04/12/2024
WANI JINKIRIN ALKHAIRI NE 'YAR UWA.
Sau da yawa za ka samu mace ta kai wani mataki wanda ya kamata a ce ta yi aure amma har yanzu ba ta yi ba, age-mates ďinta sun yi aure wasu ma har da 'yaƴa, ita kuma bata yi ba, qin yin auren ba daga gare ta bane, itama tana so, sai dai kuma har yanzu Allah bai kawo mata mijin aure ba. 'Yar uwa wannan ba komai bane illa jarabawa daga Allah Mabuwayi, mai yiyuwa ya jarrabe ki ne domin Ya ga yadda za ki yi, idan kika yi hakuri kuma kika mayar da Al'amuranki ga Allah, sai ki ga Ya kawo maki miji adali mai addini da kyawawan dabi'u da dukkan siffofin da mace za ta bukata a wajen namiji ta hanyar da ba ki yi tsammani ba 'yar uwa.
Allah Shi ne Ya yi alkawarin zai jarrabi muminai a duniya da jarabawa iri-iri, kuma Ya ce Lallai a yi bushara ga masu hakuri. 'Yar uwa wani irin babban rabo k**e tunani Allah Ya tanadar maki idan kika kasance cikin masu hakuri.
Hakurin shi ne a kowane lokaci ki dinga jin Allah Yana son ki, kuma Yana sane da halin da k**e ciki, kada ki kai kukan Sa wajen bayin Sa, kuma ki kasance mai kiyaye iyakokin Sa, ki Tsare ganinki, jinki daga haramun kuma ki kiyaye al'aurarki, ki kare mutuncin kanki kuma kada ki tozartar da tarbiyyar da su Abba da Umma s**a ba ki, kada ki aikata abin da za su yi da-na-sanin zuwanki duniya, Sannan kada ki aikata abin da zai zama abin gorantawa ga Qannenki, 'yaƴanki da dukkan wanda yake da alaqa ta jini da ke! Ki bar tarihi mai kyau ko don gaba, kuma ki ji tsoron Allah ki dinga dubin abin da k**e aikatawa don gobe.
Da yawa daga cikin 'Yan mata kamilallu sun rasa kimarsu, inda suke tunanin mai yiyuwa sanya wadataccen hijabi da Niqabi ne ya jawo masu jinkirin aure, sai s**a koma yin shiga irin ta tsiraici da bayyana adonsu wai da sunan samun mijin aure. 'Yar uwa Wallahi arhar ta yi yawa, meyasa sai kin tallata kanki za ki samu mai aure, kin ta6a ganin wani abu mai daraja ana tallata shi, duk wani abu mai daraja rufe shi ake kuma a adana shi a mafi dacewar guri, shin a tunaninki tsinuwar Allah da ta malā'iku su za su yi maki jagoranci wajen neman mijin aure, ki watsar da wannan tunanin 'yar uwa. Ki killace kanki, ki ďauki kanki kamar sarauniya, Allah Masani ne a kan halin da k**e ciki, kuma Shi zai turo maki miji ďan asali mumini, domin su mata masu tarbiyya na maza masu tarbiyya ne, su kuwa lalatattu sai lalatattu irinsu.
Mata nawane s**a yi auren amma har yanzu ba su shaida daďinsa ba? Nawa ne s**a rabu da iyayensu s**a je gidan wani amma ya dinga azabtar da su, wata ma sai ta gwammace dama ba a haife ta ba. Ashe kun ga kenan yin auren ba shi ke tabbatar da natsuwa ba, sai an bi hanyar da Allahu da ManzonSa s**a tsara.
Ku kuma masu tsangwamar irin waďannan matan da cewa sun qi yin aure, ku ji tsoron Allah ku daina, ku sani kowa akwai irin Qaddararsa a rayuwa. Sai ku ji kawai an zauna ana firar wance ga Qannenta sun yi aure har da yara, amma ita ta tsaya sai.... Wallahi ku sani! Tafi kowa son ta yi auren, kuma iyayenta ma sun kosa su rabu da ita. To amma ya za su yi tunda haka Allah Ya tsara mata?
Allah ka ɗora mu akan abinda kake so kuma ka yarda dashi