26/09/2025
Shugaba Trump ya ce daga ranar Laraba, kamfanonin samar da magunguna da ke shigar da su kasar za su fuskanci harajin kashi 100 cikin 100 matsawar basu fara samar da masana'antunsu ba Amurka.
Manazarta sun yi imanin cewa harajin zai cutar da ƙasashe irin su Ireland, wacce ta fi kowace kasa fitar da magunguna zuwa Amurka.
Trump ya kuma ba da sanarwar ƙarin haraji kan kayayyaki daban- daban tun daga manyan manyan motoci zuwa kayan kicin da na daki da sauransu.