16/07/2025
Buɗe Masallacin Gidan Ƙadiriyya, 1974 Kwanan baya ne aka yi shagalin bude Masallacin Ƙadiriyya da aka gina a Unguwar Kabara, cikin Bìrnin Kano wanda ke hade da Makarantar Islamiyya da Laburare wadanda dukansu aka kashe jimlar kudi sama da Naira 60,000 wajen kammalawa.
A cikin jawabinsa ga taron dubban Musulmi da s**a hallara wajen, kafin ya yanke kirtanin tabbatar da budewar, Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, ya yi kira ga dukan ƙungiyoyin Musulmi na Kasan nan tare kuma da dukan Musulmin da suke da hali dasu riƙa giggina Masallatai da Makarantun Islamiyya yadda za su ba da tasu gudunmawar a cikin tsanaki wajen ginin Musulunci. Alhaji Ado Bayero, kuma ya tabbatar, cewa ta irin wadannan kyawawan ayyuka ne Musulmi na kwarai zai gina addìninsa, daga baya ya ci moriyar abin a duniya da lahira.
A nasa jawabin, Kwamishinan Watsa Labarai da Al'adun gargajiya na Jihar Kano, Alhaji Yusufu Mitama Sule, Danmasanin Kano, ya ba da tarihin gidan Ƙadiriyya na Kano ne, inda aka yi Masallacin a Kabara da kuma irin ƙwazon zuriyar gidan wajen ganin gidan tare da đarikar sun rayu.
Daga nan ne kuma sai ya gode wa kwamitin ginin saboda kokarin đa s**a yi, sa'an nan kuma ya gode wa dukan wađanda s**a taimaka da kuđi ko da gaba wajen ginin Masallacin tare da Makarantar don amfanin dukan Musulmi.
A cikin nasa jawabin, Shugaban Kwamitin ginin Masallacin, kuma Shugaban Ɗarikar Ƙadiriyya a Nijeriya da Yammacin Afirka, Alhaji Muhammadu Nasiru Kabara, Sarkin Yakin Shehu Usman Dan Fodiyo ya bayyana asalin kafuwar dukan wadanda s**a jaddada Musulunci a Nijeriya tun
shekaru aru-aru da s**a wuce sun jaddada tare da Kadiriyya ne.
Alhaji Muhammadu Nasiru Kabara ya bayyana sunayen Waliyyan farko da s**a gabata, k**ar su Wali Danmarina, da Wali Dan Masani, har zuwa kan Shehu Usman Dan Fodiyo wadanda dukansu babu irin gwagwarmayar da ba su sha ba wajen tabbatad da Darikar Kadiriyya a zamanin rayuwarsu.
Ya kuma ce Darikar Kadiriyya kashi biyu ce da wadda ake yi a boye, ba a bayyane ba, da kuma wadda ake bayaynawa a cikin jama'a wadda Nijeriya ke bi da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.
Alhaji Muhammadu Nasiru Kabara kuma ya yi kira ga dukan Musulmi da su tashi haikan wajen fuskantar kowace irin takala da ta taso wa addinsu. Tun da farko kuwa, kafin a kai ga fara jawaban, Sheik Abdul Basidi Abdulsamadu, Shugaban makarantan Alkur'ani a Jumhuriyar Masar, wanda ya zo Nijeriya mussamman don bikin bude Masallacin bisa gayyata, sai da ya karanta wadansu Surori daga cikin Alkur'ani Mai Girma.
Sakataren Kungiyar Jama'at Nasril Islam, Alhaji Tbrahim Dasuki, Baraden Sakkwato, ya halarci wurin, inda ya bayad da gudunmawar Naira 1,000 a madadin Jama'atul Nasril Islam. Alhaji Muhammadu Nasiru Kabara ya bayar da gudunmawar littattafai guda 20,000 ga sabon Laburaren, da aka bude a gefen Masallacin.
Muhimman Mutane daga Kasashen makwabta da kuma gida Nijeriya sun halarci shagalin bude Masallacin wanda ya ƙayatar ainun.
Gaskiya Ta Fi Kwabo, 16 Satumba, 1974