06/03/2025
HALARTAR TARON DA KUNGIYAR HADINKAN MUSULMI TA DUNIYA, TA KIRA, AKAN SAMO HANYOYIN DA S**A DA CE, DOMIN SAMUN HADINKAN KUNGIYOYIN MUSULUNCI, DAKE CIKIN KASASHEN MUSULMI NA DUNIYA, TARON DA YA GUDANA CIKIN DARENNAN NA JUM'AH TA FARKO A CIKIN WANNAN WATA NA RAMADHAN, NA SHEKARAR 1446.H A BIRNIN MAKKAH, ABIN GIRMAMAWA, KUMA DAB DA WURI MAFI DARAJJA A DUNIYA, WATAU HARAMIN MAKKAH, INDA DAKIN ALLAH MAI ALFARMA YAKE.
A Cikin Daren nan na Jum'ah, 06/ga Watan Ramadhan Maigirma Mai yiwa Jama'a Hidima, Kuma Wakili A Majalisar Koli ta Majalisar Hadinkan Musulmi ta Duniya Mai Mazamni A Birnin Makkah Abin Girmamawa, Dottijo. Dr. Aliyu Magatakarda Wamakko, Sarkin Yamman Sakkwato, Sarkin Yakin Sakkwato.
Ya Samu Halartar Taron da Wannan Kungiya ta Hadinkan Musulmi ta Duniya ta yi Masa, Karkashin Jagorancin Shugaban Kungiyar Sheikh Abdulkarim Muhammad Al- Isah, Inda Taron Zai Tattauna Hanyoyin da Za'a Samu Hadinkan Musulmi na Duniya Tare da Toshe Duk Wata Kafa Wadda Zata Iya Kawo Sabani ga Kungiyoyin Musulunci na Duniya.
Muna Rokon Allah da ya yi Musu Muwafaqa ga Dukkan Abinda Za su Tattauna Kuma yasa Ayi Lafiya Akare Lafiya Cikin Nasara.
Rubutawa, Malam Bashir Gidan Kanawa.
Alhamis, 06/Ramadhan, 1446H dai dai da 06/03/2025