16/07/2025
Aisha Buhari, Saki da Ikirarin Neman Gafara
Daga Farooq Kperogi
Wasu mutane na yadawa cewa Aisha Buhari ta ce mijinta, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya roƙe ta da ta nemi gafara daga 'yan Najeriya a madadinsa.
Ba zan iya tabbatar da sahihancin wannan magana ba, amma abin da nake da tabbaci da shi shi ne kafin mutuwar Buhari, shi da Aisha sun rabu da aure.
Sun yi saki, kuma Aisha ta koma amfani da sunanta na haihuwa — Aisha Halilu.
Idan ka lura da kyau, za ka gane cewa Aisha ba ta bi Buhari zuwa Daura ba bayan ya kammala mulki. Har ila yau, lokacin da ya koma Kaduna daga baya, shi kaɗai ne.
A gaskiya ma, lokacin da ya kamu da rashin lafiya, kuma aka ba da shawarar cewa Aisha ta je Landan ta kula da shi, rahotanni sun ce ta yi jinkiri domin ba ta ƙara zama matarsa ba. Sai daga baya ta tafi kwanaki kaɗan kafin ya rasu — bayan matsin lamba mai ƙarfi.
Yanzu ma da ake cikin zaman makoki, ana ganin Aisha na cikin ruɗani dangane da matsayin da take a ciki.
Saboda haka, ina da matuƙar sha'awar sanin a wane lokaci ne da kuma a ina Buhari ya ce ta roƙi 'yan Najeriya su gafarta masa? Kuma a ina ne Aisha ta faɗi haka?