Azare Media

Azare Media Media

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na duba yiwuwar karin haraji a kan kiran waya a fadin kasar.Minti daya na kiran waya ...
08/08/2022

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na duba yiwuwar karin haraji a kan kiran waya a fadin kasar.

Minti daya na kiran waya zai kai kusan Naira 40. Ya wannan sabon shirin na karin haraji da ake gab da aiwatar da shi ya zo muku?

DW Hausa

Tsohon Abokin Dan Kwallon Nijeriya, Ahmed Musa Tun Na Kuruciya Na CigiyarsaTsohon abokin dan kwallon Nijeriya Ahmed Musa...
07/08/2022

Tsohon Abokin Dan Kwallon Nijeriya, Ahmed Musa Tun Na Kuruciya Na Cigiyarsa

Tsohon abokin dan kwallon Nijeriya Ahmed Musa wanda s**a taso tun yarinta a Layin Giginya dake Unguwar Bukur a garin Jos yana cigiyar aminin nasa biyo ya rasa yadda zai yi su yi ido hudu.

Mutumin ya ce Ahmed Musa ya fi saninsa da Gwamna, wato sunan da ake kiransa da shi a lokacin, sannan kuma ya bayyana cewa bacci ne kawai yake raba su da Ahmed Musa a lokacin kuruciyar su, inda a wasu lokutan ma suna kwana ne a gidajen juna, wato wani lokaci ya kwana a gidan su Ahmed Musa, shi ma kuma Ahmed Musa ya kwana a gidansu.

Saidai rahotanni sun nuna cewa Gwamna yana cikin kuncin rayuwa wanda yake bukatar tallafi.

Ya ce ya fi wata biyar yana ta kokarin ganin yadda za a yi a hada shi da Aminin nasa, amma burinsa har yanzu bai cika ba, don haka ne ya ce bari ya biyo ta kafar sadarwa ko Allah zai sa Ahmed Musan ya gani ya neme shi.

A cikin wadannan hotunan za a iya ganin Ahmed Musa da Gwamna, inda aka sa musu alama akansu.

Don haka ne ma Gwamna ya ajiye lambarsa don kira kai tsaye idan Allah ya sa Ahmed Musan ya ci karo da labarin; 07069204905

BBC Hausa  ba ku kai shekaru 13 baWani matashin ɗan Najeriya mai amfani da kafafen sada zumunta mai suna Ɗahiru Mukhtary...
04/08/2022

BBC Hausa ba ku kai shekaru 13 ba

Wani matashin ɗan Najeriya mai amfani da kafafen sada zumunta mai suna Ɗahiru Mukhtar
ya musanta ikirarin da BBC tayi a yau na cika shekara sha uku da buɗe shafin su na Facebook matashin yayi bayani dalla dalla akan shafin na BBC Hausa
To ga dai rubutun nasa a ƙasa

BBC Hausa ba ku kai shekara 13
da bude wannan shafin na ku ba sai nan da ranar 5 ga watan Janairun 2023 ne kuka cika shekaru 13 cif-cif. Saboda na duba "page transparency" na wannan shafi na ku, sai na ga kun bude shi ne a "January 5, 2010" Idan muka ce shekarar da muke ciki yanzu 2022 a debe 2010 shekarar da kuka bude shafin zai bada shekaru 12 kenan ba 13 ba.

- Sannan akwai mutane (47) dake kula maku da shafin BBC Hausa daga kasar Landan (United Kingdom 🇬🇧)

- Sai kuma mutane (29) dake kula maku da shafin BBC Hausa daga Nigeria 🇳🇬

- Akwai mutane (3) dake kula maku da shafin BBC Hausa daga kasar Kenya 🇰🇪

- Haka nan kuma akwai wasu mutum (1) daga kasar Cameroon 🇨🇲 , mutum (1) daga kasar India 🇮🇳, mutum (1) daga kasar Spain 🇪🇸 da kuma wani mutum (1) daga kasar America 🇺🇸

Duk wanda bai yarda da wannan bayanin nawa ba ya je ya duba "page transparency" na wannan shafi na BBC Hausa ya duba ta can kasa zai ga ranar da aka bude shafin da kuma mutanen da suke kula da shafin BBC Hausa daga wadancan kasashen dana lissafa. . - MD
Shin hakan yana nufin sun yi kuskure ne ko kuma dai kawai dai🤔

© Ɗahiru Mukhtar

Ku kiyayi Wannan Asibiti mai suna General Hospital Azare wadda akafi sani da Asibitin Ali k'wara.Ko miyasa nace haka ??Y...
03/08/2022

Ku kiyayi Wannan Asibiti mai suna General Hospital Azare wadda akafi sani da Asibitin Ali k'wara.

Ko miyasa nace haka ??
Y'ar uwata ta dauki danta cikin yanayi na rashin lpy mai tsanani takaiga yaron wuyansa yabar ikon gangar jikinsa saboda tsananin ciwon da yake damunsa ,Bayan taje wannan Asibiti taje Emergency domin abashi agajin gaggawa , hakan ta farune bayan sallar isha'i kadan ,anbawa yaronta gado to Amma babu wani wadda yazo domin ya duba yaron har garin Allah ya waye , hakan yasa mahaifiyar yaron taje Emergency ta sake report akan abunda ke faruwa Amma babu wani wadda ya shaurareta sai wani mutum guda daga cikin ma'aikatan yazo yace mata in zata biyashi zaizo ya dorawa yaronta ruwa hakan yasa ranta ya b'aci ta fara fad'a ganin haka yasa ya janye maganar karban kud'i yazo ya dorawa yaronta ruwan wadda hakanma bayan zuwan in charge na wurin ta gane bai samo jijiyar ba kawai ya lojana kalular ne ya tafi kayansa .

Bayan sun kwana 2 a Wannan Asibiti wani daga cikin ma'aikatan yazo ya rubuta musu allurai guda 2 yace a siyo yanzu yayi masa , bayan an siyo yayi masa allurar daganan yaron ya k'ara shiga wani hali fiyeda yadda yake ada. Dasafe saiga in charge ta wannan wuri tazo taga yadda yaron yake take tambaya aka nuna mata allurar da Wannan mutumi yayiwa yaron ganin haka tasa aka kirawoshi daga zuwansa ta fara masa fad'a ashe allurar masu ciwon k'oda yayiwa yaron da baya magana kuma a lokacin take tabbatar wa mahaifiyar yaron ashe shi mai shara ne (cleaner) .

To kunji yadda Wannan Asibiti yake kuma ga yadda suke aiki bisa ganganci da kuma wasa da rayuwar mutane.

Abdullahi Ibrahim tsafi

Ɗan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Labour party Peter Obi ya kai wa Babangida ziyarar girmamawa da neman ta...
15/07/2022

Ɗan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Labour party Peter Obi ya kai wa Babangida ziyarar girmamawa da neman tabarraki

Shin hakan zai sa ƴan Arewa su Zaɓe shi?

Kimanin mutane dubu shida da ɗari uku da goma ne  aka k**a a ƙasar Saudiyya suna ƙoƙarin yin aikin Hajji ba tare da izni...
11/07/2022

Kimanin mutane dubu shida da ɗari uku da goma ne aka k**a a ƙasar Saudiyya suna ƙoƙarin yin aikin Hajji ba tare da iznin hukumomi ba

Shin kuna ganin ya dace a k**a su?

A Najeriya, ga dukkan alamu yanayin tsaro na kara tabarbarewa a kasar inda a baya bayan nan aka kai hari kan ayarin shug...
08/07/2022

A Najeriya, ga dukkan alamu yanayin tsaro na kara tabarbarewa a kasar inda a baya bayan nan aka kai hari kan ayarin shugaban kasa da gidan gyaran hali na Kuje da ke babban birnin kasar.

Sai dai masana na ganin rashin hukunta masu sakaci na kara dagula lamarin.

Tor me kuke ganin yake janyo daburcewar al’amuran tsaro a kasar?

Wasu daga cikin batutuwan da muke fatan tattaunawa ke nan a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

© BBC Hausa

Duk Wanda Yasan Ya Gudu Daga Gidan Yarin Kuje Ya Gaggauta Komawa Kafin Nan Zuwa Yamma. -Muhammadu Buhari
08/07/2022

Duk Wanda Yasan Ya Gudu Daga Gidan Yarin Kuje Ya Gaggauta Komawa Kafin Nan Zuwa Yamma.

-Muhammadu Buhari

An k**a wasu matasa da ake zargi da satar turƙeƙen ragon SallahRagoJami’an ‘yan sandan jihar Ogun sun k**a wasumatasa bi...
07/07/2022

An k**a wasu matasa da ake zargi da satar turƙeƙen ragon Sallah
Rago

Jami’an ‘yan sandan jihar Ogun sun k**a wasumatasa biyubisa zargin satar ragon Sallar wani mutum Sadiq Abolore wanda kudinsa ya kai Naira 120,000.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Mista Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana k**a wadanda ake zargin.

Oyeyemi ya ce “An k**a wadanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da Sadik Abolore ya kai hedikwatar ƴan sanda da ke Ogijo.

Ya ce yanzu haka za a ci gaba da gudanar da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.

Muhammad Sani Dattijo Yana Da Siffofin Da Ba Kowanne Matashi Bane Yake Da irinsu.A lokacin da wasu ƴan siyasun ƙasar mu ...
07/07/2022

Muhammad Sani Dattijo Yana Da Siffofin Da Ba Kowanne Matashi Bane Yake Da irinsu.

A lokacin da wasu ƴan siyasun ƙasar mu suke ƙyamar ta al’umma shi kuma a dai-dai wannan lokacin yake rike su hanu biyu-biyu domin inganta rayuwar su ta hanya madaidaiciya. Ayyukan sa a kullum bai wuce ganin rayuwa talaka ta inganta k**ar Kowa ba.

Ba karamin rabo Shiyar Kaduna ta tsakiya s**a yi ba na samun Hazikin Matashi, Jarumi, Ƙwararre a fannoni daban-daban yana da matuƙar wahala kasamu matashi mai sauƙin kai irinsa. Yana iya mu’amala da kowa baya raina mutum yana daraja kowa babba da yaro.

Ƙiran mu a kullum tare da rokon alfarmar mu. Bai wuce akan al’umma su bawa wannan Bawan Allah dama domin bada tasa gudummawar a yankin mu mai albarka ba. Muna masa kyakkyawan zato kasancewar sa mutumin kirki mai Dattaku da sanin Yak**ata.

Zaben jin ra'ayin jama'aShin wanene zabin ku a cikin su?
02/03/2022

Zaben jin ra'ayin jama'a

Shin wanene zabin ku a cikin su?

Kotu ta bada umarnin ƙwace kadarori 10 a Abuja da Kaduna da kuma wasu kuɗaɗe a Amurka ma su alaƙa da YariWata Babbar Kot...
23/02/2022

Kotu ta bada umarnin ƙwace kadarori 10 a Abuja da Kaduna da kuma wasu kuɗaɗe a Amurka ma su alaƙa da Yari

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kwace wasu kadarori 10 da kudade a bankuna na wucin-gadi, da a ke zargin na tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ne.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa Mai shari’a Obiora Egwuatu ya bada wannan umarni ne a ranar Laraba ya yin da ya ke yanke hukunci kan karar da lauyan ICPC, Osuobeni Ekoi-Akponimisingha ya gabatar.

Egwuatu ya ce umurnin na wucin gadi da aka bayar zai dauki tsawon kwanaki 60 don baiwa hukumar ICPC damar kammala binciken ta, daga nan ne hukumar za ta iya neman a kwace kadarorin na dindindin.

Alkalin ya umurci ICPC da ta bayyana wannan umarni ga duk wani mutum ko masu sha’awar kadarorin na da kwanaki 14 don a nuna cewa kotu ta na da ikon ƙwace kadarorin na dindindin.

A cewa ICPC, wasu da ga cikin kadarorin na Maryland da ke Amurka, Abuja, Kaduna da sauran gurare.

Daily Nigerian Hausa

Yau ƴan Najeriya suna cike da farin cikin dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Turai bayan ziyarar aiki ta kwana ...
19/02/2022

Yau ƴan Najeriya suna cike da farin cikin dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Turai bayan ziyarar aiki ta kwana huɗu da yayi

Shin da gaske ƴan ƙasa kuna cike da farin cikin?

DA ƊUMI-ƊUMI: Abdulmalik Tanko ya musanta garkuwa da kuma kashe HanifaAbdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa ...
14/02/2022

DA ƊUMI-ƊUMI: Abdulmalik Tanko ya musanta garkuwa da kuma kashe Hanifa

Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa da kuma kashe dalibarsa, Hanifa Abubakar, ƴar shekara 5, ya musanta garkuwa da kuma kashe ta.

A yau Litinin ne a ka sake kawo Tanko, da abokan aikata laifin da a ke zargi, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin a gaban Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin Alƙali Usman Na-Abba.

Bayan da a ka karanto musu tuhume -tuhumen da a ke yi musu, dukkan su sun musanta.

Da a ke tuhumar Tanko cewa ya yi garkuwa da kuma kashe Hanifa, sai ya ce "ban aikata ba."

Ƙarin bayani na nan tafe...

Daily Nigerian Hausa

Address


Telephone

+2347067289098

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Azare Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share