24/07/2025
Wata kotu a Ilorin, Jihar Kwara, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abimbola Awogboro, ta yanke wa wani matashi mai shekaru 20, Mathew Yaba, hukuncin zaman gidan yari na watanni tara ba tare da zaɓin biyan tara ba, bayan ta same shi da laifin zamba ta yanar gizo da boye kudaden da ya samu daga ayyukan haramtattu.
Yaba ya amsa cewa ya karɓi Naira miliyan 7.38 ta asusun Kuda Bank da kuma amfani da sunan wani Raleigh Jredd domin yaudarar mutane.
A cewar Dele Oyewale, Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na Hukumar EFCC, Mathew Yaba na daga cikin mutane 11 da hukumar ta EFCC ta samu da laifi a Ilorin, a wani samame da Sashen Ilorin na hukumar ya kaddamar domin dakile ayyukan zamba da damfara ta intanet. Sauran wadanda aka yankewa hukunci sun hada da Samuel Ayomide, Bamidele Olajide, Isah Kadir, Jubril Abdulrasaq, Peter Juwon, Stephen Benefit, Kayode Opeyemi, Lasisi Abdulrahim, Michael Ikechukwu, da Abduljawad Moshood. Hukuncin ya haɗa da zaman kurkuku daga wata shida zuwa shekara guda, wasu kuma an yanke musu aikata aikin sa-kai (community service), tare da umarnin kwace dukiyoyin da s**a samu ta haram.
Mai Shari’a Awogboro da Mai Shari’a Mahmud Abdulgafar, wanda ya jagoranci shari’ar guda, sun tabbatar da hukuncin ne bayan waɗanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi, kuma an gabatar da shaidun da s**a haɗa da takardun amsa laifi, wayoyi, kwamfutoci, da kudaden fansa. Yaba, musamman, ya rasa iPhone 13 dinsa da kuma Naira 200,000 da ya dawo da su a matsayin fansa ga Gwamnatin Tarayya. Hukumar EFCC ta bayyana cewa wannan nasara wata babbar alama ce ta ƙoƙarin tabbatar da tsafta a sararin intanet da kuma hana matasa fadawa tarkon damfara.