28/07/2024
Yanzu-Yanzu: Ƙungiyar 13×13 ta gudanar da gangamin taron jaddada goyon baya ga Shugaba Tinubu a jihar Kano
Cikin bayanan da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana wasu daga cikin nasarorin da shugaba Tinubu ya cimma a cikin shekara ɗaya kacal waɗanda su ne s**a ja hankalinta wajen shirya gangamin taro na musamman domin yabawa gami da jaddada goyon baya a gare shi.
Nasarorin da ƙungiyar ta bayyana sun haɗa da:
1. Samowa ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kai a kotun ƙoli, wanda hakan zai ba wa al'umma damar samun tsaro da zaman lafiya gami da wadatar kuɗaɗe a hannun jama'a.
2. Ƙirƙiro da sabuwar ma'aikata musamman domin kula da dabbobi, kiwo, da harkokin fulani domin gina tattalin arziƙi da wadata ƙasa da abinci.
3. Sake buɗe iyakokin Najeriya (Boda) domin ƴan kasuwa su fita su sayo kayan abinci da sauran kayayyakin buƙata su shigo da su Najeriya tayadda za a kawar da matsalar hauhawar kayayyakin masarufi.
4. Kafa sabuwar hukumar raya yankin Arewa maso Yamma wadda ta haɗa Jihohin: Kano, Kaduna, Jigawa, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara tayadda arziƙi da cigaba za su wadata.
A jawabin da ya gabatar a wajen taron, shugaban ƙungiyar ta 13×13 reshen Jihar Kano, Muhammad Adam ya ja hankalin matasa da ka da su yarda wasu su yi amfani da su wajen lalata ƙasarsu da rusa tattalin arziƙin al'ummarsu, "shugaba Tinubu yana da kykkyawan fata, Wallahi ba shi ne ya jefa ƙasar nan a cikin matsi da talauci ba, mu kyautata masa zato". In ji shi.
Taron ya samu halartar shugaban gangamin na ƙasa gabaɗaya, Aminu Warkal tare da ɗumbin magoya baya daga sassa daban-daban na Jihar Kano.
Hausa Daily Times