Tauraruwa

Tauraruwa Zaku iya Aiko mana da Rahotanni da labarai kai tsaye. domin tallata hajarka zaka iya tuntubarmu akan lambar waya kamar haka 09060808585

Murtala Zhang Kenan, Ɗan Jaridar Kasar Sin da ya ƙware a magana da Harshen Hausa. Zhang Weiwei, wanda aka fi sani da Mur...
27/08/2025

Murtala Zhang Kenan, Ɗan Jaridar Kasar Sin da ya ƙware a magana da Harshen Hausa.

Zhang Weiwei, wanda aka fi sani da Murtala, ɗan jaridar kasar Sin da ya yi karatun Hausa a Jami’ar Beijing Foreign Studies, ya shahara a Najeriya saboda kwarewarsa wajen iya harshen Hausa. A matsayinsa na wakilin China Radio International, ya shafe kusan shekaru kimanin 6 a Najeriya inda ya gudanar da hira da fitattun mutane ciki har da Sarkin Kano, tare da nuna kishin al’adu da harshen Hausa.

Haka kuma, Murtala Zhang daga birnin Sin ya burge jama’a da iyawar Hausa k**ar jakin Kano cikin shigar gargajiya, inda ya taya Hausawa murnar Ranar Hausa ta Duniya, lamarin da ya kara jawo sha’awa da yabon muhimmancin harshen Hausa a idon duniya.

Matashi a Kaduna Ya Ƙirƙiri ɗan ƙaramin Jirgin Sama Mara Matuki Don Inganta harkar Noma. Shamsudeen Jibril, matashi ɗan ...
27/08/2025

Matashi a Kaduna Ya Ƙirƙiri ɗan ƙaramin Jirgin Sama Mara Matuki Don Inganta harkar Noma.

Shamsudeen Jibril, matashi ɗan shekara 25 daga Kaduna, ya ƙirƙiri ƙaramin jirgin sama mara matuki (Unmanned Aerial Vehicle UAV) da nufin taimaka wa manoma wajen inganta harkokin gona, musamman wajen yin feshin maganin kashe kwari a gonaki, abin da masana s**a bayyana a matsayin babbar gudummawa ga ci gaban fasaha da noma a Najeriya.

Amurka Ta Daure Sarki Oba Joseph Oloyede, Apetumodu na Ipetumodu, Bisa Laifin Wawure Kuɗin COVID-19Kotun Amurka ta daure...
27/08/2025

Amurka Ta Daure Sarki Oba Joseph Oloyede, Apetumodu na Ipetumodu, Bisa Laifin Wawure Kuɗin COVID-19

Kotun Amurka ta daure Oba Joseph Oloyede, Apetumodu na Ipetumodu a jihar Osun, bisa samun sa da laifin karkatar da kuɗaɗen tallafin COVID-19 da s**a kai kimanin Naira biliyan 6.4. Kotun ta yanke masa hukuncin shekaru huɗu a gidan yari, tare da kwace wasu daga cikin kadarorinsa.

Kotun Amurka ta k**a Basaraken Ipetumodu dake Ogun, da laifin karkatar da kudi Naira Biliyan 6.4Kotun Amurka ta tabbatar...
27/08/2025

Kotun Amurka ta k**a Basaraken Ipetumodu dake Ogun, da laifin karkatar da kudi Naira Biliyan 6.4

Kotun Amurka ta tabbatar da laifin Oba Joseph Oloyede, Apetumodu na Ipetumodu, wanda shi ne sarkin gargajiya na garin Ipetumodu da ke Ƙaramar Hukumar Ife North, Jihar Osun, bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da s**a kai Naira biliyan 6.4. Kotun ta kuma kwace masa kadarorinsa tare da yanke masa hukuncin fiye da shekaru huɗu a gidan yari.

Isra’ilawa Sun Yi Zanga-Zanga Kan Bukatar Tsagaita Wuta a GazaDubban Isra’ilawa sun fito kan tituna a manyan biranen ƙas...
27/08/2025

Isra’ilawa Sun Yi Zanga-Zanga Kan Bukatar Tsagaita Wuta a Gaza

Dubban Isra’ilawa sun fito kan tituna a manyan biranen ƙasar, inda s**a toshe manyan hanyoyi tare da ƙona tayoyi, suna kira ga gwamnatin Netanyahu da ta tsagaita wuta a Gaza. Masu zanga-zangar sun kuma bukaci a gudanar da musayar fursunoni da aka k**a tsakanin bangarorin biyu. Wannan lamari ya nuna ƙara ƙarfafa matsin lamba ga gwamnati a yayin da rikicin Gaza ke ci gaba da jawo hankalin duniya.

Hoto: Aljazeerah

An yiwa Mutane Biyu Bula 76 a Bainar Jama’a Bisa Zargin Hulɗar Jima’i da Juna a ƙasar Indonesiya. Hukumomin shari’ar Mus...
27/08/2025

An yiwa Mutane Biyu Bula 76 a Bainar Jama’a Bisa Zargin Hulɗar Jima’i da Juna a ƙasar Indonesiya.

Hukumomin shari’ar Musulunci a lardin Aceh na Indonesia sun yi wa wasu maza biyu bulala sau 76 a bainar jama’a bayan an same su da laifin hulɗar jima’i da juna, lamarin da aka gudanar a Banda Aceh.

Hukumar ta bayyana cewa an k**a su ne a watan Afrilu a bayan gidan wanka na jama’a, inda aka yi musu hukuncin. Da farko an yanke musu bulala 80, amma an rage hudu saboda watanni huɗu da s**a shafe a tsare.

Kyawawan Gine-ginen Gargajiya na na ƙasar Zimbabwe 🇿🇼Hotunan kyawawan gine-gine na gargajiya mai tsari na Zimbabwe, wand...
27/08/2025

Kyawawan Gine-ginen Gargajiya na na ƙasar Zimbabwe 🇿🇼

Hotunan kyawawan gine-gine na gargajiya mai tsari na Zimbabwe, wanda aka yi da ƙasa da laka, aka yi masa ado da launuka masu ban sha’awa da zanen geometric.

Ba Za Mu Dawwama Muna Faranta Wa Kasashen Yamma Rai muna ɓatawa namu ba - Ibrahim Traore. Shugaban ƙasar Burkina Faso, C...
27/08/2025

Ba Za Mu Dawwama Muna Faranta Wa Kasashen Yamma Rai muna ɓatawa namu ba - Ibrahim Traore.

Shugaban ƙasar Burkina Faso, Captain Ibrahim Traoré, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta dawwama tana yin abin da zai faranta wa kasashen Yamma rai ba, inda ya jaddada cewa manufarsu ita ce kare kansu da kuma bautawa ƙasarsu ta Burkina Faso.

Burkina Faso da Mali Ba su Tura Wakilai zuwa Taron Sojojin Nahiyar ba da Najeriya Ta Shirya. Kasashen Burkina Faso da Ma...
26/08/2025

Burkina Faso da Mali Ba su Tura Wakilai zuwa Taron Sojojin Nahiyar ba da Najeriya Ta Shirya.

Kasashen Burkina Faso da Mali ba su tura wakilai ba zuwa wani babban taron hafsoshin tsaro na nahiyar da Najeriya ta shirya a Abuja ranar Litinin, alamar ƙara dagula dangantaka tsakaninsu da makwabtan su bayan janyewar su daga ECOWAS a watan Janairu 2025, yayin da su da Nijar s**a ƙulla haɗin gwiwa a karkashin Alliance of Sahel States (AES); a yayin da Najeriya ta yi kira ga sabuwar tsari na tsaron Afirka da zai dogara da haɗin gwiwar ƙasashen nahiyar.

Hukumar ICPC Ta Ƙwato kudi Sama da Naira Biliyan 1 a hannun Jami’in Gwamnatin Kano Abdullahi Rogo. Hukumar Yaƙi da Cin H...
26/08/2025

Hukumar ICPC Ta Ƙwato kudi Sama da Naira Biliyan 1 a hannun Jami’in Gwamnatin Kano Abdullahi Rogo.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta tabbatar da ƙwato sama da naira biliyan ɗaya daga hannun Darakta Janar na Sashen Karɓar Baƙi a Fadar Gwamnatin Kano, Abdullahi Rogo. Wannan na zuwa ne duk da cewa gwamnatin jihar ta yi watsi da zargin badaƙalar bacewar kuɗaɗen, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Allah ya yiwa tsohon limamin masallacin Harami na Makkah Sheikh Abdul Wakeel ibn She...
26/08/2025

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Allah ya yiwa tsohon limamin masallacin Harami na Makkah Sheikh Abdul Wakeel ibn Sheikh Abdul Haq al-Hashimi rasuwa.

Sheikh Abdul Wakeel ibn Sheikh Abdul Haq al-Hashimi, fitaccen malamin Hadisi kuma tsohon Mu’azzin da Imam a Masallacin Harami na Makkah, ya rasu a safiyar yau, inda aka yi masa sallar jana’iza bayan sallar Asuba a Masallacin Harami sannan aka binne shi a birnin Makkah, lamarin da ya girgiza al’ummar musulmi tare da barin babban gibi ga dalibai da masu amfana daga iliminsa.

Rundunar Sojan Ruwa Ta Tarayya Ta Bankado Haramtacciyar Matatar Mai a Jihar Delta. A ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, 2...
26/08/2025

Rundunar Sojan Ruwa Ta Tarayya Ta Bankado Haramtacciyar Matatar Mai a Jihar Delta.

A ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, 2025, jirgin ruwan rundunar sojan ruwa na Najeriya NNS DELTA ta gano tare da lalata wata haramtacciyar ma’adinin mai da ke da tankin ajiya a ƙarƙashin ƙasa mai ɗauke da tarin haramtattun kayayyakin mai a Asinsen Creek, ƙaramar hukumar Warri South-West, Jihar Delta.

Address

Kano

Telephone

+2349060808585

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tauraruwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share