
07/10/2025
Sheikh Bala Lau ya kai ziyarar ta’ziya ga Lamidon Adamawa
Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Ash-Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, ya jagoranci wata ziyarar ta’ziya zuwa ga mai martaba Lamidon Adamawa, Alhaji Dr. Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa, sakamakon rasuwar ɗan’uwansa Marigayi Ahmed Aliyu Mustapha, tsohon shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS).
Sheikh Bala Lau ya samu rakiyar Shugaban JIBWIS na Jihar Adamawa, Alhaji Sahabo Magaji, tare da wasu manyan jami’ai da ‘yan majalisar ƙungiyar. Shehin malamin ya kai ziyarar ne a Fadar Lamidon dake Yola, inda aka gabatar da addu’o’i na musamman ga marigayin da rahama, ya gafarta masa, ya kuma ba iyalansa da masarautar Adamawa hakuri da juriya.
A yayin jawabin sa, Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa mutuwa wata gagarumar jarabawa ce ga dukkan ɗan Adam, wadda ke tunatar da mu game makomar mu. Ya ce:
“Rayuwa tana tafiya da lokaci, kuma kowa zai dandani mutuwa. Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu rayu cikin bautan ubangiji, mu yi kokari matuka wajen kyautata goben mu.”
A nasa bangaren, Lamidon Adamawa, Alhaji Dr. Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa, ya nuna matuƙar farin ciki da wannan ziyara ta girmamawa da ta’aziyya daga shugaban JIBWIS da tawagarsa. Ya gode musu bisa irin goyon baya da addu’o’in da suke bayarwa ga masarautarsa da kuma ƙasa baki ɗaya.
Lamidon ya jaddada cewa Sheikh Bala Lau da JIBWIS suna taka muhimmiyar rawa wajen gyaran tarbiyya, inganta fahimtar addini, da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Ya yi fatan Allah ya ba su ƙarin ikon ci gaba da wannan aiki na alheri.
Madogara : Jibwis Nigeria
Bajama Multimedia