Qugiya Hausa

Qugiya Hausa Qugiya Hausa Jarida ce ta Online dake Kawo Maku Ingatattun Labaran Cikin Gida Najeriya da Kasashen Ketare.

Idan Kuna Buƙatar Tallace-tallace Ku Tuntuɓi Wannan Number 👉09044351991

15/07/2025

YANZU-YANZU : Sheikh Nura Khalid ya magantu akan Asibitin da Buhari ya rasu.

ALLAHU AKBAR: Masu Taya Buhari Aiki A Gidansa Sun Roka Masa Allah Gafara.
15/07/2025

ALLAHU AKBAR: Masu Taya Buhari Aiki A Gidansa Sun Roka Masa Allah Gafara.

Karin Hotunan Yadda Aka Binne Gawar Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A Gidansa Dake Daura, Jihar Katsina Yau Talata...
15/07/2025

Karin Hotunan Yadda Aka Binne Gawar Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A Gidansa Dake Daura, Jihar Katsina Yau Talata

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

YANZU-YANZU: An iso da Gâwár Buhari birnin Katsina har an wuce da ita garin Daura domin yi masa Janaza.
15/07/2025

YANZU-YANZU: An iso da Gâwár Buhari birnin Katsina har an wuce da ita garin Daura domin yi masa Janaza.

15/07/2025

YANZU-YANZU : Daga Katsina, Ana Jiran Isowar Gawar Tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari.

YANZU-YANZU: Uwargidan Shugaban Ƙasa Sanata Remi Tinubu ta isa Katsina kan hanyarta zuwa Daura wurin jana'izar Buhari.
15/07/2025

YANZU-YANZU: Uwargidan Shugaban Ƙasa Sanata Remi Tinubu ta isa Katsina kan hanyarta zuwa Daura wurin jana'izar Buhari.

Fatima Buhari ta Tsinke da kuka bayan Isanta Gidan Mahaifinta dake Birnin Daura.
15/07/2025

Fatima Buhari ta Tsinke da kuka bayan Isanta Gidan Mahaifinta dake Birnin Daura.

DA DUMIDUMINSA: An Gudanar Da Salatul Ga'ib Ga Marigayi Muhammadu Buhari A Jhar GombeYadda dandazon daruruwan musulmai s...
15/07/2025

DA DUMIDUMINSA: An Gudanar Da Salatul Ga'ib Ga Marigayi Muhammadu Buhari A Jhar Gombe

Yadda dandazon daruruwan musulmai s**a halarci Salatul Ga'ib na marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, yau Talata a anguwan Pantami Stadium, cikin kwaryar jihar Gombe.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Tawagar Jamhuriyar Nijar ta isa Katsina domin halartar jana'izar tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari
15/07/2025

Tawagar Jamhuriyar Nijar ta isa Katsina domin halartar jana'izar tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari

HOTUNA: An gama Gina ramun Kabarin da za a saka marigayi janar Buhari. Yanzu ana dakon isowarsa.
15/07/2025

HOTUNA: An gama Gina ramun Kabarin da za a saka marigayi janar Buhari. Yanzu ana dakon isowarsa.

Da duminsa; Jirgin dake ɗauke gawar Buhari ta bar London, ta nufo Katsina Nijeriya kai tsaye
15/07/2025

Da duminsa; Jirgin dake ɗauke gawar Buhari ta bar London, ta nufo Katsina Nijeriya kai tsaye

Allah Ya ji kan Buhari: A Bar Gaskiya ta yi Halinta Muhammadu Buhari ya rasu — tsohon shugaban da ya shigo da sunan wand...
15/07/2025

Allah Ya ji kan Buhari: A Bar Gaskiya ta yi Halinta

Muhammadu Buhari ya rasu — tsohon shugaban da ya shigo da sunan wanda zai tsirantar da al’umma, amma ya bar ta cikin bakin ciki, talauci, da rashin gaskiya.

Ya sha neman mulki. Ya dauki alkawura. Ya samu amincewar talakawa. Amma abin da ya bari?
– Matasa ba aiki.
– Ƙananan ‘yan sanda da sojoji suna azabtuwa.
- Cire manyan ‘Yan Sanda daga tsarin CPS na zalunci
– Kudin fansho ya zama arzikin wasu barayi
– Manoma, malamai, ma’aikata — dukkansu sun zama marasa ƙarfi a garuruwansu.
– Gwamnatinsa ta zama mafaka ga barayi da azzalumai.

Ya rasu a asibitin ƙasar waje — abin da yawancin talakawa ba su da damar zuwa ko mafarkin samu idan ba su da lafiya.

Amma Dole Mu Fadi Gaskiya:

A al’adance kuma a addinance, muna addu’a ga matattu. Amma mu ‘Yan Gaskiya ba za mu binne Gaskiya ba. Idan ka yi mulki ka jawo mutuwar wasu, ka jawo wahala, ka karya alkawura — to babu wanda ya isa ya wanke ka a tarihi.

Gaskiyar da muke Gudu:

Yafiya ba gazawa bane. Amma tunanin cewa ba za mu yi kamar ba’a zalunci talaka ba don mutum ya koma ga ubangiji — hakan ne ke sa azzalumai da barayi su ci gaba da cin zarafinmu su na satar arzikinmu.

Mu roƙi gafara a matsayin Musulmi — amma ba za mu karyata tarihi ba.

Buhari bai zama waliyi ba saboda ya rasu. Kuma ba zai tsira daga abunda yayi a tarihi ba.

✊🏽 Dan Bello | ‘Yan Gaskiya

Address


Telephone

+2349033391934

Website

http://Qugiyahausa.com.ng/

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Qugiya Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Qugiya Hausa:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share