27/07/2025
A GUDANAR DA MUZAHARAR ASHURA A GARIN DAWAKIN KUDU DA KE KANO.
Bayan shafe tsawon watan Muharram, a ranakun Litinin, Laraba da Alhamis, na wannan shekara ta 1447, ana gabatar da zaman juyayin Waki'ar Ashura, a garin Dawakin kudu dake yankin Kura, da'irar Kano da kewaye, an gabatar da gagarumar muzaharar da ta samu wakilcin dukkan masoya gidan Manzon Allah daga lungu da sako na yankin.
Muzaharar da aka fara ta da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar 1 ga watan Safar 1447 ( 26/07/2025), ta daga ne daga Muhallin makarantar Fudiyya Dawaki.
Daga nan sai mahalarta muzaharar, da s**a kunshi maza da mata, yara da manya, sanye da bakaken kaya, rike da bakaken tutoci, rubuce da kalmar 'labbaika ya Hussain', don bayyanar da juyayin kisan jikan Manzon Allah imamu Hussaini (AS), s**a gangara izuwa hanyar da ta nufi Kofar Arewa ta gaban Dawaki Unity Bank. Sai Unguwar Na'ibawa, izuwa kan kwana da kuma Galadanchi, ta biyo ta gaban gidan Hakimin Dawaki.
Muzaharar ta nausa izuwa Unguwar Maliki, sai Masaka da kuma Kofar kudu. Hakan nan muzaharar ta shiga Unguwar Dabino da kuma Rinji. Sai Unguwar Kuka, izuwa Kofar Gabas, inda ta biyo ta gaban asibitin Dawakin kudu General Hospital.
Misalin karfe shida da rabi, muzaharar ta iso wani katon fili, kafin ka karasa asibitin Sani tiyata (Dawaki Nursing Home), inda aka rufe ta.
A wajen rufe muzaharar, kafin jawabin wakilin yan'uwa na garin Dawaki, Malam Abubakar Takiyyu Dawaki tare da Malam Arma Kura, sun fadakar da yan'uwa akan daukar takalifin iyalan shahidai.
Malam Ibrahim Abdu D/kudu, wakilin yan'uwa almajiran Sayyeed Ibraheem Zakzaky (H) na garin Dawakin kudu, ya fara jawabin rufe muzaharar ne da godewa Allah (T) da ya tsawaita rayuwarmu har muka ga wannan rana ta gabatar da muzaharar Ashura ta Dawakin kudu, bayan share wata guda ana zaman juyayi.
Daga nan sai malamin ya labartawa mahalarta, hakikanin abin da ya faru a ranar Ashura, inda yace, 'babu shakka rundunar makiya Allah, mai dauke da dubban mayaka karkashin jagorancin Yazidu dan Mu'awiyya la'ananne sun zubda jinin jikan Manzon Allah ta hanyar yanke kansa mai albarka, da kuma kisan Iyalansa da Sahabbansa da basu wuce su saba'in da 'yan kai ba. Sannan yace, " Imamu Hussaini da wadanda suke tare dashi sun sadaukar da rayukansu ne domin ceto wannan addini ga barin shafewa daga doron kasa." Ya kara da cewa, "da ace Imamu Hussaini da wadanda ke tare dashi sunyi bai'a ga Yazidu, da wallahi sai dai mu ringa jin labarin anyi wani addini wai sunansa Musulunci", inji malamin.
Daga nan sai ya bayyana cewa duk wanda ke kiran kansa musulmi, wanda yai imani da Manzon Allah (S.A.W.A.), Imamu Hussaini yana da hakki a kansa na kokawa kan zaluncin da aka yiwa gidan Manzon Allah. " Don haka nema, idan irin wannan lokacin yazo, muke gabatar da tarurruka, da zamammaki, da muzaharori domin tunatar da al'umma da kawukanmu, irin abin da ya faru ga gidan Manzon Allah (S.A.W.A.)"
Bugu da kari, Malam Ibrahim Abdu yace, "a filin hamadar Karbala, imamu Hussaini (AS) yayi kira, inda cewa, 'Hal Min Nasirin Yansurna'? ( Shin babu wani mai taimako da zai taimakeni?), yayin da makiya Allah ke yunkurin shahadantar dashi." Don haka sai Malam Ibrahim yace, " ko da ya kasance, mutum ba ya waccen lokacin da Imam yai waccen kiran, ballantana ya amsa masa, to idan a yanzu ya koka akan abin da ya samu Imamu Hussaini na musiba, tamkar ya amsa masa waccen kiran ne.
A karshe ya koka akan mulkin zalunci, da zubda jinin bayin Allah, dake faruwa babu gaira bare dalili, a kasar nan, inda yace, "mafita kawai shine al'umma tayi koyi da sadaukarwa irin wadda Imam Hussaini yayi, domin samun wanzuwar adalci a doron kasa.
Ya karkare da yin kira ga al'umma, dasu taimaki al'ummar kasar Falasdinu, da duk abin da zasu iya, domin tseratar dasu daga danniya, zalunci da keta, wanda kasar Israila da kawayenta ke aiwatarwa a kansu.
Hakan nan, shima ya fadakar da yan'uwa, kan hakkin shahidan harka a kanmu, inda yace, ya zama wajibi yan'uwa su dauki dawainiyar iyalansu da kuma biyan hakkin shuhada'u na tsarin wata wata ko kuma shekara shekara.
Yayin muzaharar an rarraba takardu ga al'ummar garin na Dawakin kudu, wadda ke dauke da hakikanin sakon Ashura.
Misalin karfe 7: 00 na Magariba, Malam Abdullahi Musa ya gabatar da adu'ar kammalawa, aka sallami jama'a.