Hausa media

Hausa media Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hausa media, Media/News Company, Sokoto.

JAKADUN MUSULUNCI SUN GANA DA SHUGANA BUHARIBabban Sakataren kungiyar IZALA na duniya Ash-sheikh Dr Muhammad Kabir Harun...
18/12/2020

JAKADUN MUSULUNCI SUN GANA DA SHUGANA BUHARI

Babban Sakataren kungiyar IZALA na duniya Ash-sheikh Dr Muhammad Kabir Haruna Gombe (H) ya gabatar da zazzafar khuduba yau a jihar Katsina, yace:

"Dazun nan mun shiga gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, an bude mun shiga, mun gaya masa gaskiyar abinda ke faruwa, mun ja ayoyi da Hadisai mun gaya masa tsayuwar sa a gaban Ubangiji, Ya Allah kai ne shaida, Ya Allah kai ne shaida mun isar masa, Ya Allah Ka na sama kana kallon mu mun isar, mun sauke nauyin dake kan mu.."~Sheikh Kabiru Gombe, cikin jawabin sa na Juma'a, dazu a Katsina.

Masu zagin Malaman Sunnah akan halin da kasa take ciki sai kuji tsoron Allah ku dena, Malamai sun sauke nauyin da Allah Ya daura musu

Allah Ka kare mana Malamanmu, Allah Ka bawa shugaban Kasa Buhari ikon karban shawaransu na alheri Amin

J A N    H A N K A L I    T A R E    D A    N A S I H A      Z U W A   G A    D U K’K A N I N    A L’ U M M A R     I S ...
03/11/2020

J A N H A N K A L I T A R E D A N A S I H A Z U W A G A D U K’K A N I N A L’ U M M A R I S L A M A.

Yin barna ko yadata ko wacce iri ce bana goyon bayanta.

Lallai shigar tsiraici ga mace musulma, sharri ne mummuna mai girma gareta, da kuma Al’ummar da take cikinsu. Kuma shigar zubar da mutuncin family din ta ne.

Rashin Magana akan wannan yana daidai da kace a cigaba da aikatawa. Ita kuma Uqubar Allah in ta tashi zuwa zata shafi kowa da kowa’ne. Badoline sai kasan menene mafarinta’ba.

Allah yakara shiryardamu.

Nasiha da jan hankali ba da tozarci ba.
Itace hanya mafi kyau da tadace musulmi yayiwa dan uwansa musulmi Nasiha, akan wata barna da yake aikatawa.

Ita dai Dabi’ar shigar banza nema take ta zama ruwan dare, konace tazama ruwan’daren ga Al’ummarmu.

Abu ne da yake faruwa a rayuwar Yau da kullum, mu duba gidajen biki, Gidan suna, tarurruka, makarantu, tun daga primary zakaga wasu yara mata na tafiya kansu babu DANKWALI sai gashin kansu a daure, ballantana aje secondary ko Universities, kuma dukkan wadan’nan abubuwa suna faruwane a gaban.👇🏻👇🏻👇🏻

IYAYE, MALAMAI, YAYYE, KAWUNNAI, DA KUMA SHUWAGABAN’NINMU.

MACCE TANADA DARAJA. A Gyaruwarta kuma a gyaruwar Al’ummarmu, mu tashi tsaye akan fahimtar’dasu, kunyarsu da mutuncinsu. Domin gyaran ‘Yayanmu masu zuwa anan gaba.

RASULILLAH ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

Yace”👇🏻👇🏻👇🏻

Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowannenku za a tambayeshi game da abin da aka bashi kiyo, a ranar gobe al’qiyama.

Kofar tuba a bude take ga dukkan wanda yayi kuskure, yayi gaggawar Istighfari yafi Jinkirin yinsa.

Dukkanin’mu masu aikata laifuka ne, Allah ne yake rufamuna asirin. Ya Allah kakara karemu ka’kare mutuncinmu. Duniya da lahira Ameen ya rabbi 👏🏻👏🏻👏🏻

A cigaba da addu’ar neman yafiyar Allah, tareda gafararsa. Ina fatan Allah yakara rufamuna asiri, duniya da lahira Ameen ya hayyu ya qayyimu.🤲🏻

DAGA KARSHE.

Ga Hadisin Annabin tsira (S.A.W) akan masu FIDDA TSIRAICI👇🏻👇🏻👇🏻

Yace;👇🏻👇🏻👇🏻

"A karshen zamani za’a samu wasu mata ga tufafi a jikinsu amma tsirara suke, tufafinsu bai rufe tsiraicin suba."

RASULULLAH (S A W)Yace;👇🏻👇🏻👇🏻

“A TSINE musu, domin su din TSINANNUNE."

RASULULLAH (S A W) Yakara da cewa;👇🏻👇🏻👇🏻

Wallhi ko Kamshin ALJANNA baza su ji ba.”😢😫

Ina addu’ar;” Ubangiji Allah yakara fahimtardamu yakara shiryardamu, tareda zuriarmu da dukkan al’ummar musulmi baki daya. Allahumma Ameen ya Allah.🤲🏻🤲🏻🤲🏻

Wajibine Mazanmu da Matanmu mu tashi mu yaki Shaidan La’anannen Allah, Yadda baibar Uban Talikai Annabi Adamu ba, haka muma bazai bar mu ba. Yakinsa kullum shine yasa mu kaucewa hanyar Allah mubi tasa batacciyar hanya marar bullewa.

Allah ya shiryemu baki daya ya tsare mu biyewa son zuciyarmu.

Ameen ya Allah 👏🏻👏🏻👏🏻

Wassiyar Marigayi Saddam Hussaini Ga Musulman Duniya Kafin A Rataye shi.Daga: Naseer Afakallah.Da Sunan Allah mai Rahama...
03/11/2020

Wassiyar Marigayi Saddam Hussaini Ga Musulman Duniya Kafin A Rataye shi.

Daga: Naseer Afakallah.

Da Sunan Allah mai Rahama mai jinkai dukkan Yabo ya tabbata ga cik**akin Manzanni Annabi Muhammad tsira da aminci Allah su Tabbata a gare shi da Ahlinsa.

Allah ne Shaidana a Tsawon Rayuwata nayi Gwagwarmaya da Makiyan Islama Domin Tabbatar da Tsaro a kasar Iraki.

Da yawa daga cikin ku Sun butulce min inda a yanzu suke Murnan Mutuwa ta.

Amman lokaci Zaizo da zakuyi Nadamar reshina, Kukuma Shugabannin Kasashen Musulmai kun bada ni a hadaya ga azzalumai kasashen Yamma wadan da ke cigaba da kashe dumban Musulmai Domin Tabbatar Manufarsu da Mallakar wannan Duniya.

To kusani cewa ko ba Dade, ko ba jima Zaku Zama Ababen farauta ga Wadanda kuka Marawa baya a Yau wasu daga cikin ku na kokarin kawo mun Tallafi Amma sun daina. Domin na Mika Rayuwata Ga Ubangijin na Sai kuyi kokari Ceto naku Rayukan da kuma hana Rabuwar kasar Iraki.

Yaku yan Uwa Musulmai na Duniya ku Gaggauta hada kawunanku ko kuma ku Zama Tamkar Kwallo a Hannayen Amurika da Kawayenta Allahu akbar! Allahu akbar! Babu wani abin Bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu Manzonsa ne.

Allahu akbar, Ya Allah kajikan Saddam Hussaini

A KAN YUNKURIN HANA RUNDUNAR TSARO  MAI YAKI DA 'YAN FASHI DA MAKAMI: SANATA WAMAKKO YA YABAWA MATASAN AREWA KAN KIN SHI...
24/10/2020

A KAN YUNKURIN HANA RUNDUNAR TSARO MAI YAKI DA 'YAN FASHI DA MAKAMI: SANATA WAMAKKO YA YABAWA MATASAN AREWA KAN KIN SHIGA ZANGA-ZANGAR DA AKA YI.

Shugaban Kwamitin tsaro kana mataiamakin Shugaban Kwamitin kula da hukumomin Hana cin hanci da rashawa na Majalisar dattawa ta Kasa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto, ya jinjinawa Matasan Arewacin Nijeriya Kan kin shiga zanga-zangar da ta barke a kan neman kawo karshen Rundunar tsaro Mai yaki da Yan fashi da makami, wadda aka gudanar a kudancin kasar nan.

Wamakko, Mai wakiltar Gundumar Sokoto ta Arewa, ya yi wannan yabon ne a Gidan sa dake Unguwar Gawon Nama Sokoto a ranar Alhamis da ta gabata bayan da yake magantawa Jim kadan bayan ya dawo ziyarar aiki a Abuja.

Sanata Wamakko ya Kara da cewa, " Na ji Dadi sosai Kan ladabi da Zama lafiya da Matasan Arewa s**a nuna duk da irin kalaman tunzura da bacin rai da masu zanga-zangar s**a yi ta yi abin da ya koma fadace-fadace da Kuma kaucewa silar alkiblar zanga-zangar".

Dan Majalisar dattawan ya yi mamakin dalilin lalata Kaya da masu zanga-zangar s**a yi duk da yake Gwamnatin Tarayya ta karbi bukatun su.

Sanata Wamakko ya ce: "Daya daga cikin bukatun masu zanga-zangar ita ce, a janye Rundunar tsaro ta SARS ba tare da Bata lokaci ba.

Ya Kara da cewa, " Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gayawa Matasan cewa, suna da niya Mai kyau a lokacin da s**a Fara zanga-zangar, amma kawai sai aka gurbata musu niyar su".

Sanata Wamakko ya bayyana Matasan da cewa Matasa ne masu kyakkyawar fata a kasar nan, saboda Haka Kada su Bari wasu marasa kishi su Bata musu manufar su Mai kyau.

Ya nanata kudurin Majalisar dattawar kasar nan Kan ganin ta tabbatar da Matasan kasar nan sun cimma gurin su nan gaba.

Rubutawa: Bashir Rabe Mani Dan Masanin Mani mataimaki na Musamman ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto Kan sha'anin Watsa labarai da hulda da Jama'a.

Fassara: Bashar Abubakar MC Sarkin Hausawan Sarkin Yamman Sokoto.
Jumu'a: 23/10/2020

Yadda uwa 'ta yi wa 'ya'yanta yankan rago saboda an mata kishiya a Kano'Rundunar 'yan sandan jihar Kano a arewacin Najer...
04/10/2020

Yadda uwa 'ta yi wa 'ya'yanta yankan rago saboda an mata kishiya a Kano'

Rundunar 'yan sandan jihar Kano a arewacin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar wasu yara biyu da ake zargin mahaifiyarsu ta yi musu yankan rago.

'Yan sandan sun ce ana zargin cewa matar ta sami sabani da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watanin baya.

Wannan lamari ya faru ne a unguwar Sagagi Layin 'Yan Rariya da ke kwaryar birnin Kanon.

Yaran da ake zargin mahaifiyar tasu ta yanka su ne Yusuf Ibrahim mai shekaru biyar da yar uwarsa Zahra'u Ibrahim mai shekaru uku kuma sun gamu da ajalin nasu ne a jiya Asabar.

Lamarin ya daurewa mutane da dama a unguwar ta Sagagi da ma fadin jihar Kano kai, musamman ga makotan gidan da lamarin ya faru inda suke cewa a iya sanin da s**a yi wa matar bata da tabin hankali haka kuma ba a santa da shaye-shaye ba.

Amma sai dai wasu, sun kuma alakanta abin da matar ta yi da kishiyar da mjin ta ya yi mata a 'yan kwanakin baya, wanda har ta kai ga sun samu rashin jituwar da ya janyo mutuwar aure, amma daga baya aka dai-dai ta ta koma dakinta.

Ana neman matar
BBC ta yi kokarin jin ta bakin mahaifin yaran da aka kashe ma'ana mijin matar da ake zargi da kashe 'ya'yan natan, amma bai iya magana ba saboda yanayi na juyayi da alhali ni da ya ke ciki sak**akon abin da ya faru.

Wani lamarin da yake kara daure kai a cikin batun shi ne rashin sanin inda matar take da kuma halin da take ciki, domin a cewar kakakin rudunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Kiyawa abin da s**a sa gaba yanzu shi ne neman inda matar take, domin tuni s**a kaddamar da bincike.

Tuni dai aka yi wa yaran jana'iza a dai-dai lokacin da ake ci gaba da neman mahaifiyarsu da ake zargin ita ta raba su da duniya, bayan ta sha wahalar daukar cikinsu da rainonsu har s**a fara zama mutane.

Lamarin dai ya dauki hankulan jama'a da dama musamman ganin irin shakuwar da ke tsakanin da da mahaifi, abin da wasu ke ganin ruwa ba ya tsami banza, kuma dalilin kishi ba zai sa uwa ta hallaka 'ya'yanta ba, don haka mutane ke fatan samun takamemen amsa duk lokacin da aka samu matar da ake zargi aka kuma gudanar da bincike.

Wamakko na cigaba da raba Na'urorin Raba wutar Lantar ki (Transformers) a unguwanin Jahar sakkwato.A Yau ma Sanata Dr, A...
02/10/2020

Wamakko na cigaba da raba Na'urorin Raba wutar Lantar ki (Transformers) a unguwanin Jahar sakkwato.

A Yau ma Sanata Dr, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bada tallafin sabuwar Na'urar Raba wutar Lantarki (Transformer) a Unguwar Kofar Kware da ke sokoto.

Dan Majalisar dattawa Mai wakiltar Gundumar Sokoto ta Arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto, ya sake bayar da wata na'urar wutar lantarki ga Jama'ar unguwar kofar Kware dake yankin mulkin Sokoto ta Arewa.

Na'urar Mai karfin doki dari biyar, an bayar da ita ne ga wadannan Jama'ar sak**akon koken da s**a Kaiwa Sanata Wamakko na neman sabuwar na'urar saboda wadda suke amfani da ita ta lalace watannin bayar.

Da Yake magantawa Jim kadan bayan bayar da na'urar, wakilin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Shugaban Ma'aikatan Ofishin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Dr. Abdullahi Ahmad Gada, ya bayyana cewa, wannan na'urar za ta Samar da hasken lantarki ga shiyoyin da s**a kunshi; Kofar Kware, Rumbukawa, Adarawa, Jibdawa da sauran shiyoyin dake kusa da su.

Wani da aka zanta da shi, Alh. Abubakar Yaro, Wanda Yake mazauni Unguwar ne, ya yi bayanin cewa, sun Sha kashe kudade wajen kokarin Gyara waccen tsohuwar na'urar, Amma dai abin ya faskara.

Daga nan, sai ya nuna jindadin su Kan wannan karimcin na Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kana ya yi Kira ga masu abin Hannun su da su yi koyi da wannan halin na taimakawa Jama'a d Sanata ke yi.

Haha Kuma Jama'a da dama dake wannan yankin sun yi ta tsalle da murna a lokacin da aka iso da wannan na'urar.

Idan dai za a iya tunawa, Makon da ya gabata ne Al'ummar wannan yankin s**a turo wani ayari karkashin jagorancin Alh Musa Kangiye Turakin Gwadabawa zuwa a Gidan Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko domin rokon wannan na'urar, kuma take yanke Sanata ya umurce da a sawo sabuwar na'urar domin sakawa a wannan shiyar.

Dai-dai wannan lokacin da ake rubutun wanan labarin, Jami'an Kamfanin Samar da wutar lantarki na can na kokarin saka wannan na'urar.

Wata mai k**a da wannan kuma, shi ne duk wani abinda al'umma suke anfani dashi ya lalace ko ake bukatar sa don amfanin al'umma babu Inda za'a sameshi a jahar sakkwato sai gidan Sanata Wamakko.

Munafatan Allah yasak**a da mafificin alkairinsa yakarabashi ikon cigaba da taimakawa al’ummarsa.Ameen 👏🏻👏🏻👏🏻

SANATA WAMAKKO YA SAKE BAYAR DA TALLAFIN NA'URAR WUTAR LANTARKI A SHIYAR RUNJIN SAMBO DAKE SAKKWATO:Al'ummar Yankin Mulk...
27/09/2020

SANATA WAMAKKO YA SAKE BAYAR DA TALLAFIN NA'URAR WUTAR LANTARKI A SHIYAR RUNJIN SAMBO DAKE SAKKWATO:

Al'ummar Yankin Mulkin Sokoto ta Arewa Musamman shiyoyin Runjin Sambo, Gidan Kuka, shiyar Fulani, Gidan Dare, Gidan Igwai, da kuma Titin Kangiwa sun Dade suna fama da matsalar hasken wutar lantarki saboda kasawar na'urar da ke bayar da hasken wutar a wadannan shiyoyin.

Kamar yadda Mai Magana da yawun Jama'ar wadannan unguwannin Kuma Wanda ya jagoranci neman wannan na'urar Alh. Sani Mai Eka Tambagarka ya fada, suna kashe a kalla naira dubu Goma kowane lokaci domin ganin sun gyara tsohuwar na'urar su.

Ya bayyana cewa, na'urar ta tsufa Kuma karfin wutar da take bayarwa ya yi kadan domin na'urar karfin doki dari uku ce.

Alh. Sani ya bayyana cewa sun kawo koken neman wannan na'urar ne ga Sanata Mai wakiltar Gundumar Sokoto ta Arewa maigirma sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto, Kuma cikin ikon Allah , Mai girma Sanata ya saurari bukatun su Kuma ya shafe musu hawayen nan take inda ya umurci da a saka musu na'urar wutar lantarki Mai karfin doki dari biyar domin magance wannan matsalar kowa ya huta.

A yau Assabar ne, alkawarin ya cika domin kuwa tuni Jami'an Kamfanin Samar da hasken wutar lantarki a karkashin jagorancin Darektan lamurran Mulki na Ofishin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Alh Almustapha Abubakar Alkali s**a Kai wannan na'urar.

Almustapha Alkali ya Kara bayanin cewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, a koda yaushe yana sauraren bukatar Jama'ar sa saboda Haka Bai yi Kasa a Gwiwa ba ya bada umurnin saka wannan na'urar sabuwa hul.

Jama'ar wadannan unguwannin, a karkashin jagorancin Alh Sani Mai Eka Tambagarka, sun godewa Mai girma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Kan wannan karimcin, abin da s**a bayyana fa cewa ba za su manta da wannan kokarin ba.

Alh. Mai Eka, ya ci gaba da cewa, Basu da wadatattun kalaman da za su yi amfani da su Domin godewa Mai girma Sanata, Sai dai su ce, Allah ya ci gaba da yi Mai jagora ga dukkan lamurran sa.

Ya bada tabbacin cewa, za su kula da wannan na'urar domin Hana a lalata ta ko Kuma a yi Mata lodin da ba za ta iya dauka ba.

Jama'ar wadannan unguwannin dai sun fito suna murna da Godiya da s**a ga isowar wannan na'urar.

Idan dai ba a manta ba, a shekaranjiya Alhamis Mai girma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayar da irin wannan na'urar a wadansu unguwannin tsakiyar Birnin Sakkwato inda suke fama da matsalar Zama cikin duhu da sauro.

Labari: Bashar Abubakar MC Sarkin Hausawan Sarkin Yamman Sokoto.

Assabar: 26/9/2020

KUSKUREN DA YA KAMATA SHUGABANNI DA 'YAN BOKO MUSULMAI SU GYARADaga Datti Assalafiy Jiya Maigirma gwamnan jihar Kaduna M...
25/09/2020

KUSKUREN DA YA KAMATA SHUGABANNI DA 'YAN BOKO MUSULMAI SU GYARA

Daga Datti Assalafiy

Jiya Maigirma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya fitar sa sanarwa a shafinsa na Facebook cewa yana karanta wannan Littafin wanda wani bature ya rubuta a kan tsarin gudanarwan gwamnatin kasar Kaduna daga shekarar 1800 zuwa 1950 Miladiyyah

Gwamnan yace yana duba Littafin ne domin ya taimaka masa wajen zaben sabon Sarkin Zazzau

Jama'a wannan babban kuskure ne da aka jima ana yinsa a Nigeria tsakanin mutanen da suke kiran kansu Musulmai, saboda abinda sukeyi bisa ga takaituwa da dogaro akan abinda turawa s**a rubuta na tarihi ko bincike akan Musulunci da jihadi

Mafi girman kuskure da gwamnan jihar Kaduna zaiyi wajen neman madogara akan tarihin Daula da Sarakunan Kasar Zazzau gabannin shigowar turawan Mulkin Mallaka shine takaituwa zuwa ga abinda yake kunshe a cikin wannan Littafin da bature ya rubuta

Da jimawa na karanta wani yanki na wannan Littafin, akwai gurin da baturen ya bada tarihin yadda mayaka mujahidai na Shehu Usman Dan Fodio kabilar Fulani s**a shigo Kasar Zazzau da yaki, s**a yaki Sarkin Zazzau wanda yake Musulmi, wai basu farmasa ba sai a daidai lokacin da ya fita sallar karamar idi, daga nan ne s**a fara sarautar Fulani

Wannan Littafin da Malam Nasir yake karantawa akwai karya da kura-kurai masu tarin yawa a cikinsa, Shehu Usman bai yaki Musulmai ba, bidi'ar da yazo ya tarar Musulmai nayi ya yaka da hujja na ilmi ba makami ba, amma ya yaki maguzawa da kafurai da s**a farmasa, wanda wannan shine jihadin Musulunci

Jihadin Shehu Usman turawa sun lalata tarihinsa, yadda turawa s**a rubuta tarihinsa zaku ga bai da maraba da jahadin Abubakar Shekau na Boko Haram, haka yahudawa da nasara suke wajen kokarin lalata tarihin mutanen kirki har da Annabawan Allah

Hatta tarihin Manzon tsira Annabi Muhammad (SAW) sai da s**a lalata, sun rubuta tarihinsa cewa makami ya dauka yayi kisa ya tilasta mutane shiga addinin Musulunci, har suna cewa Musulunci addini ne da aka ginashi da kaifin tokobi da zubar da jini

Idan kuna karanta Bible, ku duba surar Karin-Magana (Proverb), zaku ga yadda s**a bada tarihin rayuwar Annabi Sulaiman, sun bata tarihinsa, sun bayyanashi a matsayin wani shahararren mutumin banza fasiki mashayi kartagin mazinaci, babu dadin karantawa, to haka turawa suke basu bar Annabawan Allah ba wajen bata tarihi

Kuskure ne babba muna yadda da tarihin da turawa da yahudawa suke rubutawa akan rayuwar Musulmai da kuma Musulunci

Maigirma gwamna Malam Nasir El-Rufai ka duba Qur'ani, Hadisi da Ijma'in Malamai sun isheka madoga wajen zaben Sarki, wanda ba zakayi zaben tumun dare ba Insha Allah

Allah Ya bamu ikon gyarawa Amin

WATA SABUWA: Ango ya bawa amaryarsa kyautar wani fili da ya siya a duniyar wataDAGA Comr Bashir Suleiman Bash..." Wani m...
25/09/2020

WATA SABUWA: Ango ya bawa amaryarsa kyautar wani fili da ya siya a duniyar wata

DAGA Comr Bashir Suleiman Bash...

" Wani mutum dan kasar Pakistan ya siya wa matarsa fili a duniyar wata a matsayin kyautar aure

- Ya siyawa matar tasa filin ne a wata unguwa mai suna 'Sea of Vapour' a can duniyar wata

- Mutane da dama basu yarda ba, sai da s**aga takardun filin a hannunsa

Sohaib Ahmed mazaunin Rawalpindi ya siyawa matarsa fili a wata unguwa mai suna 'Sea of Vapour' a duniyar wata akan kudi dalar amurka arba'in da biyar ($45) a hannun hukumar duniya ta filayen duniyar wata.
Bayan Sushant Singh Rajput, jarumin fim din Indiya ya siyi filin a duniyar wata, shima dan Pakistan din yace baza'a barshi a baya ba, hakan ya sanya ya siyawa matar tasa a matsayin kyautar aure.

Mutumin ya siyawa matar tashi filin mai girman filoti guda daya ne.

Kamar yadda rahotanni s**a riskemu, Sohaib Ahmed, mai shekaru 23 da haihuwa, mazaunin Rawalpindi ya siya wa matar tasa filin, kuma takardun filin yanzu haka suna nan a hannunsa.

A wata hira da SAMAA TV s**ayi da Ahmed, yace ganin Sushant Singh Rajput ya siya filin yasa ya samu kwarin gwuiwar siya shima.

Madiha, matar Ahmed ta bayar da labarin yadda kawayenta s**aki yarda lokacin da ta sanar dasu mijinta yayi mata wannan kyauta ta musamman.

Bayaga Sushant, sanannun mutane k**ar irin su Tom Cruise, Shah RukhKhan, John Travolta, Nicole Kidman suma duk suna da filaye a duniyar wata.

"A lokacin da na fada wa mutane, kowa yasha wasa nikeyi sai da s**a ga takarddun filin, mamaki ya k**asu," a cewar Madiha a lokacin da take hira da Samaa TV.

Yadda Aka Fasa Auren Budurwa  Saboda Yad'a Bidiyon TsiraicintaDaga Indabawa Aliyu ImamHukumar Hisbah a jihar Sakkwato da...
24/09/2020

Yadda Aka Fasa Auren Budurwa Saboda Yad'a Bidiyon Tsiraicinta

Daga Indabawa Aliyu Imam

Hukumar Hisbah a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da k**a wasu matasa su uku bisa zarginsu da yaɗa bidiyon wata yarinya da ɗaya daga cikinsu ya yi lalata da ita k**ar yadda jaridar BBC ta rawaito.

Bayanai sun nuna an saka ranar auren yarinyar a watan gobe, amma sai wanda zai aure ta ya janye bayan da waɗannan matasan da ake zargi s**a saki bidiyon a shafukan sadarwa.

Kwamandan hukumar Hisbah Dr. Adamu Bello Asarawa ya shaida wa BBC cewa mahaifiyar yarinyar ce ta kai musu ƙorafi inda ta ce tun a shekarar 2017 matasan s**a lalata yarinyar tare da ɗaukar bidiyon.

Dr. Adamu ya ce ''Matashin ya yaudari yarinyar ne ya kai ta otel kuma ya ɗauki bidiyon tsiraicinta. Sai bayan da ta samu miji za ta yi aure sai kawai aka ga ya saki bidiyon.

''Mun binciki yaron ya kuma tabbatar mana cewa abin ya faru, zuwansu otel da abin da ya yi da ita, sannnan mun kamo abokansa biyu da ya turawa kuma su ma sun yi ikirarin cewa shi ya tura musu.

''Don haka duk wanda ya samu bidiyon daga baya to ta hanyar abokan nan biyu ya samu,'' a cewar kwamandan.

Me ya sa yaron ya ɗauki bidiyon?

Kwamandan hukumar Hisbah ya ce yaron bai bayar da wasu dalilai da s**a sa ya ɗauki bidiyon tare ya yaɗawa ba.

''Ɓarna dai ta riga ta faru. Rashin tarbiyya ce irin ta yara. Ina ga ya yi hakan ne don cin zarafi da lalata mata rayuwa da kuma suna,'' in ji Dr Adamu.

Kwamandan ya ce sun tambayi yaron ko zai auri matashiyar ne tun da yanzu ya lalata maganar aurenta, ''sai ya ce min ba shi da niyyar hakan, ai ba zai iya aurenta ba don dama da niyyar yaudara ya je,'' in ji shi.

Shekarun yaron 17 ita kuma yarinyar tana da 16 a lokacin da lamarin ya faru. A yanzu kuma yaron na da shekara 20 ita kuma 19 a cewar shugaban Hisbar.

''Dukkansu yara ne lokacin da abin ya faru don ba wanda ya kai 20."

Me iyayen yarinyar s**a ce?

A cewar mahaifiyar yarinyar wadda yanzu aka ce shekarunta kimanin 20, wanda ake zargin ya yi lalata da 'yar tata ne tun a shekara ta 2017 kuma ya nadi masha'ar ta wayar salula.

Ta ce ya ajiye bidiyon tsawon shekaru uku da nufin wata rana ya yi amfani da shi wajen ɓata sunanta idan yau da gobe ta yi halinta s**a ɓaɓe.

''Ni dai a cikin watan Yuni ina zaune yayata ta kira ni daga Legas tana ta salati ta ce ga wance nan ta ganta a bidiyo tsirara ana ta yaɗawa. Sai na kira ƴar tawa na tamabaye ta, sai ta ce min ita ma yanzu take jin labari wajen wata ƴar makarantarsu.

''Sai na ce wa take zargi? Sai ta gaya min sunan yaron. Na ce ta ba ni nambarsa. Daga nan na je har gidan iyayensa, na tambayi yaron me ƴata ta yi masa a rayuwa da ya zaɓi yi mata wannan cin mutuncin?

''Sai ya ce ba abin da ta yi masa. Ga yarinya a bidiyon k**ar wacce ta sha wani abu ta bugu. Duk wanda ya san tarbiyyar da na yi wa ƴata dole ya taya ni kuka wallahi.

''Daga nan sai mahaifiyar yaron ta kira babansa, ta ce ka zo ka ga abin da ɗanka ya aikata. Daga nan uban ya neme shi da ya nuna mana, sai kuwa yaron ya buɗe bidiyon muka gani.''

Uwar yarinyar ta ce bayan haka ne uban yaron ya nemi da a taru a rufawa juna asiri, ''don a ganinsa hakan ba wani abu ba ne,'' k**ar yadda uwar ta ce.

''Sai ya ce min ai da a ce ciki ne da sai a shiga tashin hankali. Ni ko na ce wannan ma tashin hankali ne. Sai kawai ya ce na je dai kawai.

''Ni ko daga can sai na tafi Hisbah na kai ƙararsu. Da yanzu bikin ƴata 17 ga watan Oktoba ne, amma yaron ya ce ya fasa auren don shi s**a fara aika wa bidiyon.''

Haka kuwa aka yi in ji rahotanni, bayan yarinya ta yanke shawarar yin aure da wani ba shi ba sai ya saki bidiyon a shafukan sada zumunta abin da ya sa wanda za ta auran ya ce ba da shi ba.

Wane hali yarinyar ke ciki?

Mahaifiyar wannan yarinya dai ta ce a yanzu haka yarinyar na cikin tsananin damuwa ta yadda ko abinci ba ta ci. ''Ba ta da aiki sai kuka dare da rana.

''A yanzu haka dole mu nemi inda za mu kai ta don ta samu kwanciyar hankali,'' a cewar uwar.

Mahaifiyar yarinyar ta ce babban burinta shi ne a bi mata hakkin cin zarafin da aka yi wa ƴarta.

Wane hukunci za a yi wa yaron da abokansa?

Kwamandan Hisbah ya ce za a kai maganar gaban hukumar NAPTIP don ta duba ta ga dokokin da aka tanada kan ɓangaren abin da ya shafi ikirari na saduwa ga masu ƙananan shekaru.

''Su ne ke da hakkin hakan. Sai kuma mu kai hukumar tace bidiyo da fina-finai wato Censor Board don su ma su yi nasu aikin.

''Idan sun yi abin da ya dace daga nan kuma sai akai maganar kotu. Kuma abin da ya sa za a haɗa da abokan biyu saboda su nasu laifin shi ne na yaɗa batsar da baɗalar,'' a cewar Dr Adamu.

Wannan labari ka iya zama darasi da kalubale ga matan da ke yarda ayi lalata da su, ko masu tura hotunan tsiraici, zai zama kalubale ga iyaye wajen saka ido da kula da tarbiyyar yaransu yadda ya dace.

LABARI DA DUMI DUMI Innalillahi wa'inna ilaihirraj'unAllah Ya Yiwa Mai Martaba Sarkin Zazzau Hrh Alhaji Shehu Idris Rasu...
20/09/2020

LABARI DA DUMI DUMI

Innalillahi wa'inna ilaihirraj'un

Allah Ya Yiwa Mai Martaba Sarkin Zazzau Hrh Alhaji Shehu Idris Rasuwa Yanzun Nan

Muna Adduar Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa.

Address

Sokoto

Telephone

+2348030652560

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa media:

Share