21/04/2025
Kun san wanene wannan?
Shi ne Sheikhul-Islam, kuma ƙarshe a jerin manyan masu fassarar Al-Qur’ani. Shi ne Al-Allama, masani ne mai zurfin ilimi a fannin harshe, wanda ilimi ya lullube shi daga kan kansa har zuwa yatsun ƙafafunsa.
Yana da ƙwaƙwalwa mai ƙarfi, basira mai zurfi, da kuma ƙarfin himma da ƙoƙari da ba a saba gani ba. An haife shi a shekarar 1325 Hijriyya a garin Kiffa, kasar Mauritaniya.
Rayuwarsa:
Ya rasa mahaifinsa yana cikin karatun Juz Amma, amma hakan bai hana shi ci gaba ba. Ya kammala haddar Al-Qur’ani yana da shekaru 10 kacal, hannun kawunsa. Ya koyi rubuta Al-Qur’ani daga ɗan kawunsa, wanda ya koyar masa da tajwid sannan ya bashi izini (ijāzah) yana da shekaru 11.
Ya karanta wasu gajerun littattafan fiqhu na Malikiyya, da adabi, da ilimin harshe, da tarihin zuriyya a wajen matar kawunsa. Haka kuma ya koyi ilimin mantiƙi da ƙa’idojin muhawara ta hanyar karatu da nazari.
Himma da ƙwazo:
Yana da ƙwaƙwalwa mai ban mamaki – yana haddace baitocin larabawa da yawa, mafi yawan hadisai a cikin Sahih al-Bukhari da Muslim, Alfiyyah na Ibn Malik, Maraqi as-Su’ud, Alfiyyah na Al-‘Iraqi, da sauran rubuce-rubucen manzanni.
Ya ce: “Babu wani aya a cikin Al-Qur’ani da ban nazarce shi da kaina ba.”
Kuma ya ce: “Duk wani bayani da magabata s**a faɗa akan wata aya, to yana tare da ni.”
Littafinsa mashahuri:
Ya rubuta littafin "Daf’u Ihām al-Idtirāb ‘an Āyāt al-Kitāb" a cikin kwanaki 15 kacal, a lokacin hutu na jarrabawa a shekarar 1373 Hijriyya. Littafin yana da shafuka 390, an wallafa shi a Dār ‘Ālam al-Fawā’id.
Yana karanta shafi guda daga Al-Qur’ani fiye da sau 100 kafin ya fassara.
A wata rana ya fassara kalmar Allah da ke cewa: ﴿اهْبِطُوا مِصْرًا﴾ a tsawon sa’o’i 4, ba tare da maimaita kansa ba ko barin ma’anar ayar.
Ya fassara Al-Qur’ani sau biyu gaba ɗaya, sannan ya rasu a yayin karantarwa akan ayar:
﴿أُولَٰئِكَ حِزْبُ اللَّهِ ۚ أَلَا إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ﴾ – yana cikin fassarar sau na uku.
Halin sa da dabi’unsa:
– Idan aka tambaye shi abu game da harshen Larabci kuma ya ce “ban sani ba”, to ba sai an buɗe ƙamus ba, domin ya riga ya bincika.
– Zai iya bincike akan wata mas’ala har na kwana ɗaya da dare.
– Yana haddace Lisān al-‘Arab na Ibn Manzur gaba ɗaya.
– Ba zai taɓa lamuntar zagin wani a majalisa ba.
– Bai san bambancin takardun kuɗi ba.
– Bai taɓa bayar da fatawa a mas’alolin saki ba.
Rasuwarsa:
Ya rasu da safe ranar Alhamis, 17 ga Zul-Hijjah, shekarar 1393 Hijriyya, bayan ya kammala aikin Hajji. An yi masa salla a Masjidul-Haram, sannan an sake masa sallar Salatul-Gha’ib a Masjidun Nabawi. An binne shi a Maqbarat al-Ma‘lā a Makka.
Shi ne Sheikh al-Allāma Muhammad Al-Amin Ash-Shanqīṭī – Allah ya jikansa da rahama, ya ba shi mafi girman daraja a Aljannah.
Daga Muhammad Ismail Ali.