Junaidu Abubakar Sadiq.
👉🏽 Sheikh Nasiru Sheikh Ado.
👉🏽 Sheikh Burhanudden Sheik Aminu M/Goje
👉🏽 Sheikh Hadi Musa.......
👉🏽 Da sauran Shehunai da Khalifofi na Zawiyyoyi dabam-dabam daga Jihar Kano.

WURIN TARO:
KOFAR GIDAN MAULAN MU SHEIKH AMINU BAKIN KURA BAUCHI.

🛑 LOKACI: KARFE 8:30PM NA YAMMA

ALLAH YA BADA IKON HALARTA AMEEN 🙏🏾

~ZIYARRA 1444/2023Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi (Khadimul_Fayda_General) Yayinda Yakaiwa Wasu daga Cikin Manyan Ma...
12/06/2023

~ZIYARRA 1444/2023

Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi (Khadimul_Fayda_General) Yayinda Yakaiwa Wasu daga Cikin Manyan Maluma na Garin Bauchi, da wasu sashi na Makarantun Shehi, Inda Ziyarar ta Hada da Katafaren Masallacin Shehi Da ake Ginawa na Bauchi Central Market.

Allah yataimaki Khadimul Fayda yakara masa himma yakuma jamana kwanan Shehi da Lapia wadatatta Albarkar Manzon Allah s.a.w❤🤲

📝Al'ameen Ibraheem Cisse
~Sheikh Dahiru Usman Bauchi New Media Team]

11/06/2023
MARIGAYI MUHAMMAD ALI Yana Cewa: "Ni Ba Na Shan Taba(Sigari), Amma Na Kan 'Dauki Ashana Na Ajiyeta a Aljihuna, Duk Lokac...
11/06/2023

MARIGAYI MUHAMMAD ALI Yana Cewa:

"Ni Ba Na Shan Taba(Sigari), Amma Na Kan 'Dauki Ashana Na Ajiyeta a Aljihuna, Duk Lokacin Da Na Ji ZUCIYATA Ta K**a Hanyar Kutsawa Zuwa Sa6o, Sai Na 'Kyasta Ashanar Na 'Kona Tafin Hannuna Da Ita,

Sannan Sai Na Cewa Raina: In Har Ba Ki Iya Jure Wannan 'Yar Wutar Ba To, Ta Ina Za Ki Iya Jure Wutar Jahannama".

ALLAH Ya Gafartawa Marigayi Muhammad Ali, Ka Kai Rahama Kabarinsa, Mu Kuma Idan Na Mu Lokacin Yayi ALLAH Yasa Mu Cika Da Kyau Da Imani Ameeeeeen.

Address

Bodinga
Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tijjaniya Media Bodinga posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share


Other Media/News Companies in Sokoto

Show All