20/04/2025
Sirrin Samun Kuɗi a Facebook Monetization:
A yau, Facebook yana daya daga cikin manyan hanyoyi da masu kirkirar Content ke amfani da su wajen samun kuɗi. Wannan tsari ana kiransa da Facebook Monetization, kuma yana da hanyoyi daban-daban da za ka iya cin gajiyar su idan ka fahimta da kyau. A cikin wannan muƙala, za mu bi mataki-mataki domin fahimtar In-Stream Ads, Reels, Gina page mai monetization, da sauran muhimman dabaru.
1: In-Stream Ads — Yadda Ake Saka Talla a Bidiyoyin Facebook
Menene In-Stream Ads?
In-Stream Ads su ne tallace-tallace da ke bayyana a tsakiyar bidiyonka lokacin da mutane ke kallo. Facebook yana saka wadannan tallace-tallace, kuma kai za ka samu kason kuɗin da aka samu daga kallon tallan.
Sharuddan Samun In-Stream Ads:
Kana bukatar shafi da:
Akalla 5 active videos a shafinka.
Kasamu Viewers masu tarin yawa
Ace Kanada active followers.
Yadda Ake Sanya In-Stream Ads:
1. Shiga cikin Facebook Creator Studio
2. Zaɓi Monetization > In-Stream Ads.
3. Duba eligibility.
4. Idan ka zama eligible, ka amince da terms and conditions ɗin su ta hanyar accepting.
5. Zaɓi bidiyonka da za a saka ads.
6. Saita nau'in tallan: before video (pre-roll), during video (mid-roll), ko after video (post-roll)
Yadda kakaeso tallan ya dinga bayyana a video ɗin Kenan.
> Tips: Yawaita yin bidiyo masu tsawon 3 minutes ko fiye domin In-Stream Ads yayi aiki sosai.
2: Facebook Reels — Samun Kuɗi Daga Reels;
Menene Reels Bonus Program?
Wannan wani tsari ne da Facebook ke biyan kuɗi ga masu kirkirar short videos (Reels) idan sun samu adadin views da engagements masu yawa.
Sharuddan Shiga:
Shafi ko Profile mai Professional Mode.
Ana buƙatar samun gayyata daga Facebook (invitation).
Samun ingantattun Reels(Video)da ke jawo hankalin mutane.
Yadda Ake Samun Kuɗi Daga Reels:
1. Tabbatar da shafinka yana Professional Mode.
2. Kirkiri reels masu kayatarwa da originality.
3. Yin reels akai-akai (at least 5 reels a sati).
4. Cika targets na views da engagements.
3: Yadda Ake Gina Page Mai Samun Monetization dawuri;
Matakan Gina Shafi:
1. Ƙirƙiri sabon page ko sabunta wanda kake da shi.
2. Sa hoton dake da alaƙa da content ɗin ka hoto mai kyau.
3. Rubuta description mai gamsarwa
4. Tas mabiya ta hanyar posting abun da yake jab hankali.
5. Yawaita amfani da videos fiye da rubutu kaɗai.
6. Kula da bin Facebook Policies sosai.
Muhimmin Bayani:
Kada kayi reposting content na wasu.
Yi amfani da keywords da hashtags masu kyau.
4: Dalilan Da Ke Hana samun Monetization!
Abubuwan da ke hana shafi samun monetization:
Karya Facebook Policies (dokar Monetization da Community Guidelines).
Fake Engagements: sayen likes, comments, ko fake views.
Copyright Violations: amfani da waƙa ko bidiyon wani ba tare da izini ba.
Misinformation: yada ƙarya ko labaran da ba a tantance ba.
Yadda Ake Guje Wa Wannan:
Samu sahihan mabiya ba fake ba
Yi amfani da dabarun maida content ya zama naka in yazama dole sai kayi amfani da content ɗin wasu.
Editing videos da rubuce-rubuce kafin wallafawa.
5: Facebook Content Strategies: Yadda Ake Ƙirƙirar content Mai saurin samun Monetization;
Ƙirƙiri bidiyo na nishadi, ilimi, ko abubuwan al'ajabi da ban mamaki
Kasance kai tsaye da mabiyanka (Live videos).
Yi scheduling na posting: 3 zuwa 5 posts a rana.
Aiwatar da trending ideas ya hanyar amfani da hashtags.
Best Formats:
Storytelling videos
Challenge Reels
Tips da Educational Videos
Funny skits
6: Sirrin Nasara a Facebook Monetization;
Focus akan original content.
Gane Audience: Wa kake wa aiki? Me suke so?
Posting consistency: ko da kuwa ba a samu likes da yawa a farko.
Amfani da Analytics: Fahimtar wane content ke jan hankali.
7: Sabbin Canje-Canje a Facebook Monetization (2025 Update)
Canje-canjen Da Kayi La’akari Da Su:
Yanzu an fi karkata akan short videos (Reels).
Facebook na amfani da AI sosai wajen tantance content (copyright da originality).
Professional Mode sun samu damar yin monetisation
Yanzu ana buƙatar more real engagement ba kawai views ba.
Samun kuɗi daga Facebook ba kawai ƙirƙirar content ba ne — sai an bi matakai da dabara, tare da dagewa da bin dokoki. Da zarar ka fahimci abubuwan da muka tattauna a wannan muƙala, zaka iya gina monetisation mai ƙarfi a duniyar content na zamani domin cimma buri.
Ayi aiki tukuru kuma a Jajir ce!
✍️ Hegi Tech Rumbuki
Telegram Channel 👇
https://t.me/Hegitechrumbuki
WhatsApp 09077187787