First Aid Group Of Fityanul Islam Borno Media Team

  • Home
  • First Aid Group Of Fityanul Islam Borno Media Team

First Aid Group Of Fityanul Islam Borno Media Team F. A. G. OF F. I. N

TA’AZIYYA CIKIN RUBUTUDa alhini da juyayi, muna isar da sakon ta’aziyya a madadin Shugaban Rundunar ‘Yan Agajin Kungiyar...
18/07/2025

TA’AZIYYA CIKIN RUBUTU

Da alhini da juyayi, muna isar da sakon ta’aziyya a madadin Shugaban Rundunar ‘Yan Agajin Kungiyar Fityanul Islam Reshen Jihar Borno, Brig. Gen. Muhammad Abdullahi Karaji, tare da dukkan membobin kungiyar a jihar.

Muna miƙa ta’aziyya ta musamman ga National D.G Alh. Muhammad Sani Suleiman (Kaduna Commander in Chief FAG) bisa rasuwar 😭 Malama Aisha Muhammad, mahaifiyar mai dakinsa.

Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta mata.

✍️ Rabiu Babayo

Yakubu Mustafa Grema
FAG/FIN/BORNO/MEDIA/TEAM_17/07/2025

ZIYARA CIKIN HOTUNAKungiyar agajin Gamayyar Musulci (JIFAO) FCT ta kai ziyara ga Hajiya Rahama Sheikh Abdulmajeed, mai t...
13/07/2025

ZIYARA CIKIN HOTUNA

Kungiyar agajin Gamayyar Musulci (JIFAO) FCT ta kai ziyara ga Hajiya Rahama Sheikh Abdulmajeed, mai taimaka wa shugaban ƙasa a kan harkokin Media da Rediyo, domin taya ta murnar dawowa daga Makkah.

Ta yaba da ziyarar, ta ba da shawarwari masu amfani, tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da jihohi da su hada kai tare da tallafa wa kungiyoyin agaji wajen gudanar da ayyukan addini da jin ƙai.

Ta kuma tabbatar da cewa kofarta a bude take don haɗin gwiwa.

Muna addu’ar Allah Ya sa zaman lafiya ya ɗore a ƙasarmu. Ameen.

💻 Media & Publicity
Office of the National Parade & Decoration, FAG 12/07/2025

TA’AZIYYAZuwa Ga Zawiyyar Sheikh Abagoni Maiduguri.A madadin Shugaban Fityanul Islam reshen Jihar Borno, Prof. Sheikh Ab...
12/07/2025

TA’AZIYYA

Zuwa Ga Zawiyyar Sheikh Abagoni Maiduguri.

A madadin Shugaban Fityanul Islam reshen Jihar Borno, Prof. Sheikh Abba Saleh Ahmad Abulfathi, da Shugaban Rundunar ‘Yan Agaji, Brig. Gen. Muhammad Abdullahi Karaji,_ tare da daukacin membobin kungiyar — muna miƙa ta’aziyya ga Dr. Abba Sani Abagoni Secretary Kungiyar Fityanul Islam na jihar Borno bisa rasuwar😭 yar uwarsa tare iyalan marigayiya Sayyada Asabe, 'yar Sheikh Abagoni.

Allah Ya gafarta mata, Ya jaddada rahama a gareta, Ya sada ta da Manzon Allah (S.A.W) a Firdaus.

✍️ Rabiu Babayo

JANA'IZA CIKIN HOTUNADubban Al'ummar Musulmi s**a halarci jana’izar😭 Sayyada Asabe, ‘yar Sheikh Abagoni, a Zawiyar Sheik...
12/07/2025

JANA'IZA CIKIN HOTUNA

Dubban Al'ummar Musulmi s**a halarci jana’izar😭 Sayyada Asabe, ‘yar Sheikh Abagoni, a Zawiyar Sheikh Abagoni, Hausari, Maiduguri. Al’ummar Musulmi da dama sun halarta, suna roƙon Allah ya jaddada rahama a gareta.

Allah ya gafarta mata, ya sada su da Manzon Allah (S.A.W).

✍️ Rabiu Babayo

BARKA DA SABON MUƘAMI!A madadin dukkan membobin Borno Media Team na yan agajin Fityanul Islam muna taya Lt. Coln. Abubak...
10/07/2025

BARKA DA SABON MUƘAMI!

A madadin dukkan membobin Borno Media Team na yan agajin Fityanul Islam muna taya Lt. Coln. Abubakar H. Surrinbai murna bisa samun sabon muƙamin Assistant Deputy Director (Training Officer), FAG, Fityanul Islam, Jihar Nasarawa.

Wannan karin girma alama ce ta kwazonka, biyayya, da jajircewarka wajen hidima ga al’umma da kuma ci gaban ƙungiyarmu. Muna fatan Allah Ya ba ka ikon gudanar da wannan nauyi cikin nasara da tawali’u, Ya kuma sa muƙamin ya zama alheri gare ka da al’umma gaba ɗaya.

Muna alfahari da kai!

— Tare da fatan alheri daga:
Tawagar Borno Media Team, First Aid Group Fityanul Islam Reshen Jihar Borno.

✍️ Rabiu Babayo

🏆 GASAR PARADE A BIKIN DAURIN AUREA yau, 05/07/2025, an gudanar da gasar fareti a bikin daurin aure na ɗan uwammu Capt. ...
05/07/2025

🏆 GASAR PARADE A BIKIN DAURIN AURE

A yau, 05/07/2025, an gudanar da gasar fareti a bikin daurin aure na ɗan uwammu Capt. Abubakar Sadiq (Mai Akuya) a Anguwar Moranti. Gasar ta gudana ne ƙarƙashin jagorancin Coln. Muhammad Alh. Muhammad, Borno State Deputy Director Admin FAG.

📊 SAKAMAKO:

🥇 MMC A – 96.0% (Na ɗaya, kofi + ₦5,000)
🥈 Mafa – 93.0% (Na biyu, ₦3,000)
🥉 MMC B – 80.6% (Na uku, ₦2,000)
4️⃣ Konduga – 65.4% (Ba a samu kyauta ba)

Muna taya Karamar Hukumar MMC LGA murna bisa lashe wannan gasar fareti, tare da fatan alheri ga shugaban karamar hukumar, Maj. Musa Usman Allah ya qara hazaƙa.

Muna kuma taya ma’auratan murna, muna fatan Allah ya basu zaman lafiya da albarka.

✍️ Rabiu Babayo

Yakubu Mustafa Grema
FAG/FIN/BORNO/MEDIA/TEAM – 05/07/2025

TUNATARWAAzumin Tasu’a da AshuraKungiyar Fityanul Islam of Nigeria tana tunatar da daukacin al’ummar Musulmi a fadin dun...
03/07/2025

TUNATARWA

Azumin Tasu’a da Ashura

Kungiyar Fityanul Islam of Nigeria tana tunatar da daukacin al’ummar Musulmi a fadin duniya, musamman ‘yan agaji da mambobin Kungiyar Fityanul Islam, muhimmancin yin azumin Tasu’a (Juma’a, 4 July, 2025 – 9 Muharram 1447H) da Ashura (Asabar, 5 July, 2025 – 10 Muharram 1447H).

Manzon Allah Saw ya azumci Ashura kuma ya umarci Musulmi su azumce ta. Daga baya ya ce:

“Idan na rayu zuwa shekara mai zuwa, zan azumci ranar tara 9 (Tasu’a) ma.”(Muslim

Saboda haka Sunnah ce Musulmi su azumci Tasu’a da Ashura, ko ku azumci Ashura kawai idan ba za ku iya duka biu ba.

Muna kira ga Musulmi su yi kokari su azumci wadannan ranaku, tare da addu’a domin zaman lafiya da cigaban Musulunci.

Allah Ya karbi ibadunmu. Amin.

✍️ Rabiu Babayo

CONGRATULATIONS!Bismillahir-Rahmanir-Rahim.Da farin ciki marar misaltuwa, muna mika sakon taya murna a madadin Tawagar B...
30/06/2025

CONGRATULATIONS!

Bismillahir-Rahmanir-Rahim.

Da farin ciki marar misaltuwa, muna mika sakon taya murna a madadin Tawagar Borno Media Team. Muna taya abokan aikinmu na Social Media Team, Nasarawa State, murnar samun Takardar Shaida ta Kwarewa daga Kungiyar First Aid Group of Fityanul Islam of Nigeria, Nasarawa State, a taron da aka gudanar a Garin Gora, Karshi Development Area, Karu.

Musamman muna taya murna ga jagoranku, Abubakar H. Surrinbai Nasarawa, fatan Allah ya kara masa nasara. Allah ya daukaka Fityanul Islam of Nigeria.

✍️ A madadin
Borno Media Team

📝 Rabiu Babayo

Alhamdulillahi,Mahajjatan Jihar Borno suna shirin dawowa gida Nigeria daga Kasar Mai Tsarki. Yayin da ’yan Agajin FITYAN...
27/06/2025

Alhamdulillahi,

Mahajjatan Jihar Borno suna shirin dawowa gida Nigeria daga Kasar Mai Tsarki. Yayin da ’yan Agajin FITYANUL ISLAM RESHEN JIHAR BORNO za su tafi tarbar su a Filin Jirgin Sama na Maiduguri. Muna roƙon Allah Ya tabbatar da saukarsu lafiya, Ya karɓi ibadarsu, kuma Ya saka masu da alheri. Amin.

✍️ Rabiu Babayo

BARKA DA SABON SHEKARAR MUSULUNCI
27/06/2025

BARKA DA SABON SHEKARAR MUSULUNCI

SANARWA PARADE COMPETITIONIna mai farin cikin sanar da dukkan membobin kungiyar Fityanul Islam cewa, a madadin ɗan uwanm...
27/06/2025

SANARWA PARADE COMPETITION

Ina mai farin cikin sanar da dukkan membobin kungiyar Fityanul Islam cewa, a madadin ɗan uwanmu Capt. Abubakar Sadiq (Mai Akuya), ɗaya daga cikin shugabannin Agajin Fityanul Islam na Karamar Hukumar Konduga, muna gayyatar dukkan membobin kungiyar zuwa bikin daurin aurensa kamar haka:

📍 Anguwa: Moranti
📅 Rana: Asabar
🗓️ Kwanan wata: 05/07/2025
🕘 Daurin aure: 9:00 na safe
🕙 Parade Competition: 10:00 na safe

Muna roƙon duk membobi su halarta cikin tsari da sanya kayan uniform na kungiya domin taya ɗan uwanmu murnar wannan babban lokaci.

Bayan daurin aure, za a gudanar da gasar fareti tsakanin kananan hukumomin da s**a halarta, insha Allah.

Allah ya sanya alheri, ya ba ma’auratan zaman lafiya da albarka. 🤲 Amin.

✍️ Rabiu Babayo

26/06/2025

Address


Telephone

+2348140957032

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when First Aid Group Of Fityanul Islam Borno Media Team posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to First Aid Group Of Fityanul Islam Borno Media Team:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share