31/07/2026
TARIHIN MARIGAYI ALHAJI ABUBAKAR ALHAJI SARDAUNAN SOKOTO
Marigayi Alhaji Abubakar Alhaji KBE, OFR (wanda aka sani Tripple A) fitaccen ma’aikacin gwamnati ne, gogaggen ɗan siyasa kuma jinin sarautar Sakkwato. Ya fito ne daga zuriyar Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ta ɓangaren mahaifinsa, Muhammadu Buhari Dan Shehu. An haife shi a gidan Sarkin Shanu Muhammadu Sani (Alhaji Alhaji), ya yi karatunsa a Kano da Katsina Government College kafin ya wuce Birtaniya, inda ya kammala digiri a fannin Tattalin Arzikin Siyasa daga Jami’ar Reading, sannan ya halarci ƙarin horo a Hague Institute of Social Studies da IMF Institute.
Ya fara aikin gwamnati a shekarar 1964 a Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, inda ya yi aiki a muƙamai daban-daban har ya zama Babban Sakatare a ma’aikatun gwamnati. Daga baya ya zama Karamin Ministan Kasafi da Tsare-tsare, sannan tsakanin 1990 zuwa 1991 ya riƙe muƙamin Ministan Kuɗi na Tarayyar Najeriya.
Alhaji Alhaji ya wakilci Najeriya a matsayin Babban Kwamishina a Birtaniya, inda ya taka muhimmiyar rawa a harkokin diflomasiyya da tattalin arziki.
A ɓangaren sarauta kuwa, an naɗa shi Sardaunan Sakkwato a shekarar 1990, sarautar da ta kasance babu mai riƙe da ita tun bayan rasuwar Sir Ahmadu Bello a 1966.
Marigayi ya shahara da nagarta, ƙwarewa da sadaukarwa wajen yi wa ƙasa hidima, kuma tarihinsa ya kasance abin koyi ga masu tasowa.
Allah Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Amin.