16/06/2025
SHAWARA ZUWA GA MAI GIRMA SHUGABAN KASAR NIGERIA DA SHUGABAN JAM'IYYAR APC NA KASA.
Mun Sami Labarin Abubuwan da s**a Faru A Babban Taron Jam,iyyar APC Na Arewa maso Gabas,
Dangane da Suna ganin Shugaban Kasa bazai tafi da Dansu Wato Kahim Shattuma ba A Kakar zabe Mai Zuwa 2027
Shine Har Daya Daga Cikin Yaransa Gwamnan Jihar Borno Prof. Babagana Zulum yakeyin Wasu maganganu Na Rashin Da'ah har yake Cewa Idan babu Kashim Shattima Babu Northeast,
Mukuma Mukacemasa Akwai Kahsim Shattima An Rasa Kuru,un Northeast din A 2023 ko yamantane,
Bawa Kahsim Shattima Mataimakin Shugaban Kasa daga Northeast Asara yajawowa APC Domin Akwai Jahohin da APC batataba faduwaba Amma Saboda da Bawa Kahsim Shattima Mataimakin Shugaban Kasa saida APC ta fadi A 2023
Ga Sakamakon yadda Zaben 2023 Na Shugaban Kasa ya kasance Dukda Akwai Kahsim Shattima.
(1) Borno State. APC. 252,282 PDP. 190,921.
(2) Adamawa State. APC. 182,881. PDP 417,611.
(3) Bauchi State. APC .316,694 PDP. 426,607.
(4) Yobe State. APC. 151,449. PDP. 198567.
(5) Taraba State. APC. 135,165. PDP. 189,017.
(6) Gombe State. APC. 146,977. PDP. 160,000.
Dukda Akwai Kahsim Shattima Acikin jihohi 6 dasuke Northeast jiharsa kawai ya iya ciyowa itama Akwai magun magun Acikin harkar. TINUBU yafadi Jiha Biyar kenan,
TOTAL DIN KURU'UN DA ASUWAJU BOLA AHMAD TINUBU TARE DA KASHIM SHATTIMA S**A SAMU A NORTHEAST DIN .APC....1,185,458.
ATIKU ABUBAKAR NA PDP YASAMU KURU'U 1,438,723.
TAMBAYA TA ZUWA GA GWAMNA PROF. ZULUM.
(1) Wacce irin Gudunmowa kuka bayar kaida Mai Gidanka Kashim A Northeast?
(2) Ko 2023 Babu Kashim ne shiyasa muka fadi jihohi 5 Acikin 6?
(3) Ya Akayi Shugaba Buhari da ba Dan Northeast ba yake iya cin zabe A Borno Yobe da Gwambe, Kahsim Dan Northeast yafadi?
SHAWARA TA ITACE KAMAR HAKA.
Kasan Cewar Fadin Allah Subhanahu Wata'ala Cewa shiyake bada Mulki ga Wanda yaso kuma Lokacin da yaso, Kuma ita Wannan Gwamnatin Ankafatane da Musulum Musulum,To yakamata muyi imani da cewa Wanda yabaku yananan kuma baya Barci,
Ku Ajiye Wannan Mataimakin Shugaban Kasar Kashim Shattima Duba da Rashin sanin Wannan Ayar dayanunawa Duniya, Da zaremuku ido dayakeyi da Barazanar Banza dayakeyi ku Dogara da Allah,
Kuduba A Northwest ku dauko Daya daga Cikin mutane Biyunnan kusanyashi A matsayin Mataimakin Tinubu, Acikin Ikon Allah da Yardarsa zamu ci zabe Da gagarumin Rinjaye.
Ko Kuzo JIhar Kano kudauki .DPS. DR. BARAU I JIBRIN MALIYA.
Duba da yadda yake kokari A Dukkannin fadin jihohi 7 dasuke Northwest.
Ko kuzo Zamfara Kudauko DR. SEN. ABDUL,AZIZ YARI, Duba da Tsohon Gwamna ne Kuma yanata tiri tiri da Yan jam,iyya A fadin Northwest,
Idan kayi haka Asuwaju Bola Ahmad Tinubu zai cinye jihohi Arewacin Nigeria Acikin Ruwan Sanyi in sha Allah,
DALILAINA SUNA DA YAWA,AMMA BARI NA FARA KAWO GUDA UKU YANZU KAFIN RUBUTUNA NA GABA.
(1) Kowa yayarda Babu inda Ake da Tarin kuru,u kamar Northwest, Domin ko wancen zaben daya wuce na 2023 Tinubu yasami kuri,u 2,169,952.. Idan kuwa Mataimakin Shugaban Kasa Dan Northwest inada Tabbacin cewa Sai Kuri,a sama 5,000,000 tafito daga yankin in sha Allah.
(2) Duk Dan Northeast zai Ajiye Maganar wata Jam,iyyarsa yayi Tinubu Saboda yanajin kashin samun Shugaban Kasa ban da Shekaru hudu masu zuwa,
(3) Dukkanninsu Matasane masu Jini Ajika kuma masu kishin yankinsu da Kasa baki daya, kuma kudu Da Arewa Babu inda basu da Abokan mu,amula Sannan zasu karawa Shugaban Kasa kwarin gwaiwa waja ciyar da Kasa gaba, Sannan basu da kabilanci ko wani yare Idan babu Hausa ba.
Wadannan sune kadan Daga Cikin Dalilan Nawa kafin Rubutu na gaba.
Akarshe ina Adduar Allah yabamu lfy da zaman lfy A Kasarmu Nigeria
Allah yazaunar da jam,iyyarmu ta APC lfy.
Allah yazabamana Shugabanni Nagari masu jin Tausayinmu.
Allah yasa Shugaban Kasa da Shugaban Jam l,iyyarmu ta APC suduba Wannan Shawarar tawa da idon Basira.
Hon. Malami Abubakar Nasidi. Kano