DBM HAUSA

DBM HAUSA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from DBM HAUSA, Media/News Company, No 20 Ahmad Rufa'I Road, sokoto, Sokoto.

DBM Hausa na kawo muku Labaran Hausa, documentary, da sauran abubuwan jan hankali cikin harshen Hausa, domin samar da Galihu ga marasa murya
DBM Hausa Gaskiyar Labari

lambar WhatsApp 08137962522

https://www.youtube.com/

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su nazarci alkawuran ’yan siyasa kaf...
14/09/2026

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su nazarci alkawuran ’yan siyasa kafin yanke shawarar wanda za su zaɓa a 2027.

Sultan ya ce bai kamata ’yan Najeriya su yanke hukunci bisa son zuciya ko jam’iyya kawai ba, sai sun duba abin da ’yan takarar s**a yi alkawarin cimmawa.

Ya kuma buƙaci masu zaɓe su tantance tarihin ’yan takara da irin ayyukan da s**a gabatar a baya, domin sanin waɗanda za su iya cika alkawuransu.

A cewarsa, ya kamata ’yan Najeriya su yi amfani da ƙuri’arsu yadda ya kamata, tare da fifita muradun ƙasa wajen zaɓen shugabanni.

Sarkin Musulmin ya jaddada muhimmancin shiga zaɓe cikin lumana da kuma zaɓar shugabannin da za su yi aiki domin cigaban ƙasa da jin daɗin al’umma.

DBM Hausa

Farashin man fetur ya sake tashi a kasuwannin duniya bayan rufe wani bututun mai mai muhimmanci a Saudiyya, da gazawar t...
14/09/2026

Farashin man fetur ya sake tashi a kasuwannin duniya bayan rufe wani bututun mai mai muhimmanci a Saudiyya, da gazawar tattaunawar diflomasiyya da kuma hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a yankin Gulf.

Farashin ɗanyen man Brent ya kai dala 108 kan kowacce ganga.

A ranar Juma'ar da ta gabata, Saudiyya ta sanar da cewa ta rufe bututun man, bayan wasu hare-hare da Iraqi ta kai da jiragen marasa matuƙa, sun yi masa ɓarna.

Tun da farko masarautar Saudiyya ta zargi mayaƙan ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran da kai irin waɗannan hare-hare.

A ɓangare guda kuma, ƙasar Oman ta ɗage wani taro da aka shirya yi a ranar Litinin tsakanin Iran da ƙasashen Larabawan da ke yankin Gulf domin tattauna batun mashigar Hormuz. Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya.

BBC Hausa
DBM Hausa

Gobara ta tashi a Babbar Kasuwar Sokoto, amma a halin yanzu an shawo kan wutar.DBM HAUSA
13/09/2026

Gobara ta tashi a Babbar Kasuwar Sokoto, amma a halin yanzu an shawo kan wutar.

DBM HAUSA

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran na matuƙar son cimma yarjejeniya da Amurka, yana mai cewa ƙasar na ci gaba da ne...
13/09/2026

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran na matuƙar son cimma yarjejeniya da Amurka, yana mai cewa ƙasar na ci gaba da neman a tattauna da ita.

Trump ya ce ya yi imanin cewa yaƙin da Amurka ke yi da Iran zai ƙare kafin ko kuma jim kaɗan bayan zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka.

"Iran na son cimma yarjejeniya. Suna ci gaba da kira na. Suna son cimma yarjejeniya, amma dole ne yarjejeniyar ta zama wadda ta dace. Ba zan amince da yarjejeniyar da ba yi daidai ba," in ji shugaban Amurkan ga manema labarai yayin gasar Irish Open.

Trump ya yi irin wannan magana a makon da ya gabata, inda a ranar Laraba 9 ga watan Satumba ya shaida wa manema labarai cewa yana ganin yaƙin da Iran zai ƙare "nan da nan bayan zaɓen Amurka", yana nufin zaɓen tsakiyar wa'adin da za a gudanar a watan Nuwamba.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Iran ta ce taron da za a gudanar gobe a Oman zai tattauna wata sabuwar hanya ta zirga-zirgar jiragen ruwa ta Mashigin Hormuz.

DBM Hausa

12/09/2026

“Za mu koyar da sama da mata dari sana’o’in hannu a yankin Magajin Gari,” inji Kungiyar Magajin Gari B APC Youth Mobilization.

DBM HAUSA

11/09/2026

Malam Musa Ayuba Lukuwa ya nemi magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, inda ya tabbatar musu cewa yana cikin ƙoshin lafiya.

DBM HAUSA

Mahukunta sun tabbatar da mutuwar yara ƴan makaranta aƙalla 24, a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa daga gobarar da ta tas...
11/09/2026

Mahukunta sun tabbatar da mutuwar yara ƴan makaranta aƙalla 24, a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa daga gobarar da ta tashi a cikin wasu makarantu biyu, a birnin Bukavu da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, lamarin da ya janyo ruɗani sosai.

An kuma bayar da rahoton mutuwar wasu manya a wajen, yayin da hukumomi ke bayyana fargabar ƙaruwar yawan mutanen da za gobarar ta kashe saboda akwai wasu da aka garzaya da su asibiti domin duba lafiyar su.

Hotunan da aka yaɗa na wajen da abin ya faru sun nuna ƙananan yara a kwance a ƙasa, a cikin asibiti, suna kuka saboda tsananin azabar ƙunar wuta.

Gidaje 300 wutar ta ƙona, kuma har yanzu ba a gano abin da ya tayar da ita ba.

Mahukunta sun ce lamarin ya faru ne a birnin Bukavu da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da ke ƙarƙashin ikon ƴan tawaye, inda ake fama da cunkoson jama'a.

Bayanan da mayaƙan ƴan tawaye da ke iko da wajen s**a fitar sun nuna cewa mutanen da s**a rasu sun kai 24, amma akwai fargabar adadin zai ƙaru.

Hotunan da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna ƙananan yara kwance a ƙasa, kuma da alama gawarwaki ne.

Shaidun da kamfanin dillanci labarai na Reuters ya zanta da su sun ce tun da rana aka kashe wutar, amma ana ci gaba da ganin hayaƙi da ke ɓullowa daga ƙarƙashin gine-ginen da aka rusa domin kashe gibarar.

Bukavu, babban birnin kudancin lardin Kivu kuma yankin da ya fi cunkoson jama'a a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya faɗa a ƙarƙashin ikon mayaƙan tawaye na M23 ne a watan Faburairun bara.

Amma gwamnati a Kinshasa ta wallafa sanarwa a shafin X, ba tare da ta bayyana yawan mutanen da gobarar ta kashe ba.

Sanarwar ta ce "Ma'aikatar ilimi da kula da ƴan ƙasa ta bayyana damuwa matuƙa kan mummunar gobarar da ta tashi,''

"An yi asarar rayuka da yawa kuma wasu da dama sun ji rauni. Ministan Ilimi na aikewa da ta'aziya ga iyalan waɗanda lamarin ya ritsa da su, kuma ya bayar da umarnin tantance halin da makarantun da abin ya shafa suke ciki, tare da tabbatar da ganin an ci gaba da harkokin karatu.''

Gobarar biyu sun faru ne bayan wata gobarar ta daban a ƙarshen makon da ya gabat a Kinshasa, inda aka samu asarar rayuka wajen turereniyar neman guduwa daga gobarar da ta tashi a wajen wani ɗakin taro ana tsakiyar biki.

Gwamnatin ƙasar ta bayar da umarnin tsaurara matakan rigakafi, kuma ta tura jami'ai a sannan ƙasar domin sanya ido da tabbatar da kaucewa tashin gobara a wuraren da mutane ke taruwa.

BBC Hausa
DBM Hausa

Rahotanni daga Unguwar Mabera da ke birnin Sokoto na cewa wani matashi ya daba wa Malam Musa Ayuba Lukuwa wuka jim kadan...
11/09/2026

Rahotanni daga Unguwar Mabera da ke birnin Sokoto na cewa wani matashi ya daba wa Malam Musa Ayuba Lukuwa wuka jim kadan bayan kammala Sallar Juma’a a masallacinsa.

Wani mazaunin unguwar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an garzaya da malamin zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Sai dai rahotanni sun ce matashin da ake zargin ya aikata lamarin ya jima a cikin masallacin tun kafin fara Sallar Juma’a, inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa a wajen.

Har yanzu ba a bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.

DBM Hausa

Wani babban jami'in Falasɗinu ya ce ba za a gudanar da zaɓen majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba ba...
10/09/2026

Wani babban jami'in Falasɗinu ya ce ba za a gudanar da zaɓen majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba ba, a maimakon hakan ya yi kira da a fara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

Jibril Rajoub, babban sakataren ƙungiyar wani tsagin Fatah da ke mulki a yankin Yammacin Kogin Jordan, ya shaida wa manema labarai a Ramallah cewa har yanzu ba a gabatar da jerin ƴan takara masu ƙarfi ba.

Ya ce zai dai fi sauƙi a fara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, wanda ake sa ran yi a farkon shekara mai zuwa, sannan a gudanar da wata tattaunawa ta ƙasa baki ɗaya.

Zaɓe na ƙarshe irin wannan a yankunan Falasɗinawa, an yi shi ne shekaru 20 da s**a gabata, inda ƙungiyar Hamas ta samu nasara.

BBC Hausa
DBM Hausa

Ministocin harkokin waje na Turkiyya, Masar, Indonesia, Jordan, Pakistan, Qatar, Saudi Arabia da Haɗaɗɗiyar Daular Larab...
09/09/2026

Ministocin harkokin waje na Turkiyya, Masar, Indonesia, Jordan, Pakistan, Qatar, Saudi Arabia da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun yi maraba da matakin da gwamnatin Birtaniya ta ɗauka na hana shigo da kayayyaki daga matsugunan haramtacciyar ƙasar Isra'ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye da kuma taƙaita ayyukan da ke da alaƙa da irin waɗannan matsugunan.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da s**a fitar a ranar Laraba, ministocin sun bayyana fatan cewa wannan mataki zai taimaka wajen jan hankalin al'ummar duniya su ɗauki irin wannan mataki bisa ga dokokin ƙasa da ƙasa da kuma hukunta kungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da suke da hannu a ayyukan haramtattun matsugannai.

Sun kuma yi maraba da sanarwar haɗin gwiwa kan mafita ta samar da ƙasashe biyu da ministocin harkokin waje na Canada, Denmark, Finland, Faransa, Iceland, Ireland, Norway, Poland, Portugal, Sifaniya, Sweden da Birtaniya s**a fitar.

Ƙasashe 12 sun tabbatar da aniyarsu ta gabatar da takunkumi da kuma goyon bayan takunkumin Turai kan cinikayyar kayayyaki daga haramtattun matsugunai a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, ko kuma su yi la'akari da waɗannan da sauran matakai bisa ga ƙa'idojin ƙasa da ƙasa.

Minisitojin ƙasashen takwas sun buƙaci al'ummarrin duniya da su ɗora a kan waɗannan matakai tare da ɗaukar matakai na zahiri don kawo ƙarshen ayyukan da ke tallafawa ko kuma ci gaba da matsayar da ƙasar haramtacciyar Isra'ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye.

Sun ce matakan da aka sanar sun yi daidai da dokokin kasa da kasa da kuma ƙudurorin Majalisar Dinkin Duniya masu alaƙa da su, ciki har da ƙudurin Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2334 da kuma shawarar da Kotun Duniya ta bayar a ranar 19 ga Yuli,

Sanarwar ta ambato wajibci kan dukkan ƙasashe na ƙin amincewa da yanayin da ya taso daga mamayar haramtacciyar ƙasar Isra'ila a yankin Falasɗinu a matsayin doka, kuma kada su bayar da tallafi ko taimako wajen wanzar da yanayin da mamayar ta haifar.

DBM HAUSA

Address

No 20 Ahmad Rufa'I Road, Sokoto
Sokoto
840253

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DBM HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share