
20/07/2025
Tare Da Jama'a Na, Yau Lahadi Wadda Tayi Daidai Da 20-07-2025 Mun Sami Kai Ziyarar Ta'aziyyar Mu Garin Daura Na Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Marigayi Muhammadu Buhari, Wanda Allah Ya Karbi Rayuwar Sa a Satin Daya Gabata.
Bayan Mun Gabatar Da Ta'aziyyar Mu Ga Iyalai Da Yan Uwan Mamacin, Mun Kuma Wuce Fadar Mai Martaba Sarkin Daura a Inda Shima Muka Gabatar Mashi Da Ta'aziyyar Mu Da Kuma Adu'oi Na Musamman.
Muna Adu'ar Allah Madaukakin Sarki Daya Gafarta Masa, Ya Kuma Baiwa Iyalan Sa Hakurin Wannan Babban Rashi. Amin
Honorable Lawal Samai’la Abdullahi Yakawada
Chairman, North-West Development Commission (NWDC)
#20-07-2025