Jafar sa'ad

Jafar sa'ad alhamdulillah ala kulli halin

Hausa novel writer........✏✏✏

📝📝📝📝📝
📚📚📚📚
📖📖📖
WhatsApp number 👉09124400024
(6)

MIJIN HANIFA___PART__5_______________©®"Gaba daya ya bude bottles din ya 'daukobelt ya nannade a hanunsa ya kura mataido...
29/10/2025

MIJIN HANIFA___
PART__5___
____________©®"Gaba daya ya bude bottles din ya 'dauko
belt ya nannade a hanunsa ya kura mata
ido, wani mugun tsananta yakeji.
KE! ya daka mata tsawa, a razane ta
'd**o idonta da s**ayi raurau tana
dubansa.
"Na miki k**a da wanda zaki raina?
"Kasa cewa komai tayi sai 'barin da jikinta
keyi.
"Am asking you, you piece of trash.
"A hankali ta soma girgiza kai,
"Murmushi yayi gamida 'dauko goran
ruwan sanyi ya shiga juye mata a jikinta
ga shi dama lokacin sanyi ake, take ta
shiga 'bari ha'de da kwalla ihu, wani
wawan mari ya 'daura mata yace "shut
up! Idan kika sake kuka plus goran ruwan
sanyi daya dan haka gwarama kiyi shiru.
"Kuka take tana 'barin sanyi amma
Haidar ko a jikinsa babu alamun tausayi a
tare da shi. Bayan wann azaba da ya
gama yima Hanifa yana ji yana gani tana
rawan 'dari yace oya tidy this mess. Haka
ta dauko mopa ta shiga goge wajen ga
sanyin ac gana gari ga kuma na ruwan
jikinta. Ta gama gyara wajen tsaf sann ya
fito da kayan wardrobe dinsa yace she
should tidy it. Tana gani ya dauki car key
ya fice gamida kulleta cikin 'dakin....
"Tsugunawa tayi a wajen tana rera kuka,
wani mugun tsanan yaHaidar na dada
fizganta.
"Koda mamy ta tambayi su Shema Hanifa
sai ce mata s**ayi tana sashen inna dan
haka mamy bata kuma bin ta kansu ba
dan tasan wataran s**an kwana wajen
kakar tasu mussaman Hanifa yar lele....Yana fita bai zarce ko ina ba sai gidan
abokinsa Saif,,
" Haidar sojan ruwa yau 'batan kai kayi
naganka a gidanmu, cewan Saif matashi
kyakyawa maiji da ku'di da class.
"Ka fara halin naka ko wllhi kasa tsiya zan
juya. Haidar ya fadi sanda yake kokarin
zama bisa sofa.
"Hannu Saif ya mika masa s**a gaisa
kafin yace "mutumina nasanka ne ba'a
ganinka saida dalili idan ba new series
nace maka na samu ba bazan ganka ba,
anyway yaushe kazo.
"Last week and gobe zan wuce insha
Allah.
"Haba dai so soon.
"Wllhi nayi receiving urgent call frm my
boss 'dazun nan.....
"Dariya Saif ya kyalkyale kana yace kace
in law dinka mana....
"Mtsw don't even start ko na rasa mata ai
bazan auri Lateefa ba kawai dai tana
'bata lokacinta ne. Toh wai ni yaushema
nakeda lokacin wasu mata, I don't think
suna agenda dina. Kawai so nake nayi
kusa da Dad dinta coz am spying on him.
"Saif ya tsare Haidar da ido sann yace "
kasan Allah zai tambayeka idan ka
yaudari yarinyar nan ka duba ka gani fa
how she's dying for you.
"So! Ni nace mata ta soni, beside ni ban
ta'ba ce mata ina sonta ba in the first
place kawai dai tana shirmenta ne.... Saif
zaiyi magana Haidar ya dakatar dashi ta
hanyar 'daga masa hannu yace " kaga
malam let's change the subject if not nayi
tafiyata...
"Murmushi Saif yayi gamida 'dauko masu
ta'din series din da suke bi *24*.
hira sosai s**a sha da Saif har s**ayi
sallahn magrib. 'Karfe 7:00pm on the dot
Haidar ya mi'ke dan tafiya gida tare s**a
fito da Saif s**a nufi gidansu Haidar...
"Tun bayan fitan Haidar Haneefah keta
cin aikin gyara masa wardrobe, saida ta
shirya komai ta maidasu mazauninsu. Ga
wani irin zazza'bi da ya sau'ko mata
lokaci guda, karkarwa take tana numfashi
da kyar abu k**an wasa nan fa taji bata
iya 'daga koda 'dan yatsanta ne. A haka
ta zube a wajen k**an sumemmiya.....
" yana zura key jikin 'kofa gaban shi yayi
mugun fa'duwa sai yanzu ya tuna da
Hanifa, yayi saurin 'karasa bu'de 'kofan
gamida shigewa bedroom. Kwance ya
ganta a 'kasa k**an bata numfashi,
gaba daya ya kidime ya 'karasa ya shiga
jijjigata yana ambato sunanta amma shiru.
"Saif dake zaune a parlor yaji shirun
Haidar yayi yawa ya mike ya nufi 'dakin,
da sauri ya 'karasa ganin Haidar na shafa
ruwa ma Hanifa....
"Lafia friend meya sameta,
"Dauko car key na mu kaita asibiti pls
Saif she's running out of conscious...
"Saif kam tuni yayi mutuwan tsaye yana
bin Haneefa da kallo... _tunda yake bai
ta'ba ganin kyakyawa k**ar Haneefa
ba_......." a fili ya furta "GOD HAVE
MERCY"....
"cikin 'kuluwa Haidar yace dan Allah ka
wuce muje kar ta mace mun a nan.... da
sauri Haidar ya azata bisa kafa'da s**a
nufi asibiti....
"Gaba 'daya sunyi jigum suna tunanin
baby sis dinsu har yanzu bata dawo daga
wajen yaHaidar ba gashi sunji fitar
motarsa ko wani irin azaba yake mata sai
Allah.... suna a haka mamy ta turo 'kofan
'dakin ganinsu tayi gab 'daya k**an
marassa lafia..
"Ku kuma lafia meye kuka zauna haka.
"Ba komai mamy Shema tayi 'karfin halin
fa'din haka....
"Har yanzu Hanifar tana sashen inna
ne..... mamy ta tambaya
"Kame kame s**a soma daidai nan
wayan mamy ya 'dau ruri...
"Daga 'daya 'bangaren Haidar yace
"mamy dama muna asibiti ne.. na kawo
Haneefa batada lafia...
"Haneef kuma ta fa'di sanda take fita
daka 'dakin.... su Shema kuwa kallon
kallo s**a shigayi wa junansu.
"Sady tace bakuji wayan da mamy keyi
ba da yaHaidar take waya kardai yaji ciwo
wa Hany ce.
"Haba dai saidai bata da lafia amma bazai
mata dukan kisa ba Shema ta fadi.
"Hm shiasa nake kwa'ban ta ai,
kwatakwata hany bata jin magana ta faye
tsaurin ido yanzu ga irinta nan, su sojoji
basuda imani ko ka'dan inagama idan
zaka shiga soja sai an

AUREN KWANGILA__PART__73___________©®meeting din daya kawosu.Cikin farin suit mai Jan shirt daga ciki yashirya, yasa nec...
29/10/2025

AUREN KWANGILA__
PART__73___
________©®meeting din daya kawosu.
Cikin farin suit mai Jan shirt daga ciki ya
shirya, yasa necktie ja irin dan guntun
nan, ya taje sumar kanshi daketa walqiya
saboda gyara sannan ya feshe Jikinshi da
turare sannan ya dauki briefcase dinshi
ya fito.
Afalo ya isketa lafe jikin kujera idanunta a
lumshe Amma yasan ba barci take ba,
kallo daya yayimata ya dauke kai cikin
basarwa yana gyara necktie dinshi.
Taji fitowarshi amma taqi bude idanu don
iya shaqa ta shaqa.
"Coffee" yafada in his usual husky voice
Saurin bude idanu tayi tana kallonshi cikin
mammaki, she was like, what the hell?
Shikau babu abinda yadameshi ya duqufa
sai gyara takalminshi yake.
Ganin bata tashi ba yasashi d**owa yana
kallonta, sai yaga itama shi take kallo
fuskarnan har wani ja ja take don 6acin
rai, abinda ta Dade yanaso kenan, ya
6atamata rai.
"Hello??" Yafada yana waving hannu a
fuskarta
"Nace coffee and fried spiced egg"
yafada cikin son qara qular daita
"What? Ni kuku ce?" Tafada cikin
tsananin fishi don yau kwata kwata takasa
controlling din fushin ta
"Then mecece? Am your boss kuma
komai bazaki sai kinyi it's part of your job,
after all biyanki zanyi ba kyauta bane"
yafada Yanajin wani nishadi a zuciyarshi
ganin sai qara hawa take
"Yes aiki nake maka but am not a cook,
am a secretary for crying out loud" tafada
tana yarfa hannuwa cikin fishi.
"Wannan ke ya shafa, nidai kawomin
abinda nasaki, now!" Ya qarasa maganar
cikin dan daga murya
Shiru tayi ranta a mugun 6ace, tunda
take bata ta6a shiga 6acin rai data kasa
controlling irin yau ba.
Ya shanyata na kusan 2hours sannan
kuma yace ta hadamashi coffee harda
wata shegiyar fried spiced egg?
Dakyar ta iya controlling din kanta sannan
ta tashi fuu tashiga kitchen.
Binta yayi ta kallo harta shige sannan ya
juyo yana murmushin jindadi
Cikin yan mintuna saigashi ta dawo
riqeda mug din coffee ta diremashi a
gabanshi tanufi hanyar dakinta a fusace
"Karki qara step guda anan" yafada yana
dakatar daita.
"Kijirani ingamamutafi" yafada yana
daukar mug din batareda yayi
complaining din Rashin ganin kwan ba.
Nanma saida ya 6atamusu lokaci sannan
ya gama sha ya miqe yayi gaba yana
cewa "shall we"
Binshi tayi da mugun kallo sannan itama
ta biyo bayanshi zuciyarta k**ar zatayi
bindiga.
Saida yashiga mota ya zauna sannan
tafito.
Tunda tafito yake kallonta tacikin motar.
Ta taho sanye da fuskar angry bird yan
kumatunta sun dan turo alamun she's still
angry.
Tunda yake beta6a ganin Wanda fushi
yaima kyau ba k**arta, k**ar fuskar
taita zama ahakan.
Ganin ta qaraso yasashi saurin kauda kai
yana basarwa.
Bude kofar tayi ta shigo ta zauna still
fuskarta a tamke jitake k**ar taita ihu
don haushi.
Kunna motar yayi yaja s**a fita daga
harabar gidan.
Tsit motar tayi kowa da abinda yasha
mishi kai, saudart sai cika take tana
batsewa, jitake k**ar tayi kuka, sosai
take missing yan Niger she badly want to
call them.
"The meeting will hold at 2:00pm" taji
yafada
Yaitayi k**ar bata jishiba don ko kallon
gefenshi batayiba.
Hakan yasashi juyowa yace
"Are you deaf?" Ya tambaya cikin husky
voice
Juyowa tayi ta watsa mashi Lulu eyes
dinta sannan ta dauke kai tana cewa "ok"
Shiru yayi shima ya kauda Kai yana
lumshe ido yana budewa ahankali don
shikadai yasan abinda yaji data
watsamashi idanun nan.
Cigaba da tuqin yayi yana sauraron
bugun zuciyarshi data sauya a take.
Itakau cigaba da kallon waje tayi tana
kumburi gashi tana son cemashi ya biya
dasu wajen saida layi amma takasa.
Kamar wasa sai gani tayi yayi parking
gaban wani babban shagon siyarda
wayoyi.
Hakan yasata saurin gyara zamanta daga
kishingiden datake tana kallon wajen
murmushi na su6ucemata batareda
tasaniba.
Jin k**ar ana kallonta yasata juyowa
s**a hada idanu, yawani basar ta hanyar
gallamata harara yana ta6e baki.
Kauda Kai tayi tana cewa "oho dai" cikin
zuciyarta amma qasan zuciyarta fall
farinciki at last zata samu kiransu daddy
Saida tabari yafita sannan itama tafito
lokacin harya shigewarshi, hakan yasa
itama ta shiga zuciyarta fall murna
Direct wajen wani saurayi taje cikin masu
saida wayoyin shagon
"Hi" tafada
"Hello ma'am you're welcome, wane
taimako zan iya yimiki?" Yafada cikin
murmushi
"Layi nakeso" duk a harshen turanci suke
maganar
Nan ya fiddomata ta sayi guda biyu
tasaka nan take
"Zai fara aiki bayan awa daya" yafada
mata yana bata receipt
"Ok thanks" tafada tana amsa fuskarta fall
murna
Waje tafita fuskarta a sake sa6anin dazu
ta taddashi jingine da motar ya rungume
hannu a qirji.
Qarasowa tayi ahankali zata zagaya ya
dakatar daita da "take" yana cillomata
makullan motar.
Cafewa tayi tana kallonshi da alamun
tambaya
"Drive us ai ba nikadai na iya driving ba"
yafada yana zagayawa inda take zama
Mere baki tayi sannan tadawo ta bude
mazaunin driver tashiga ta kunna motar
sannan tajasu cikin driving dinta mai
burgewa.
Tafiya s**a fara yana gwada mata hanya
har s**a iso wani shahararre kuma
qawattacen hotel.

Jafar sa'ad comments

AUREN YAR JEJENIYA__PART___103____________©®........suna fitowa soro Abdallah ya kalleta cikinmuryar rarrashi yace"wanna...
29/10/2025

AUREN YAR JEJENIYA__
PART___103__
__________©®........suna fitowa soro Abdallah ya kalleta cikin
muryar rarrashi yace"wannan fushin da k**eyi
duk sbd zaki rabu da innar ne khairee?"karki
damu zamu dinga zuwa kina ganinta
ko?"yak'are maganar sadda s**a fito k'ofar
gidan"ita kuwa k'in mgn tayi "da kansa yabud'e
mata back sit ta shiga ya rufe"ya zagaya
mazaunin driver yashiga"yayinda k**al ke zaune
yana waya da leemart"big man na k'ok'arin
tashin motar kiran sa'ada yashigo cikin
wayarsa"d'an murmushi yayi be d'auka ba ya
juyo yana mik'oma ummu wayar had'e da fad'in
Aminiyar kice ke kira"murmushi ummu tasaki
tana Amsar wayar"Abdallah yashagala da
kallonta har ya rik'e hannun ta batare daya
saniba"saida ta sakar masa mintsini sannan
yacika mata hannun nata"kuma wayar saita
katse"yana k'ok'arin mgn wani kiran yakoma
shigowa"ummu dai batama yarda ta kallesaba ta
d'auki wayar tana murmushi tayi sallama"sa'ada
tayi ihun murna tana fad'in Anty dama kina kusa
da yayan?"Eh baby yasu Ammi?"gata nan lafiya
qlau"kice ina gaida ita"yanzun muna kan hanya
ne"to Anty kimun tsarabar irin turarukan da
mama ta tab'a bani"to shikenan dama dasu
nazo"dg haka s**ayi sallama ta rik'e wayar
tanata masa bincike" Abdallah kuwa duk
yakashe kunne yana jin firar tasu yana kuma
driving d'in"jefi jefi yana kallonta ta madubi"idan
sun had'a ido yasakar mata killer smile"ita kuma
ta hararesa"k**al kuma suna fira dashi sama
sama bayan yagama wayar da leemart"gaba
d'aya ummu ta tsorata da irin text message d'in
data gani na y'an matan dake Rok'onsa
yasosu"tasha Alwashin bashi kulawa ta yadda
bbu wacce zatayi gigin shiga rayuwarsu"saidai
Inda hankalinta yad'an kwanta"wasu messages
d'in ko dubasu beyi"b***e harma ya musu
reply"duk delete tayi had'e da blocking
nasu"saima sannan ta tuna da pic d'in daya
musu ita dashi kwanaki A d'akinsa"tana kuwa
dubawa ta ganshi"tanata kallosu tana jin tsananin
sonshi da kishinshi nabin ko ina Ajikinta....
khairee ki kwanta kiyi bacci kafin mu iso idan kin
gaji da zaman"ko kuwa na bawa Abokina driving
d'in na shigo na miki tausa?"Ahankali tace"ah ah
banajin bacci Ai"k**al Aransa yace"YAU DA
GOBE kenan"(book d'ina)....tun suna tafiyar
Idonta biyu har tayi bacci sai gab da magrib s**a
shigo garin KD"kai tsaye gidansu k**al s**a
fara nufa"wanda har lokacin ummu bacci takeyi ,
mutumin naku nata kallonta ta madubi"bayan
sun iso big man yakoma yi masa godiya"k**al
na dariya yace"yau dai nasan kai Angone"to
moyafi raina?"bbu ,muma mun kusan bin layinku
, yak'are maganar yana dariya yyi gaba"big man
yaja motar batare daya tashi khairee dake bacci
ba"sbd beson yakatse mata baccinta"sadda
s**a iso gida harma Anfara kiran sallar
magrib"ummu ta bud'e idanuwanta tana
hamma"y'an mata nah kin tashi ko?"taji
sanyayyar muryanshi me dad'in
Amo"uhmm"kawai ta furta bata yadda ta
kallesaba"yanxun sai muje ki huta ko?"shiru tayi
tak'i kulashi"yyi parking s**a fito dg cikin
motar"yana rik'e da troley d'inta"ita kuma ta
rik'e hand bag nata da wayoyinsu ita dashi"kai
tsaye part nasu s**a wuce"shine yasaka key ya
bud'e k'ofar"be shigaba sai juyowa yayi ya
kalleta yaga tayi k'asa da kanta"zoki shiga
khairee nah"batayi mgn ba ta wuce"sannan ya
shigo ya rufe k'ofar da key"parlourn share k'al
yake"da Alama sa'ada ta gyarashi ta musu
girki"dan ga warmers d'in Abinci nan jere A
dining area"d'akinta ummu ta nufa ta bud'e ta
shiga"Abdallah yabiyota da troley d'in yana fad'in
nasan kina jin yunwa ko?"ah ah"sallah zanyi
kaje kaima kayi"to shikenan Amma dan Allah
khairee karki rufemin k'ofa kinjiko?"uhmm kawai
ta fad'a"bece komaiba yanata kallonta tayi
tsaye"badan yasoba ya barta yafita dg cikin
d'akin"ita kuwa kayan jikinta ta cire ta d'aura
towel"saida ta share d'akin ta goge sannan ta
shiga wanka"bayan tafito tayi sallah"tana idarwa
ta shirya cikin doguwar riga ta bacci ta d'aura
zani daga k'asa"jikinta nata k'amshi"tana zaune
gefen bed ta kira mama tasanar mata sun sauka
lafiya"nasiha ta k'ara yimata kafin suyi
sallama"Ajiye wayar tayi tana tunanin tashi taje ta
d'akko ruwa tasha taji knocking"gabanta yafad'i
tace"waye?"nice Anty"cewar sa'ada"ki shigo
baby ,gama sakonki nan kan mirror ki d'auka"da
sallama sa'ada ta shigo d'akin"ta gaida ummu
had'e da yimata sannu da zuwa kafin tace"dama
Anty Ammi da daddy da yaya suna
parlour"daddy yace"kizo"dato ta Amsa k'irjinta
nata bugawa"sa'ada ta fita"ita kuma ta saka
hijab ta fito"muryar daddy taji yanata yima
Abdallah fad'a"yana zaune k'asa kan carpet ya
sunkuyar da kai"yana sanye da farar jallabiya
Ajikinsa"sallama ummu tayi ta zauna gefen big
man ta gaidasu"Ammi ta Amsa tanata binta da
kallon tausayi"tana kuma godema Allah daya
bama Abdallah ita Amatsayin matar Aurensa"sbd
d'azun bayan yayi sallah ya shiga yasanarwa
Ammi yadda Akayi"shiyasa taga gara tasanarwa
daddy shima Amasa fad'a dukda iyayen khairee
d'in basusan wane irin Aure s**ayi ba"saidai
yadda mahaifiyarta tayi mata fad'a ta tursasata
tadawo yasaka Ammi ganin k'imar
iyayenta...lokacin da daddy yaji komai ransa
yab'aci matuk'a

AUREN WATA TARA__PART__58_______________©®magana ake fad'amun stupid kawai"durkushewa a wajen Zarah tayi batasanlokacin ...
29/10/2025

AUREN WATA TARA__
PART__58__
_____________©®magana ake fad'amun stupid kawai"
durkushewa a wajen Zarah tayi batasan
lokacin da wani kuka Yazo mata ba Dan
sosai taji zafin murde mata bakin da yayi
"sosai kukan nata ya bawa MD Haushi ya
rasa wace irin yarinya ce wannan Ganin
tana shirin Mikewa tabar wajen ya
sanyashi saurin ruko hannunta kokarin
fusgewa ta fara ya rik'e gam ganin tana
wasting time nasa ya sanyashi rungumota
gam a k'irjinshi a tare s**a sauke
nauyayyar Ajiyar zuciya Zarah ko shiru
tayi sai Lafewa da tayi tana shak'ar
daddad'an k'amshin turarenshi mai
sanyaya zuciya Wayarshi ya lalubo tare
da dannawa wata number kira ringing
biyu aka daga wayar yayiwa Wanda ya
kira bayanin Inda yake Ba ayi minti biyar
ba saiga lafceciyar mota fake a wajen An
fito an bud'e masa back seat tare ya
shiga da ita dukda turjewar da ta fara
suna shiga Driver yayiwa motar key s**a
bar wajen Hade kanta da guiwa tayi ta
fara kuka na babu gaira babu dalili tsaki
yaja a ranshi ya ce " sudai mata matsala
ce wlh ita wannan matsalar tata ma tafi ta
kowa mtwss"jin kukan ya fara damunshi
ya sanyashi saurin janyota Jikinshi tare
matseta tsam k**ar zai maida ita ciki
gidanshi dake nan g r a ya umarta driver
da ya kaisu Bayan sun isa har lokacin
shashekar Zarah take jin an tsaida motar
ya sanyata saurin Dagowa Kallon wajen
tayi daga mota kafin ta kalli MD da a ka
bud'e masa yake shirin fita saurin ruko
hannunshi tayi ta ce "Ina ne ka kawoni
nan kuma" ba tare da ya Kalleta ba ya ce
sayar dake nazoyi dukda Zarah tasan
wasa yake mata bai hanata tsorata ba
marairaicewa tayi ta ce "Dan Allah kayi
hakuri ka maidani Makaranta Dare nayi "
Banza yayi mata ganin ya fita Ya sanyata
saurin fita itama ta bishi baya tana karewa
katafaran gidan Kallo Aljannar duniya
kenan"ta fad'a cikin ranta binshi ta
dingayi cikin Sauri duk Inda ya nufa Dan
taji akwai karnika a gidan kuma ita daman
ba abunda ta tsana sama da k'are ganin
yayi mata nisa ga haushin Karen dake
tunkarowa ya sanyata saurin Rugawa a
guje Aikonan Karen ya biyota Dan tayi
gudu daukarsa bata Gaskiya ihu Zarah ta
fasa tare da rugawa taje ta kankame MD
tsam ta fashe da kuka tana yarfe hannu
ta gama rikicewa daidai lokacin da Karen
ya Iso Inda suke yana haushi murmushi
MD yayi ya ce "matsoraciya a ransa
common kare ya firgita ta Cikin kuka ta
ce " Dan Allah ya Musty ka taimakamun
kar Karen nan ya cijeni wlh tsoronsa nake
please mubar gidan nan Dan Allah "ta
fad'a ta na k'ara kankamesa " Shafa
bayanta yayi yana Daddab'a cikin sigar
lallashi batare da yace mata uffan ba
shafa kan Karen yayi Tare da ce masa
yabar wajen Lokaci guda Karen yabar
wajen Ajiyar zuciya Zarah ta sauke Dan
Allah kadai yasan irin yanda zuciyarta ke
Bugawa saboda tsoro "matsoraciya saiki
sakeni tunda na kori Karen kuma daga
yau Kika karayimun musu ko na fad'a
magana kika maida ga da abunda zan
hadaki ina da ire_irensu sunfi goma" cike
da kunya ta zame jikinta daga nashi turo
baki tayi Jin Abunda ya ce "wara idanu
yayi tare da nuna kanshi da yatsa ya ce "
ni k**ewa"cikin shagwabar da ta zame
mata jiki duk sanda tazo mata ta ce "Nifa
ba da kai nake ba " ta k'arasa fad'a
hawaye na sauka daga idanunta "Had'iye
kukan ya fad'a yana k**a hannunta "
k**ar an d'auke nefa haka ta Had'iye
kukan shi kanshi har Dariya taso ta bashi
ya fusge "hars**a isa katafaran palourn
gaban Zarah na fad'uwa saida ta kusa
kauyanci cin karo da hadaddun turkey
furnitures d'in da suke shake a palourn
komai na palourn y'an waje ne bazaka
tab'a cewa a Nigeria kake ba "a rakube
ta zauna d'aya daga cikin kujerun palourn
tana ta kalle_kalle a wayance Wanda
bazaka tab'a cewa tanayi ba a ranta ta ce
" Wasu na cikin wahala wasu bama
susan anayi ba jifa Dan Allah wannan
lafcecen gida da kayan cikinsa k**ar
baza a mutu ba "zaki iya tashi kije kiyi
salla kafin na dawo ga bedroom Chan" ta
tsinkayi muryarshi data dawo da ita daga
duniyar tunanin da ta Lula Firgit ta
Kalleshi k**ar mai shirin fashewa da
kuka ta ce "Amma kuma ni kad'ai zaka
bari a gidan nan ni tsoro nakeji wlh
karnikan nan karsu shigo Su cinyeni ni
kadai" murmushin da baikai fuska ba yayi
ya ce "bazan jima ba zandawo babu
abunda zasu maki bazasu shigo nan ba "
Badan taso ba ta ce "To Amma karka
jima Dan Allah " Ba tare da ya amsa ta ba
yayi Hanyar waje tanajin fitarshi ta turo
baki tare bin kofar da harara ta ce "Mugu
Allah saiya sakamun ta fad'a tana nufar
d'akin da ya nuna mata Dan tayi salla
Nanma saida tayi kauyanci cin karo da
kayan alatun dake dakin ga gaban mirror
din dake shake da kayan shafa irir_iri
tab'e baki tayi cikin Sauri ta shiga toilet
tayi alwala ta fito Bayan ta tada salla cikin
Sauri ta bar d'akin Dan ji take a tsorace
take palourn ta dawo ta zauna Kan kujera
tare da Yin tagumi sai Bayan isha i Taji
tsayuwar mota lek'awa tayi ta window
taga shine cikin Sauri ta koma ta zauna
harya shigo Mikewa tayi ta ce " yawwa
nazo mu tafi ya Musty?Batare da ya
Kalleta ba ya ce "Sai gobe " yana gama
fad'ar haka ya Aje take away din da ya
shigo dashi tare da Yin hanyar dayan
bedroom

RAINA K**A__PART___38____________©®da jakadiya yafara cin karo tana rik'e daKhaleel a hannu, khaleel yakwace yatahoda gu...
29/10/2025

RAINA K**A__
PART___38___
_________©®da jakadiya yafara cin karo tana rik'e da
Khaleel a hannu, khaleel yakwace yataho
da gudu yana fad'in “Uncle oyoyo”.
Hannayensa ya bud'e masa yafad'a
jikinsa, ya shafa kan yaron yana fad'in
“my boy ykk?”.
“lafiya Uncle Sam... yaushe kadawo?”.
Murmushi Galadima yayi, yad'an ja
kumatun khaleel “to maganatu yau na
dawo”.
Dariya yaron yayi, zai sake joho wata
maganar Galadima ya d'ora yatsansa
akan bakin yaron alamun yayi shiru.
Shirun kuwa khaleel yayi dan yasan halin
Uncle Sam.. saraii.
Jakadiya ta rissina tana gaidashi, amsawa
yayi fuskarsa da 'Yar fara'a, ya tambayeta
ya jikin Abie.
“jiki Alhmdllh ranka ya dad'e”.
Kansa kawai ya jinjina mata yay gaba
rik'e da hannun Khalel.
Da sallama ya shigo d'akin da Abie ke
jinya, d'akine babba k**ar Bana asibitiba,
daka gani Kasan anyisane saboda
manyan mutane irinsu, Momma na zauna
akujerar gaban gadon da Abie ke
kwance, gadon Kansa bawai ainahin
gado bane na asibiti, duk wasu na'urori
ne ajikinsa, da alama sune suke
taimak**a jikin Abie d'in, k'umba
Momma ke yanke masa.
Aunty Mimi na zaune bisa kujerun da aka
shirya a gefe tamkar falo, System Ce
agabanta tana danne-danne.
Sallamar Galadima yasata d'agowa tana
murmushi, “My k'ani oyoyo” tafad'a tana
ture system d'in daga cinyarta.
Murmushi yamata shima, cikin
maganarnan tasa ta k'asaita maik**a da
anmasa tilas yace “my dear aunty
barkanki”.
Hannu tasa tad'an bigi damtsen
hannunsa, cikin wasa tace barka zakace
ba bagyka ba”.
Shafa Inda tad'an bigesan yakeyi yanda
6ata fuska k**ar wani k'aramin yaro,
“ALLAH akwai zafi aunty Mimi, wai har
yanzu ban girma da buguba awajenki?”.
“tab ai da sauranka, sai randa kayi aure
zan daina”.
Bakinsa ya ta6e yak'arasa inda Momma
take yana fad'in, “aiko k'yadad'e baki
barinba kenan”.Momma dake murmushi saboda drama
d'in tasu ta kalli Abie da shima fuskarsa
take a washe alamun yayi farinciki da
ganin d'an nasa.
Gabansa yaje ya durk'usa, saitin Face
d'insa, ya saka hannunsa cikin NASA
fuskarsa d'auke da murmushi yace, “my
Abie barka da rana”.
Da idanu Abie ya amsa masa, dan sune
bakin maganar yanzu.
Yakuma masa magana da ido alamar
yaka barosu?.
Murmushi Galadima yayi na takaici,
sannan yace, “mai martaba na gaidaka,
shima zaizo nextweek”.
Farin cikine Yakuma fad'ad'a a fuskar
Abie, dasu s**asan yanayinsa, s**ad'ai
zasu iya fahimtar farin cikinsa ko
damuwarsa, musamman ma Momma.
Momma dake kallonsu tayi murmushi,
Galadima ya maida kallonsa gareta,
“Momma na yana sameku?”.
“Alhmdllh Muh'd, yaka barosu?”.
Baki yad'an ta6e sannan yace “lfy lau, ya
jikin Abie?”.
“jiki Alhmdllhi, dan randa ka tafi yatsun
hannun damarsa sund'an motsa”.
Da Sauri Galadima yace “da gaske
Momma?” yay maganarne yana kallon
hannun Abie d'in, sannan cikeda farin
cikin ya sumbaci hannun yana fad'in
Alhmdllh ala kulli halin, ALLAH yabaka
lafiya my sweet Abie”.
Lumshe idanu Abie yayi farinciki na k'ara
fad'ad'a a face nashi, aunty Mimi da
momma da jakadiya suna kallonsu cikeda
tausayi s**a amsa da amin. khalel yata6a
kafad'arsa, juyowa yayi yana kallonsa.
yaron yakai hannu yana sharema
Galadima hawayen dasuke kwance a
kumatunsa. galadima yajawosa ya
rungume yana sumbatar kan yaron,
fuskarsa d'auke da murmushi.
★★★
Yau mune k'arshen tafiya school, saboda
lectures d'in yamma ne damu, Fauziyya
kuma batada lafiya bazatajeba.
Kasancewar abubuwa sun kuma lafawa
yau sai bamu saka nik'af ba, amma yana
rik'e a hannunmu idan mun shiga cshool
zamu saka.
Mun fito bakin t**i muna jiran taxi ko
napep saiga wata bak'ar mota wulik ta
faka agabanmu, dagani har Munubiya
d'auke kanmu mukayi gefe.
Mai motar ya sauke glass d'in yana
kallonmu, sallama yayi mana, Munubiya
ta amsa, nikam koma kallo bai isheniba.
Ganin haka saiya bud'e motar yafito,
matashin saurayine bak'i k'yak'yk'yawa
mai yawan fara'a. Yace, “haba 'yan mata,
babu fad'a miya kawo gaba”.
Cikeda tsiwa nace “sai aka cemaka mu
'yan matane? to matan aurene”.
Murmushi yayi, sannan ya gyara
tsayuwarsa, “dear hakan ma dakikayi
yakuma tabbatar min da Bahaka
baneba”.
d'an hararsa nayi na d'auke kaina, danni
yanzu maza duk haushi suke bani wlhy.
Dariya yayi, “oh sweety karkisa na sume
mikifa a t**innan”.
Ganin yana neman shiga hancinmu
yasani jan hannun Munubiya muka bar
wajen, k'yalemu yayi Yakoma mota ya
zauna. har muka sami abin hawa yana
kallonmu. haka yayta bin mai napep d'in
har k'ofar makaranta, daga nan kuma
bamusan ya akayiba mudai muka shige.
Kwana biyu da faruwar haka muna wanki
a tsakar gida saiga ya Anas yashigo, ya
kallemu yana murmushi, twins cikinku
waye mai saurayi mai bak'ar mota?”.
Mu duka kallonsa mukayi, gwaggon
Haleema da maman safara'u dake aiki a
tsakar gidan suma duk s**a kallemu.
Da sauri Munubiya tace “munaya Ce yaa
Anas”.
“kije to yana jiranki a k'ofar gida”.
harara na dallama Munubiya “wlhy
Munubiya k'arya dai babu k'yau”.
Dariya tayi tacigaba da wankinta, “kitashi
kije kina 6ata masa lokaci”.
Hijjab na d'auka nafita danufin zuwa na
sauke masa masifa na dawo.
Gwaggon Haleematu da maman Safara'u
s**a

TANA TARE DANI__PART__103________©®Kai take girgizawa continiously No! No! No! Thiscan’t be happening bareyi in auri Bos...
29/10/2025

TANA TARE DANI__
PART__103__
______©®Kai take girgizawa continiously No! No! No! This
can’t be happening bareyi in auri Boss d’ina koba
dan haka bama bareyi in barsa ya aureni ba,
*BANIDA BUDURCI, BANIDA MARTABA* duk
ranan da Mr. Fauzi ya gano hakan ze tsaneni
fiye da yadda ya tsani mutuwar sa, I can’t marry
him saboda barin iya fad’a masa sirri na ba
k**ar yadda barin bari yagano hakan ba da
kansa kuma.
“No Sir I can’t marry you, I can’t dan Allah kabar
wannan magana, ni kawai release Ya Farouq.”
“Yes, yes you will marry me Fannah Aleeyu. In
ma tunani k**e ko wani abu ze shiga tsakanin mu
ki kwantar da hankalinki. *CONTRACT
MARRIAGE* zamuyi.”
“Contract marriage?” Ta tambayesa cike da
rashin fahimta.
“Yes contract marriage nima some weeks ago
Abuu yace se nayi aure, seya aura min wata ‘yar
uwarshi Falmata saboda yana ganin I’m still
young wataran baran iya managing Enterprise
d’ina ba kuma wai ban gama mallakin hankali na
ba so yakeson yamin aure, nikuma nace masa
barin aureta ba, mukayi deal dashi akan in 6
months time zan nemo mace in kawo masa gida
wanda zan aura. Ni koda nan da infinity,
k’arshen duniya za’a bani banga macen da zata
min ba har inji ina sonta zan aureta ba, I will use
you Miss Aleeyu and fake up a relationshop with
you. Ni a rayuwa na banason aure, duk abinda
ze had’ani da mace ma hasali banaso ke kad’ai
ne...” Ya nisanta “when it comes to you I just
don’t feel thesame way. Mu rufa wa junan mu
asiri and help each other. Zan aureki for just *6
MONTHS TIME* after then semu rabu ince wa
Abuu kinci amana na kin tafi kin barni, kince you
don’t love me anymore, you see daga lokacin
nan bare sake tak’ura na da zancen aure ba
zece I’m broken I cannot move on k**ar yadda
shima har yau yakasa sake aure tunda Ummimi
ta tafi ta barsa. Ke kuwa kinga nasan by 6
months time d’innan Farouq halan ya gaji da jira
ya koma inda yafito kinga seki cigaba da tafiyar
rayuwarki k**ar yadda take da. NikumaI
promise you a k’arshen 6 months d’innan bayan
munyi ending marriage d’in zan baki 6 million
tunda dama contract marriage ne.” Ido sosai
Fannah ta zaro 6 million???? Ta fad’i a ranta.
“Kinga inma so k**e kubar garin nan da
family’nki zuwa wani garin zaku iya, yadda
Farouq bare sake tak’ura muku ba. Kuma a
kowani k’arshen wata zanna biyanki albashinki
na aiki N500,000 sede bawai zakina min aiki
bane still, zan sauk’e ki daga zama min PA,
bareyi ace mata ta PA ta ba. I’ll get the papers
ready gobe, all you have to do is sign them So
what do you say?”
Shiruu tayi dan tunanin ma ta kasa. Taya zatayi
agreeing wa qudurin nan? Contract marriage,
how? Setayi decieving kowa kenan tasa su
yarda eh soyayya s**ayi da Mr. Fauzi har ya kai
ga aure? Kuma seya b’ata mata image gun
iyayensa, yace taci amanar sa? Gaskia baratayi
ba amman kuma intayi la’akari itace ma zata fi
benefiting. Dubu d’ari biyar sau 6 miliyan uku
kenan plus miliyan shida daze bata ta tashi da
miliyan tara kenan. Wow! Zata samu takai
Babanta har k’asar waje ayi masa aiki takuma
tattara family’nta subar Maiduguri su koma ko
Kano ko Kaduna inda su Farouq bara su sake
saminsu ba. Zata samu ta sa Afrah ma a
makaranta. To yanzu ya? Ta yarda kenan?
“Miss Aleeyu?” Ya tsamota daga cikin duniyar
tunanin data wula. “Have you make up your
mind?”
“Sir naji komai amman seka b’ata min image
gaban iyayenka ne su d’au mutumiyar banza ce
ni?”
“Yes Miss Aleeyu this is the only way zan
kub’uta, the only way Abuu zeji tausayi na bare
sake min maganar aure ba har se in ni na masa.”
Kai ta gyad’a a hankali “Sir amman baramu na
had’a kwanciya bako?”
Lallai ma yace a ransa, shi d’inda ko wace mace
nada burin ganinsa kan gadonta ita tasamu zata
tsaya tana masa tsiya.
“Miss Aleeyu nima ba so nake ba dan yazama
dole ne, ofcourse we will share a bed amman ba
abinda ze shiga tsakanin mu, in ma gudun
abinda k**e kenan, kisani banida interest cikin
wancan abin ko physical contact ban yarda ba,
lokacin da zamu iya tab’a juna shine only if either
your family or my family visits saboda kar su
gane faking auren mukeyi.”
“Sir you mean barin sanar da su Mami ba? Ai ya
k**atasu su sani-”
“Bek**ata ba” ya katse ta. “Ko Afrah ban yarda
ki fad’a mata ba, this is our secret dan the
moment kika sanar da mutum d’aya kin mana
ruining komai kenan. Don’t tell anyone, clear?”
Kai ta gyad’a tana nazarin ya zata soma b’ullo
wa family’nta da wannan zancen

comments

BIBIYATA AKE__PART__130________________©®\Nisawa mai martaba yayi yace, yareematashi mutafii gida, girgiza kai yayi yace...
29/10/2025

BIBIYATA AKE__
PART__130___
_____________©®\Nisawa mai martaba yayi yace, yareema
tashi mutafii gida, girgiza kai yayi yace A'a
abba bazan tafii ba, zata dawo, zan
jirata." girgiza masa kai mai martaba yayi
yace Zamu nemota kataso mutumii, zaiyi
magana mai martaba yayi saurin katseshi
yace, kada muyi haka dakai, yareeema
ka tashi mutafii, har indai nine nahaifeka
kabii umarnina, miqewa yayi yana Shirin
fad'uwa mahaifinsa yayi saurin riqoshi,
haka yafita dashi daga cikin asibitin yariqe
hannunsa k**ar k'aramun yaro, shikuma
yana ta kalle kalle, haka mai martaba ya
sashi amota s**a nufii, gida."Fad'in irin tashin hankalin da marshall
yashiga wannan ma tsayawa, bata lokaci
ne, gabaki d'aya yazama wani iri, bud'e
idanuwansa ma wahala suke bashi, b***e
aje ga cin abincii ko wani abun." nauyii
idanuwansa ke masa, alokacinne yak'ulla
mugun alaqa da ciwon kai, wanda
akullum kansa ke barazanar tsagewa
gida biyu,
Baida sukunii, baida wani sauran
kwanciyar hankali, kullum cikin zullumi da
tunanin yanda *hanna* tashiga yake,
tunaninsa ko awana irin hali take, baisani
ba." a kullum har wani hucii ne mai d'umi
yake fita daga jikinsa, idanuwansa kuwa
idanya bud'e yanda kasan garwashi, har
shakkarr bud'esu yakanyi, dan har indai
mutum yana kusadashi sayyya razana,
sa'ii-sa'ii yakanyi aman jini, amma bai bari
kowa ya lura ba, koda sallah ma ad'aki
yakeyi, ummiii tayi kukan harta gajii,
Ganin bbu Wata mafita yasa umma takira
mama akan tanason ganinta idan zata
samu dama suzo suda baba, dafarko
mama tayi tunanin su hassana da
hussaina,
Hakan tafad'awa umman, amma umma
tace mata tabarsu ma ammah tazo, ganin
zancen mai k'arfii ne yasa tasanarda
baba, kiran k'aninsa yayi awaya, abba
yacewa baba gaskiya yanadakyau
zuwannasu, haka s**a shirya washe garii
s**a d'auki hanyar kano, sha d'aya
tamusu acikin garin kano, gidan Abba
s**a wuce kai tsaye, ganin Wata irin
ramar da umma tayi mama ta matuk'ar
tsorata, dasaurii tak'arasa kusada ita, riqo
hannunta mama tayi cikin kid'ima tafara
magana,yaya menene yasameki haka?"
yaya dama bakida lpy ne baki
fad'amunba?, girgiza mata kai umma tayi
kawai hawaye nabin fuskarta, da sallama
abba yashigo falon, ganin umma na
hawaye yasa yace ashsha assha, yanzu
daga zuwansu kintaryesu da kuka, hava
da Allah wai kekam bakyada hakurii ne,
kuma bakida juriya, hava, idon mama har
yacika da hawaye tashi d'aya yafara zubo
mata takalli abba tace dan Allah
kafad'amun ko wani abun ne ke
damunta, rintsawa abba yayi kafin yace,
kuzauna ku huta kafin namukubayani, girgiza kai mama tayi tace, nidai
bazan iya wani hutawa ba, bayan Ina
kallon y'ar uwata cikin wani hali, juyawa
abba yayi batareda yak'ara cewa komai
ba, yanufii babban palour wajan baba."
Duk yanda mama taso tambayar umma
abunda ke faruwa takasa sanarda ita,
abba baifii 10minute da tafiya ba ya leqo
yace, sutaso su tafii, tunda s**a d'auki
hanya bbu wanda ya iya magana, ganin
sun nufi fadah yasa gaban mama da
baba yayi mugun fad'uwa tunainsu d'aya
badai wani abun bane yasamu *hanna*
sunfii ma karkata da ko batada lpy ne,
har s**a isa fada, bbu wanda yatofa ko
da kalma d'ayane, dama ansan da
zuwansu, dan haka falon mai martaba,
aka sauk'esu marshall na kwance tun
shigarsu afalo, amma bai iya d'aga kansa
ya kallesu ba b***e susaran zai gaidasu
abun bak'aramun mamaki yabawa baba
da mama ba, banda umma da abba dan
dama sunsan irin halinda yake ciki, tunda
*hanna* ta6ata bai k'ara furta ko kalma
d'aya ba, ummii da mai martaba ne
s**ayi sallama s**a shigo falon daga
d'akinsa, waje mai martaba yasamu
yazauna, sannan yabawa su abba hannu
s**a gogaisa da addu'a yabud'e taron
sannan yafara magana."
Kusani cewa Duk wani abunda yafaru
muqadda rine daga Allah, kuma Allah
subhanahu Wata ala yace, la yukalliful
lahuu nafsan illa wus'aha, yace Allah
baid'aura rai abunda bazata iya ba."
sannan Kusani kowani d'an adam da irin
hanyardaa Allah ke jarabtarsa, sai dai
muyi addu'a Allah yabamu damar cinye
tamu jarabawar data fad'o mana, sannan
d'aukan qaddara yana d'aya daga cikin
cikon imani, musani Allah baid'aura mana
abuu har sai dan yagwada imaninmu
Yaga yaya jamuyi dan yajarabcemu,
tundaga wannan lokacii ummii tafara
hawaye tana goge hawayen idanuwanta,
nan mama tak'ara karyewa sosai tace,"
ku gayamun maiya samu *hanna* mu
musulmaine tabbas zamu kar6i kaddar
mu hannu bibbbiyu, zamu riqe wannan
jarabawa, dakyau mumata kyakyawan
duba yanda idan sk**akon mu yatashi
futowa zamu samu sak**ako mai kyau."
ita kanta duniyar nawa take?" kan ummii
nak'asa takasa d'agowa takallesu tace
*hanna* ta 6ata wallhy *hanna* ta6ata,
gaban mama ne yafad'i rass, wani irin jirii
ne yafara ebanta, amma kuma duk
dauriyarta ta tattaro, da mamakin
mutanen wajan gabaki d'aya,
murunushine kwance afuskarta, sannan
cikin dakiya tace, kada ku damu da sanin
Allah in sha Allah zai bayyanata,
addu'arda zamu mata Allah yasa tana
wajan kyakyawan hannu."

Jafar sa'ad comments

Address


2233

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jafar sa'ad posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share