12/06/2026
Hisbah Ta Cafke Mutane 26 A Samame Da Takai Hubbare
Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto ta gudanar da wani samame a wasu wurare biyar da ke cikin birnin Sokoto, inda ta cafke mutane 26 maza da mata.
Wuraren da aka kai samamen sun hada da Nakasari, Hubbare, Offer Road, Babbar Tashar Motar Sokoto da kuma Giginya Otal. A cewar hukumar, an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Sokoto.