Haidar Karrar

  • Home
  • Haidar Karrar

Haidar Karrar Barka da zuwa shafin Haidar Karrar. Ka kasance damu domin samun abin da zai amfani zuciyarka Ni Mawaqine Masoyin Manzon Allah {Sww}🙏

Wannan shafi na rubuce-rubuce ne masu ma’ana, tunatarwa, da karfafa rayuwa cikin addinin Musulunci da darussa na yau da kullum.

Ba komai yake bukatar magana ba…Wani lokaci shiru shi ne amsar da zuciya take nema.Idan ka yi shiru, zaka ji komai ya fi...
16/11/2025

Ba komai yake bukatar magana ba…
Wani lokaci shiru shi ne amsar da zuciya take nema.
Idan ka yi shiru, zaka ji komai ya fito fili —
masu kaunarka, masu ƙarya, da abin da ya dace ka daina.

Rayuwa tamkar hanya ce mai tsawo…Wasu ranaku zaka yi dariya 😄, wasu kuma ka tattara zuciya ka yi hakuri.Amma duk abin da...
16/11/2025

Rayuwa tamkar hanya ce mai tsawo…
Wasu ranaku zaka yi dariya 😄, wasu kuma ka tattara zuciya ka yi hakuri.
Amma duk abin da ya zo maka, ka tabbata:
Wanda baya ƙoƙari, baya ganin cigaba.
Ka tashi ka yi naka, Allah zai yi nashi.

16/11/2025

🧠
Aure ko karatu… 😔
Don Allah kubani shawara 🙏

Wani lokaci zuciya tana jan mutum gefe guda, amma burin rayuwa yana jansa wani. Aure alkhairi ne, karatu ma haske ne.
Shawarata ita ce ka duba wacce hanya za ta baka nutsuwa, kwanciyar rai da makoma mai kyau.
Ba a yin zabi da gaggawa, kuma ba a yin sa saboda people pressure.
Ka tsaya ka tantance, ka yi addu’a, sannan ka bi hanyar da Allah Ya zaba maka. 🙏✨

Matakin Kiran Ki Uwa!Wani lokaci muna mantawa cewa kalmar “Uwa” ba suna ba ce kawai matsayi ne! Matsayi na ƙauna, juriya...
16/11/2025

Matakin Kiran Ki Uwa!

Wani lokaci muna mantawa cewa kalmar “Uwa” ba suna ba ce kawai matsayi ne! Matsayi na ƙauna, juriya, da sadaukarwa da babu wanda zai iya maye gurbin sa.

Ta haife ka cikin kunci,ta raine ka cikin wahala, taki barci saboda kukan ka, ta yi rashin lafiya, duk saboda kai. 🥺💔

Manzon Allah ﷺ ya ce:...........................................
Uwa ce, sannan uwa, sannan uwa, sannan uba.” (Bukhari da Muslim)

Wannan yana nufin darajar ta fi kowa, hakkin ta ya fi na kowa, rashin biyayya gare ta babban laifi ne a wajen Allah.

Hakkinta A Kanka:...........................................
1. Ka ji mata tausayin da ta ji maka tun daga ciki.

2. Ka taimaka mata da duka abin da kake da iko.

3. Ka yi mata magana cikin ladabi da ƙasƙantar da kai.

4. Ka dinga yi mata addu’a ko tana raye, ko ta rasu.

Ka sani:...........................................
Idan Allah ya yarda da kai ta hanyar mahaifiyar ka, to kana da haske a rayuwa. Amma idan ka wulakanta ta, wallahi rayuwa bata da daɗi ko da kana da komai.

Ka daina yin fushi da ita saboda ta gargaɗe ka. Wani lokaci zafin kalmarta alamar ƙauna ce, ba tsana ba.
Tana so ka zama abin alfahari a duniya da lahira ne.

⚠️ Uwa Gata Ce, Ba Za Ka San Darajarta Ba Sai Ka Rasa Ta. Domin wata rana zaka kira ta, amma ba zata amsa ba.🥺

Komai tashin hankali na rayuwa, ka koya kasake zuciya. Ba komai bane ya cancanci ka rasa nutsuwarka a kai. Wani lokaci s...
16/11/2025

Komai tashin hankali na rayuwa, ka koya kasake zuciya. Ba komai bane ya cancanci ka rasa nutsuwarka a kai. Wani lokaci shiru da sakewa sufi magana ƙarfi—sun fi kare ka fiye da faɗa ko damuwa.

Rayuwa ta koya min abu guda:Ba wai dole ne ka yi magana da yawa ba, a’a—wani lokaci dan taƙaitaccen abu yafi komai ƙarfi...
16/11/2025

Rayuwa ta koya min abu guda:
Ba wai dole ne ka yi magana da yawa ba, a’a—wani lokaci dan taƙaitaccen abu yafi komai ƙarfi.
Kamar yadda nake da kai, kalma kaɗan amma tana kai zuciya.
Mutum mai kirki baya yin hayaniya; aikinsa ne ke magana.

Idan Aka Cire Uwa Da Uba Waye Yafi Baka Gudunmawa Mafi Girma A Rayuwarka?
15/11/2025

Idan Aka Cire Uwa Da Uba Waye Yafi Baka Gudunmawa Mafi Girma A Rayuwarka?

Shin kuna samun kanku a wani yanayi da babu wani abu da aka muku, amma kawai kuna jin kamar kuyi kuka domin samun saukin...
15/11/2025

Shin kuna samun kanku a wani yanayi da babu wani abu da aka muku, amma kawai kuna jin kamar kuyi kuka domin samun saukin wata damuwa da baku san dalilinta ba?😭

A rayuwa ka zama kamar ruwa — baya yin ƙara amma yana canza komai. Ka rika yi wa mutane alheri ba don suna da shi ba, sa...
15/11/2025

A rayuwa ka zama kamar ruwa — baya yin ƙara amma yana canza komai. Ka rika yi wa mutane alheri ba don suna da shi ba, sai don kai ka saba zama mai kirki. Lokaci zai nuna wa kowa banbancin mutum mai zuciya da mutum mai surutu. Ka yi nisa cikin nutsuwa, ka yi ƙarfi cikin haƙuri, ka yi haske cikin kyawawan halaye.

15/11/2025

Annabi kaine abin yabona Kaine a zuciya ta wannan wakar tana sosamin raina Wallahi

Rayuwa tana da hanyoyi biyu: wata tana koya maka haƙuri, wata kuma tana koya maka kaucewa.Duk wanda ka gani shiru baya n...
15/11/2025

Rayuwa tana da hanyoyi biyu: wata tana koya maka haƙuri, wata kuma tana koya maka kaucewa.
Duk wanda ka gani shiru baya nufin baya jin zafi—sai dai ya koyi yin tafiya ba tare da surutu ba.
Wani lokaci shiru shi ne ƙarfin mutum, ba rauni ba.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Haidar Karrar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Haidar Karrar:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share