25/08/2026
YADDA AKA GUDANAR DA MUZAHARAR MAULUDI A BABBAN BIRNIN TARAYYAR NAJERIYA ABUJA
- Daga Bilyaminu Ɗan Jarida
Da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Talata, 25 ga Agusta, 2026, wanda ya yi daidai da 12 ga Rabi’ul Awwal, 1448H, al’ummar Musulmi s**a gudanar da gagarumar Muzaharar Maulidin Manzon Allah (S) a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, domin nuna farin ciki da murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S).
Muzaharar ta samu halartar ɗimbin al’ummar Musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (h) da Mabiya Dariku daga sassa daban-daban na Abuja da kewaye, inda mahalarta s**a fito cikin yanayi na farin ciki da annashuwa, suna ɗauke da tutoci da alluna masu ɗauke da saƙonnin girmamawa da ƙauna ga Manzon Allah (S).
An fara Muzaharar ne daga Mabushi Junction, Abuja, inda mahalarta s**a taru kafin fara tafiyar. Daga nan ne muzaharar ta ɗauki hanyar da aka tsara, tare da mahalarta suna tafiya cikin tsari da haɗin kai, suna bayyana ƙaunarsu ga Annabi Muhammad (S) da kuma jaddada muhimmancin koyarwarsa ga al’ummar Musulmi.
A yayin muzaharar, an rika gudanar da kiraye-kirayen yabo da girmama Manzon Allah (S), tare da ɗaga taken “Labbaika Ya Rasulallah”, wanda ke nuna amsa da biyayya ga kiran Manzon Allah (S). Mahalarta sun kuma bayyana farin cikinsu da wannan rana mai girma ta Mauludi.
Muzaharar ta kasance wata dama da al’ummar Musulmi s**a yi amfani da ita wajen tunawa da rayuwar Manzon Allah (S), koyarwarsa, halayensa na gari da kuma irin muhimmiyar rawar da ya taka wajen isar da saƙon Musulunci ga al’umma.
Haka kuma, taron ya kasance na haɗa kan al’ummar Musulmi Shi'a da Sunnah, inda maza da mata da Matasa, kabilu ma banbanta s**a fito domin gudanar da bukin Mauludi cikin kwanciyar hankali da lumana.
Bayan shafe sa’o’i ana gudanar da muzaharar a cikin babban birnin tarayya, an kawo ƙarshenta ne da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin yau, a Tsohon Filin Fareti na Ƙasa da ke Abuja, inda mahalarta s**a kammala Muzaharar cikin tsari.
An gudanar da muzaharar ne a daidai lokacin da Musulmi a sassa daban-daban na duniya ke bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S), tare da nuna ƙauna da girmamawa gare shi da kuma tunatar da al’umma muhimmancin bin koyarwarsa.
Mahalarta sun bayyana farin cikinsu da samun damar gudanar da wannan gagarumar muzahara a babban birnin tarayyar Najeriya, inda s**a yi addu’ar Allah Ya ƙara haɗa kan al’ummar Musulmi, Ya sanya koyarwar Manzon Allah (S) ta zama jagora ga rayuwarsu, Ya kuma dawo da wannan rana cikin aminci da albarka.
- Suleja Media watch
12 Rabi’ul Awwal, 1448H
25 ga Agusta, 2026