
08/08/2025
Kungiyoyi Dalibai A Jihar Bauchi Sun Mara Wa Hon Farouk Mustapha Baya Domin Takarar Gwamnan A Zaɓen 2027
Kungiyoyin ɗalibai na ƙananan hukumomi 20 na jihar, ƙarƙashin jagorancin Hon. Hamza Muhammad Maikudi — mai ba Gwamnan Bauchi shawara na musamman kan harkokin ɗalibai — sun kai ziyarar tabbatar da goyon baya ga Rt. Hon. Farouk Mustapha, kwamishinan ci gaban karkara da harkokin musamman.
Wannan matakin ya nuna ƙara samun ƙarfin gwiwar Farouk Mustapha a siyasar jihar, duba da irin tasirin da ƙungiyoyin ɗalibai ke da shi wajen tsara makomar jihar.
Bayan jerin tattaunawa da bukukuwan taya murna da aka gudanar a cikin da wajen al’ummar ɗalibai, ƙungiyoyin sun bayyana Farouk Mustapha a matsayin ɗan siyasa mai kishin al’umma, tare da nuna gamsuwa da rawar da ya takawa wajen inganta rayuwar matasa da tallafa musu.
Da yake mayar da martani kan wannan goyon baya, Rt. Hon. Farouk Mustapha ya bayyana godiya, yana mai cewa har yanzu yana shawara da iyali, abokai, da kuma Gwamnan Jihar kan makomar siyasar da zai dauka. Ya kuma jaddada cewa haɗin kan matasa da tallafin al’umma shi ne ginshiƙin nasara a kowace irin fafutuka ta siyasa.
Masu sharhi na ganin wannan matakin na iya zama babban abin da zai rinjayi manufar siyasar jihar Bauchi a 2027, duba da yadda matasa za su iya zama ginshiƙin goyon baya mai ƙarfi ga Farouk Mustapha a ko’ina cikin jihar.
KBC Hausa