24/03/2026
Dole ka tsaya da kafafunka kafin ka yi aure
Inji Dr.Alhassan Mai Lafia
Dole ka tsaya da kafafunka kafin ka yi aure, domin aure ba wasa ba ne, ba jin daɗin soyayya kawai bane, ba jima'i kawai bane, aure rayuwa ce gaba ɗaya mai ɗauke da nauyi, hakuri, da alhaki. A yau, akwai matasa da yawa da suke shiga hidimar aure da gaggawa saboda soyayya, matsin lamba daga abokai ko iyaye, ko kuma ganin wasu sun yi aure.
Suna ganin aure kamar wasa ne kawai, ba tare da sun shirya rayuwarsu ba, ba tare da sun tanadi abin da zai rike gida ba. Misali, akwai wani saurayi mai aiki na lokaci-lokaci (part-time) kawai, sai ya yi aure saboda soyayya, ba tare da ya duba yadda zai ciyar da iyali ba, ko shekara biyu ba ayiba matar ta fara amsar wankau daga maqobta saboda rashin kulawa, yaran s**a fara tasowa ba tarbiyya, suna yawo suna yawon gwangwan a t**i, shikenan gida ya rikice da rashin tsari. Wannan shine ainihin illar saurin aure.
Annabi ﷺ ya ce:
يَا مَعْشَرَ الشَّبَابِ، مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمُ الْبَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ (Bukhari da Muslim)
“Ya ku matasa! Duk wanda ya samu iko (ikon aure), to ya yi aure.” Wannan iko da Annabi ﷺ ya ambata ba sha’awa kawai ba ce; a’a yana nufin ikon ɗaukar nauyi, ikon kula da iyali, da ikon tsayuwa da kafafunka kafin aure. Duk wanda ya yi aure ba tare da wannan iko ba zai iya fuskantar matsaloli masu yawa.
Haka kuma Allah Maɗaukaki Ya ce:
الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ (Suratun Nisa’i: 34)
“Mazaje su ne masu kula da mata.” Wannan aya tana nuna cewa namiji ba kawai ya yi aure ba — yana da babban alhaki: ya ciyar da iyalinsa, ya koya musu tarbiyya da ilimi, ya samar da gidan da zai kasance mai albarka, tsari, da zaman lafiya.
Misalan rayuwa a yau suna bayyana abin da ke faruwa ga wadanda s**a yi aure da gaggawa.
Gaskiya mai zafi ita ce: aure ba wasa ba ne. Idan ba ka shirya ba, ba kai kaɗai ka lalata ba — har da matarka da ‘ya’yanka zasu fuskanci matsaloli. Ka tsaya ka duba rayuwarka: Shin ina da aiki ko sana’a mai ɗorewa? Shin zan iya ciyar da iyali ba tare da damuwa ba? Shin ina da tsari da hakuri? Shin zan iya gina gidan da zai zama mai albarka da kwanciyar hankali? Ka tuna: kadan daga halal ya fi yawa daga haram, albarka tana cikin abin da Allah Ya yarda da shi ne kawai.
Saboda haka, dan uwa, ka tsaya da kafafunka kafin ka yi aure. Ka shirya rayuwarka, ka nemi halal, ka gyara halinka, ka koya hakkin aure, ka samu tsari. Ka sani cewa aure amanar Allah ne, kuma za a tambaye ka yadda ka kula da ita. Allah Ya ba mu ikon yin aure cikin tsari, Ya tsarkake gidajenmu, Ya albarkaci iyalanmu, Ya kare mu daga kuskure da nadama. 🤲
Nura AG ✍🏻