
18/07/2025
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da kashi 85 cikin 100 na alkawuran da ta dauka wa al’ummar jihar, inda ya rage kashi 15 cikin 100 yayin da yake shiga shekara ta biyu na wa’adin mulkinsa na farko.
Daily Trust ta rawaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke rantsar da sabon Shugaban Ma’aikata na Jihar, Dr Sulaiman Wali Sani; Darakta Janar na Hukumar Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Sani Muhammad (mai ritaya), da kuma Masu Ba da Shawara na Musamman guda 11, a ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa wannan nasara ta kasance sak**akon tantancewar da aka yi kan ayyukan gwamnatinsa a cikin shekaru biyu da s**a gabata.
“Na yi farin ciki cewa makon da ya gabata lokacin da na duba wuraren da muka samu kuri’a a zabe, duk alkawuran da muka yi wa jama’a, a cikin shekaru biyu mun aiwatar da kashi 85 cikin 100. Don haka, yanzu ya rage mana kashi 15% kawai da za mu aiwatar cikin shekaru biyu masu zuwa, insha Allah,” in ji shi.
“Mun gabatar da wannan batu a gaban Majalisar Zartaswa ta Jihar. Mun dubi yadda abubuwa ke gudana kuma muna da shekaru biyu a gaba. Don haka za mu duba hanyoyin da za mu tabbatar da cika wannan kashi 15%,” inji shi.
Gwamna Yusuf ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo sababbin tsare-tsare da shirye-shirye domin kara tasiri a rayuwar al’ummar jihar Kano.
“Muna kawo sababbin shirye-shirye da ayyuka wadanda, da yardar Allah (SWT), za su ci gaba da inganta rayuwar al’ummar jihar. Kuma ba za mu iya yin hakan mu kadai ba; dole ne mu hada kai da ku duka,” in ji shi.