Solacebase Hausa

Solacebase Hausa Shafin jaridar SolaceBase Hausa

01/08/2025

"Da ace Ali Sani Madakin Gini daga NNPP yace ya fita ba Kwankwasiyya ba, da ya ga yadda zamu yi wasan kura da shi," in ji shugaban jam'iyyar NNPP, Hashimu Sulaiman Dungurawa.

Ku biyo mu gobe da misalin karfe 8 na dare domin jin cikakkiyar hirar.

Ma’aikatan Jiyya, Ungozoma Sun Fara Yajin Aikin Gargadi Na Kwana Bakwai
30/07/2025

Ma’aikatan Jiyya, Ungozoma Sun Fara Yajin Aikin Gargadi Na Kwana Bakwai

Kungiayar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa – Sashen kula da lafiya ta tarayya (NANNM-FHI) sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai a yau, duk da rokon da gwamnatin tarayya ta yi. Kungiyar ta ce matakin wanda ya fara da tsakar dare, ya zama dole ne biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 15 ...

Shugaban Hukumar Zabe ta Bauchi Ya rasu
30/07/2025

Shugaban Hukumar Zabe ta Bauchi Ya rasu

Shugaban Hukumar Zabe ta Bauchi Ya ras Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi, BASIEC, Alhaji Ahmed Mak**a Hardawa, ya rasu. Mukhtar Gidado, mai baiwa gwamna Bala Mohammed shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ne ya tabbatar da rasuwarsa a wata sanarw...

Masu ɗauke da ciwon Hanta a Kano sun haura mutum Miliyan 1- Kwamishinan Lafiya
28/07/2025

Masu ɗauke da ciwon Hanta a Kano sun haura mutum Miliyan 1- Kwamishinan Lafiya

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin kawar da cutar mai karya Garkuwar jiki a Najeriya da nufin hana kamuwa da cutar ta HIV da ciwon Hanta na matakin B da kuma cutar Syphilis wadda ake dauka sak**akon saduwa da kuma iyaye zuwa ga jariransu. Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Abubakar Labaran Yu...

Hukumar yaƙi da cin Hanci da rashawa ta Kano ta sanar da sabon shugabanta na riƙo
28/07/2025

Hukumar yaƙi da cin Hanci da rashawa ta Kano ta sanar da sabon shugabanta na riƙo

Hukumar karbar korafi da yaki da cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano PCACC, ta sanar da nadin Barista Zaharaddeen H. Kofar Mata, a matsayin shugabanta riko. Nadin nasa ya fara aiki nan take, an bayyana shi ne a cikin wata sanarwar hukumar ta fitar yau Litinin mai dauke da sa hannun babban jami’in t...

SDP ta ta kori El-Rufai bisa zarginsa da yin rijistar bogi
28/07/2025

SDP ta ta kori El-Rufai bisa zarginsa da yin rijistar bogi

Jam’iyyar SDP ta kori tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, inda ta bayyana cewa ba zai iya shiga jam’iyyar ba a kowane matsayi na tsawon shekaru 30 masu zuwa. A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran SDP na ƙasa Araba Aiyenigba ya fitar a Abuja, jam'iyyar ta ce, El-Rufai bai taɓ...

Tawagar Super Falcons Sun Iso Najeriya
28/07/2025

Tawagar Super Falcons Sun Iso Najeriya

Tawagar Super Falcons ta Najeriya sun sauka a Najeriya daga kasar Morocco inda s**a lashe gasar cin kofin Afrika na mata karo na 10. Tawagar ta isa filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a cikin wani jirgin da misalin karfe 2:26 na rana. Tawagar ta sami gagarumin tarba daga....

Yobe: An cafke matasa 60 da ake zargi da shan miyagun Ƙwayoyi
24/07/2025

Yobe: An cafke matasa 60 da ake zargi da shan miyagun Ƙwayoyi

Akalla mutane 60 aka cafke wadanda ake zarginsu da hannu a wani samame na hadin gwiwa da aka yi a Damaturu babban birnin jihar Yobe. Babban jami’in gwamnatin jihar kan hana shan miyagun kwayoyi, Malam Saidu Jakusko, ne ya bayyana hakan a yau Alhamis yayin da ya ke zanta wa da manema labarai a birn...

Neja: Cutar Kwalara ta kashe mutane 12 tare da jikkata wasu fiye da 230
24/07/2025

Neja: Cutar Kwalara ta kashe mutane 12 tare da jikkata wasu fiye da 230

Ɓarkewar cutar Amai da Gudawa watau kwalara a jihar Neja ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da 230 a wasu ƙananan hukumomin jihar. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa an fara gano bullar cutar ne a ranar Lahadi a karamar hukumar Shiroro. Ya zuwa y...

Kotu ta ɗage sauraron shari’ar zargin almundahanar fiye da Biliyan 1 da ake yi wa shugaban KANSIEC
22/07/2025

Kotu ta ɗage sauraron shari’ar zargin almundahanar fiye da Biliyan 1 da ake yi wa shugaban KANSIEC

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ɗage ƙarar da aka shigar kan Shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kano, KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, da Sakataren Hukumar Malam Anas Muhammed Mustapha, da Malam Ado Garba, Mataimakin Darakta a Sashen harkokin kuɗi na hukumar...

Tsoffin ƴan sanda sun yi zanga-zanga a gaban zauren majalisar tarayya
22/07/2025

Tsoffin ƴan sanda sun yi zanga-zanga a gaban zauren majalisar tarayya

Duk da ruwan sama da aka yi, a yau Litinin, jami’an ‘yan sanda da s**a yi ritaya sun gudanar da zanga-zangar lumana a babbar kofar majalisar tarayya da ke Abuja, inda s**a bukaci a cire su daga tsarin bayar da gudunmawar fansho CPS, wanda s**a bayyana a matsayin cin zali da rashin adalci. Zanga-...

Kotu ta hana EFCC k**a wani ɗan Kasuwa kan zargin damfarar kusan Dala Miliyan 2
22/07/2025

Kotu ta hana EFCC k**a wani ɗan Kasuwa kan zargin damfarar kusan Dala Miliyan 2

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta bayar da umarnin wucin gadi na hana hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziƙin kasa zagon ƙasa EFCC k**awa ko musguna wa wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya mazaunin Dubai, Alhaji Rabiu Auwalu Tijjani, wanda hukumar ta bayyana cewa ta na nemansa bisa...

Address

Murtala Muhammad Way
Kano
234001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Solacebase Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Solacebase Hausa:

Share