15/06/2025
Rigimar Daba a jihar Kano, laifin waye?
Daga Hadiza Nasir Ahmad
Ina hanyar komawa gida ranar Larabar da ta wuce, Ina cikin adaidaita sahu, sai muka biyo hanyar da naga taron wasu gungun mutane, dauke da makaman da ban taba ganin irinsu ba, cike da ruɗani na tambayi direban adaidaita sahun; Me ke faruwa? sai ya ce, “Fadan Daba,” sannan ya kara da cewa, “ki riƙe jakarki sosai.” Ya kara gudu da gaggawa yana ƙoƙarin tserewa daga hatsarin da ke tafe na wadancan yan Daban da s**a cike hanya suna sare-sare da kwace.
A nan ne fa direban ya cigaba da mun bayanin yadda yanayin Garin ya koma, ta yadda wadannan Yan Daba ke fita da Rana tsaka suna kwace wayoyi, kuɗi, ko kuma su kashe wanda yaki ba su abinda suke nema. A lokacin ne na fahimci cewa Allah ne ya cece ni ta hanyar dabara da ƙwarewar direban me adaidaita sahun da tuni nima sun mun kwace ko sun illatani.
Raina yayi mutukar baci yadda naga Matasa dauke da wadannan mugayen makamai, yadda mata da yara ke gudu cikin tsoro da kuka.
Na koma gida da mamaki da firgici, na bude wayata, na shiga kafafen sada zumunta, sai naga abun da yake trending kawai shine labarin kwacen waya da daba a kano. Yan Daba sun mamaye Kano, amma gwamnati ta gaza daukar mataki.
Tambayoyi s**a ta yawo a raina. Wasu sun ce ‘yan sanda sun daina jin maganar Gwamnatin Jihar Kano, suna sauraron Gwamnatin Tarayya kawai. Wasu kuwa sun ce sai kotu ta ba da umarni tukunna su yi aiki.
Ni dai ina ganin Gwamnatin Tarayya tana ƙoƙari wajen samar da tsaro.
Amma magance matsalar Daba abu ne da yake hannun Gwamnatin jiha.
Wannan ba batun Shari'a bane dake gaban kotu a'a batun rayuka ne. Gwamnatin jihar Kano ba ta da uzuri, dole ne ta daina wasan siyasa da harkar Daba, ta tashi tsaye.
Lamarin kullum sai tsananta yake yi. A na rasa rayuka, amma babu wata magana daga gwamnati, babu kwantar da hankali, babu daukar wani mataki.
Ina ganin ‘yan sanda suna iyakar ƙoƙarinsu. Amma idan gwamnatin jihar ta ci gaba da nuna halin ko-in-kula, ta yi shiru, sannan