28/09/2024
■ A Arsenal, ya lashe kyautar mafi kyawun mai tsaron raga a gasar Premier League.
■ A AS Roma, ya ajiye Alisson Becker a benci.
■ A Juventus, Yana ɗaya daga cikin mafi kyawun masu tsaron ragar su, kuma ya ajiye Buffon a benci.
■ A wasansa na ƙarshe a gasar cin kofin duniya, shikaɗaine mai tsaron ragar da Messi bai zurawa ƙwallo ba, inda ya ture Fanaretinsa.
■ Yanzu kuma, wata ɗaya bayan ya bayyana Ritayarsa, ya dawo ƙwallon ƙafa kuma zai buga wasa a ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a duniya, FC Barcelona.
Tabbas rayuwar ƙwallon Wojciech Szczesny ta yi kyau 😍
■ Fagen Wasanni