07/10/2025
A Yau Angabatar Da 2026 Budget Discussion Na Yankin Sokoto South Senatorial Zone, Wanda Yake Shine Na Farko A Tarihin Wannan Jaha Tamu Mai Albarka Sokoto, Wanda Ministry Of Budget And Economic Planing In Collaboration With Ministry For Local Government Affairs Sokoto Suka Gabatar A Garin Tambuwal.
Babban Mai Masaukin Baki Maigirma ALGON Chairman Na Jahar Sokoto Kuma Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Tambuwal Hon. Abba Shehu Tambuwal, Shine Wanda Ya Tarbi Manyan Baki Wadanda Sunkazo Wannan Taro.
Shidai Wannan Taro Ya Kunshi Kananan Hukumomin Bodinga, Dange Shuni, Yabo, Shagari, Tureta, Kebbe Da Kuma Tambuwal Local Government, Inda Kowane Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Wadannan Kananan Hukumomin, Sukazo Da Kansu Tareda Tawagarsu, Domin Gabatarda Bukarsu A Kasafin Kudi Na Sabuwar Shekarar 2026.
Acikin Jawabin Maraba Wanda Maigirma ALGON Chairman Na Jahar Sokoto Hon. Abba Shehu Tambuwal, Ya Gabatar Yayi Jinjima Matuka Zuwaga Hon Commissioner Ministry Of Budget And Economic Planing Sokoto Dr. Abubakar Muhammad Zayyana.
Bisaga Ba Maigirma Gwamnan Jahar Sokoto H.E Dr Ahmad Aliyu Sokoto Fcna Shawarwari Masu Kyau Wajan Fito Da Wannan Tsarin Budget Discussion Wanda Yake Shine Na Farko A Tarihin Jahar Sokoto, ALGON Chairman Yace Wannan Tsarin Mai Kyau Ne.
Domin Gwamnatin Jahar Sokoto Karkashin Jagorancin Maigirma Gwamna Amadun Baba Alu, Gwamnatin Al'umma Ce Wannan Tsari Yanada Kyau, Domin Jin Ra'ayin Mutane Gameda Abinda Sukeson Gwamnati Tayi Musu A Kasafin Kudi Na Sabuwar Shekarar 2026.
Maigirma Commissioner Ministry Of Finance Sokoto Hon. Muhammadu Jabbi Shagari Ubandoman Shagari, Yayi Jawabi Mai Kyau, Inda Ankaba Kowace Local Government Dama Su Bada Wakilinsu Ya Fadi Aikin Da Sukeson Gwamnati Tayi Musu A Kasafin Kudi Na Sabuwar Shekarar 2026.
Dr. Abubakar Muhammad Zayyana, Ya Bayyana Makasudin Yin Wannan Budget Discussion, Inda Yace Maigirma Gwamnan Jahar Sokoto Gwamnan Al'umma Ne, Yana Da Bukatar Sanin Kowace Local Government Su Fadi Aikin Da Sukeson Ayi Musu Inda Yace Wannan Shine Karon Farko Fitowa Da Wannan Tsarin A Tarihin Jahar Sokoto.
District Head Na Kowace Local Government Dake Wannan Yanki Namu Na Sokoto South Senatorial Zone, Duka Sun Samu Halartar Wannan Taro, Tareda Dukkan Hakimansu Hakama Shuwagabannin Jam'iyar APC Na Local Government, Dana Mazabinne Na Wannan Yanki Namu Duka Sun Samu Halartar Wannan Taro, Tareda Women Leader Ta Kowace Local Government.
Hakama Kansilolin Kananan Hukumomin Wannan Yanki Namu, Duka Sun Samu Halartar Wannan Taro Wanda Speaker Tambuwal Local Government Council Hon. Nasiru Kwazo Jabo, Ya Jagoranta Matsayinsa Na Speaker Na Tambuwal Local Government Wanda Yake Tambuwal Ake Wannan Taro.
Hakama Statistician General Na Sokoto State, Permanent Secretary Ministry Of Religious Affairs Sokoto, Da Permanent Secretary Ministry Of Budget And Economic Planing Sokoto, Da Director Planning Ministry Of Religious Affairs Sokoto Duka, Sun Samu Halartar Wannan Taro.
Malaman Addinin Musulunci Na Kowace Local Government Sun Samu Halartar Wannan Taro, Inda Liman Maniru Na Masallacin Jumu'a Na Gidan Buhari Dan Shehu, Wanda Maigirma Sarkin Yamman Sakkwato Shine Wanda Ya Gina Wannan Masallaci, Shine Ya Jagoranci Bude Taro Da Addu'a Da Kuma Rufe Taro Da Addu'a Da Fatar Allah Ya Maida Kowa Gidansa Lafiya Amin.