12/06/2025
Darussa daga Hajji 2025 (3)
na kara daukan darasi gun Babban Malamin Sunnah a Nigeria Prof Mansur Ibrahim Sokoto mni.
bayan mun kammala zaman Madina, mun sauka a Makka a wani gida da aka sauke Manyan Malaman Nigeria kusan gaba dayan su,
Prof ya jagorancin mu Sallar Asuba, kammala Sallar shi ke da wuya bayan ya waigo sai ya ganni,.mu ka.gaisa nan take ya ce in yi Nasiha.
Gabana ya fadi (Ras) na ce Ni !!!! Ya ce kwarai kuwa, na kalli Manyan Shehunnan Nigeria, da Profesoshi, da Daktoci, da Mashahuran Alarammomi kai da kusan kowa da kowa a gabana.
Bayan da na iya, haka nan na mike na yi Nasiha gwargwadon abinda Allah ya ba ni iko.
Darussan da na koya ga su kamar haka.
1- Dattako daga gun wannan Babban Malami.
2- Yanda ya kamata Babba ya dinga karfafan na kasa da shi musamman abinda ya ke da tabbas na kasan zai iya gabatarwa.
3- Hidimomi da uzurori kada ka sake su raunana Haddarka ta Qur'ani, domin yadda Prof yake Barin Tilawa kai ka ce Sheikh Sudais ne
4- amfani da kowace Dama wajan yada Sunnah koda a gaban wadanda ba sa tinkaho da Sunnar.
5- duk lokacin da Allah ya daukaka ka a cikin. Al'umma, yi amfani da wannan daukakar wajan mutunta na kasa da kai, kada ka dan kwafe su.
6- na fahimci Malaman Ahlussun da mu Dalibai mu godewa Allah, a duk inda muka hadu da wadanda ba mu ba. Se kaga Malaman Sunnah kadai ke iya Nunfasawa.
Allah ka kara ma Prof da sauran Malaman Sunnah Albarka, ka kawo duk.wanda bai taba zuwa Hajji ba kasa mai tsarki amin.
Shuaibu Salihu Zaria Hajj 2025.