Imam Aliyu Ahmad Sambo

Imam Aliyu Ahmad Sambo An ƙirƙirar wannan shafi ne don yada karatuttukan IMAM ALIYU AHMAD SAMBO. Allah yayi Mana jagora.

🌙✨ SANARWAR GAYYATA  ZUWA BUƊE TAFSIRIN ALƘUR’ANI NA RAMADAN ✨🌙Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin ƙai.Markaz-Thaqafaul Is...
16/02/2026

🌙✨ SANARWAR GAYYATA
ZUWA BUƊE TAFSIRIN ALƘUR’ANI NA RAMADAN ✨🌙

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin ƙai.
Markaz-Thaqafaul Islamiyya Toro tare da ɗaliban Malam suna farin cikin gayyatar al’umma baki ɗaya zuwa Buɗe Tafsirin Alƙur’ani Mai Girma na watan Ramadan.
Za a fara tafsirin ne da yardar Allah a yau Litinin bayan Sallar Isha’i, ƙarƙashin jagorancin malaminmu:

IMAM ALIYU AHMAD SAMBO
(NAIBI II CENTRAL MOSQUE FADAN TORO)

Wannan wata dama ce ta musamman domin ƙara kusanci da Alƙur’ani, fahimtar ma’anoninsa, da samun shiriya da falala a wannan wata mai albarka.
Allah Maɗaukaki Ya ce:

"شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدًى لِلنَّاسِ"
“Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ga mutane…” (Al-Baqarah: 185)

Muna kira ga Al'ummah, matasa da manya da su halarta domin amfana da wannan tafsiri mai albarka.

📍 Wuri: Central mosque fadan Toro
🕰 Lokaci: Yau Litinin, bayan Sallar Isha’i

Allah Ya sa mu kasance cikin masu sauraro da aiki da abin da muka ji.

Sanarwa daga:
Markaz-Thaqafaul Islamiyya Toro
🌙 Ramadan Kareem 🌙

Address

Toro

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Imam Aliyu Ahmad Sambo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share