06/08/2025
Barr. Abdul-Hadee Isah Ibraheem ✍️
Zai iya yiwuwa nan gaba k**ar shekaru 50 ko 80 masu zuwa ginin Makarantu da Bankuna su bace daga doron 'kasa, wato physical structures ya zama babu su.
Zai iya kasancewa nan gaba a rasa 'yan sanda ko sojojin da zasu dauki bindiga su kare kasar su daga cikin mutane.
Abu ne mai sauki yayin school Certificate ya zama tarihi, wato kaje makaranta ka kammala a baka certificate ya zama tsohon yayi.
~ Babu mamaki nan gaba kadan kana zaune a gidan ku a Lagos ko Bauchi zaka sayi Turare daga kasuwar Sabon Garin Kano, kana daga wajen zaka ji kamshin Turare ka zabi wanda kake so a kawo maka cikin minti 1 ko 2.
Ba mamaki nan gaba yin amfani da waya, phone call ko typing rubutu ya zama tsohon yayi har a dinga cewa haka mutane da suke zama suyi typing rubutu.
Ba mamaki nan gaba kana zaune a gida Likita zai duba ka, zai ji jikin ka akwai zafi ko sanyi, yayi maka Allura daga inda yake kai kana gida.
Nan gaba zai iya yiwuwa a daina amfani da Motoci, Babur, Jirgin sama ko Jirgin ruwa a matsayin Ababen hawa, by then duniya zata samar da wasu hanyoyi sufuri ba wannan ba.
Idan nace nan gaba kadan Ababen hawa zasu daina amfani da Gas ko Man fetur mutane zasu fi saurin hararo wannan da gaggawa. Nan gaba Man fetur da Gas amfanin sa zai kare ko zai ragu sosai ya zama yin amfani dashi ba dole ba, k**ar yadda shan Maltina ko Pepsi ba dole ba.
Zai iya yiwuwa nan gaba a daina siyar da wutar lantarki ko, cibiyoyi da kamfanonin samar da wutar lantarki duk za'a iya neman su a rasa.
Zai iya yiwuwa nan gaba Bitcoin ya kai farashin Dala miliyan 10, sannan a samu wasu token da zasu zarce shi a kudi, amma still shi zai jagoranci kasuwar Crypto saboda karfin Decentralisation da Security dinsa.
Nan gaba za'a shafe wannan Al-Qur'anin, ko ka bude ba zaka ga rubutun Ayoyin Allah a ciki ba, gara ka haddace tun ba'a je wajen ba.
Nan gaba wani mutum daga Afrika zai je ya rusa dakin Ka'abah yayi ta'adi mai yawa ga duniya da Musulmi.
Zai yiwu nan gaba ba zaka iya rubuta shafi biyar na Exercise Book 📖 ba a tsakanin sallar Azahar La'asar, saboda karancin lokacin.
Ba mamaki nan gaba a iya tracing kuma ayi tracking mutum a gano inda yake ta hanyar amfani da Blockchain ko wallet address da kayi amfani dashi k**ar yadda yanzu ake tracing da tracking mutum ta hanyar amfani da lambar wayar sa.
Watakila nan gaba za'a samar da consensus algorithm da zasu yi wannan aikin ba PoW, PoS, PoH, PoA ko DPoS da ake amfani dasu a yanzu ba.
Tabbas ne nan gaba samun kudi ba zai zama kalubalen dan Adam ba, mutanen da suke rayuwa a doron kasa zasu manta da matsalar samun kuɗi na dan wani lokaci, kudi zai zama k**ar garin kasa (soil) ta yadda ko kayi kyauta dashi babu mai so, domin kowa yana dashi.
Zai iya yiwuwa nan gaba a rasa Dazuka da Forest saboda yawan mutane, garuruwa zasu fadadu su hade birane da ƙauyuka duniya ta zama gari daya a zahiri.
Zai iya yiwuwa nan gaba a rasa gwamnati ko kuma tsarin zabe ya zama tsohon yayi. Duniya zata iya gudana akan tsarin DAO (Decentralised Autonomous Organization) ko wani abu mai k**a da wannan, da wahala nan gaba ace ga wani mutum shine shugaban kasa, gwamna ko Ministan, mutane su zasu mulkin kansu da kansu k**ar yadda kaga DAO ke gudana a tsarin public blockchain networks.
Zai yiwu nan gaba kadan bayan karanta wannan rubutu kai karanta rubutun ya tabbatar ma kanka cewa yau bai karanta Al-Qur'ani ba kuma bai yi Salatin Manzon Allah (S.A.W) ba. So, karanta yanzu ko Ayoyi uku ne daga cikin wayar ka, sannan kayi Salati ga fiyayyen halitta, yin hakan zai zama maka tsira ranar da bayi zasu tashi su tsaya a gaban Ubangijin su.