08/08/2025
“YADDA ƳAN SANDA S**A K**A NI, BA TARE DA SANIN CEWAR NINE KWAMISHINAN ƳAN SANDA BA” – MD ABUBAKAR
“A lokacin da nake Kwamishinan Ƴan Sanda a jihar Lagos, bana wasa da aiki — musamman ranar Asabar. Ko da yake ayyuka na suna farawa ne daga karfe 10 na safe, wannan rana na tashi tun 6 na safe don in kai ziyara ba tare da sanarwa ba.
Na hau motata Jeep na nufi ofis, amma sai na yanke shawarar yin ‘yin ziyarar ba-zata’ ga wasu 'yan sanda a kan hanya – domin in ga irin yadda suke gudanar da aikinsu.
A wani shingen bincike “checkpoint” dake titin Herbert Macaulay, wasu matasan 'yan sanda s**a tsaida ni. Wani karamin dan sanda (constable) ya kalle ni yace:
> "Kai saurayi, ina zaka ne da motar mahaifinka?"
Ya bukaci takardun motar da shaidar lasisin tuƙi. Na ce masa sunana Mohammed. Yace dole sai na nuna ID card. Na ce masa, to ya fara nuna mini nasa. Bai da ID card, don haka sai ya kira sergeant dinsu.
Shi ma sergeant din ya bukaci ID card dina, na ce masa ya nuna mini nasa kafin nawa. Ganin bana jin tsoro ko nuna daraja, sai s**a ce mu tafi ofishin ‘yan sanda na Yaba (Panti) domin “gano ko ni wanene”.
Muna isa station – babu parking sai a wajen DPO. Na ajiye motata a can, constable din ya fusata yace: “Wannan wajen parking din DPO ne fa!” Ko uffan ban ce masa ba.
Bayan mun shiga ciki, sai s**a kaini wurin wani ASP (Assistant Superintendent of Police) wanda ke sanye da gajeren wando 'shorts'!. Yace na shigo, na ki, nace masa ba zai yiwu ya tuhumeni cikin kayan gida ba. Yayi fushi ya jawo ni ciki da ƙarfi – nima ina jan shi. Da ya duba fuskata da kyau sai ya fara zare ido…
A gefe guda, wani tsoho da ke ofishin ya leƙa ofishin DPO don duba hoton shugabannin rundunar Ƴan sanda dake jikin bango. Da ya tabbatar cewa ni ne, sai kawai ya tsallake taga ya gudu!
Sergeant da ya kawo ni ya kasa gane me ke faruwa, har sai da wani Ɗan sanda ya matso kusa da kunnensa, ya ce masa: “Kai, CP ne wannan fa!”.