22/10/2025
Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun hallaka wata ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya, Jihar Kaduna, mai suna Hadiza Musa, wadda ta kasance mataimakiyar shugabar sashen karbar haihuwa a asibitin.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da yammacin Asabar, lokacin da marigayiyar ke dawowa daga aiki. Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce matarsa ta hau babur din haya misalin karfe 6:30 na yamma, amma daga baya wasu s**a kai mata hari domin kwace wayarta.
A cewarsa, bayan barayin sun sace wayarta, sai s**a jefar da ita a gefen t**i kusa da filin Idi na Mallawa, Tudun Wada Zariya. Wani mutum mai taimako ne ya kai ta asibiti, daga bisani aka tura ta zuwa Asibitin Koyarwa na ABU, Shika, inda likitoci s**a tabbatar da rasuwarta.
Sakataren Asibitin Gambo Sawaba, Abdulkadir Balele Wali, ya bayyana marigayiyar a matsayin kwararriya mai jajircewa da sadaukarwa wajen ceton rayukan jama’a, yana mai cewa rasuwarta babban rashi ne ga asibitin gaba ɗaya.
Majiyarmu tayi kokarin Jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Kaduna, Mansur Hassan, sai hakan yaci tura.