05/07/2025
RANAR TSINUWA
*
Allah yayi abubuwa da yawa na farinciki ga al'umma wayanda s**a gabata da al'ummar zamanin Annabi ﷺ, wanda haka yana cikin dalilin da yasa Annabi ﷺ ya yarda da yi azumi a wannan rana domin godiya ga Allah SWT.
To amma duk abubuwan da Allah yayi a baya na farinciki, nauyin su bai kai abinda yayi na jarrabawa ga muminai ba kwaya ɗaya, wanda ya faru bayan Annabi ﷺ yayi wafati, wato shahadar Imam Hussaini Alaihis salam.
Wasu malamai suna cewa "Da Jikokin Annabi ﷺ da wayanda s**a cutar dasu din, duk sun koma ga Allah don haka bai kamata a cigaba da juyayin abin aya faru ba", wannan kuskure ne mai girma, sun manta dalilin yin azumin Ashura ne, ai da wanda aka kuɓutar da wanda aka kuɓuta daga gareshi duk sun koma ga Allah, meye namu na jindadi har da yin azumi, sun yarda wancan ya dace amma nuna alhini ga wayanda soyayyar su ta zama wajibi shine kuskure? Abin mamaki!
Annabi ﷺ ya ba Sayyada Ummu Salma ƙasar karbala wanda Jibrilu ya kawo, yace mata "ƙasar nan zata zama jini a ranar da s**a kashe Hussaini", haka kuwa ya faru, kuma bayan sun kashe shi sun cire kan sa, sai s**a ga a jikin wani dutse an rubuta:
"أَتَقْتُلُونَ سِبْطَ النَّبِيِّ وَيَسْأَلُونَ بِجَدِّهِ الشَّفَاعَةَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ"
Ma'ana: Za ku kashe jikan Annabi ﷺ sannan ku roki ceton kakan sa ranar alkiyama?
Bayan kisa da tozarci da s**a yiwa jikokin Annabi ﷺ, kowani juma'a yayin huɗuba sai sun tsinewa Imam Ali (kw) basu gushe suna tsine masa ba har sai lokacin mulkin Umar Bin Sulaiman RTA, shi ya kawo ƙarshen wannan tsinuwar.
Ranar lahira, Sayyada Fadimah A.S zata tafi gaban Allah, hannun ta riƙe da rigar da Imam Hussaini yayi shahada da ita, dumu-dumu da jini, zata ɗaga rigar tace:
يَا رَبِّ، خُذْ لِي بِحَقِّي وَوَلَدِي
"Ya Ubangiji, ka kwato min hakki na da na ɗa na".
Kafin wannan ranar, za mu cigaba da tsinuwa ga Yazidu ɗan Mu'awiya da sojojin sa da wa'yanda suke farinciki da ta'addancin sa, domin Maulan mu Shehu Ahmadu Tijjāni RTA yana cewa "Yazidu tsinanne ne saboda aya ta 57 a Suratul Ahzab da aya ta 22-23 a Suratul Muhammad, babu cutarwa ga Annabi ﷺ wacce ta wuce kashe ɗan sa".
Azumi na na yau, na bada shi hadiyya ga Annabi ﷺ ina mai yi masa ta'aziyyar abinda ya sami jikokin sa masu albarka, Allah ka tsinewa yazidu da magoya bayan sa a jiya da yau da gobe, fiye da tsinuwar da ka yiwa Iblis.
LABBAIKA YA HUSSAIN.
Daga: Sidi Sadauki