Matashiya TV

Matashiya TV Matashiya! bahaushiyar tasha mai tsage gaskiya komai ɗacinta. Tasha mai zaman kanta, mu na yaɗa labarai ba tare da son zuciya ba
(1)

Wai ina ƴan baiwa ne? Me ake ciki ne kwana biyu?
26/07/2025

Wai ina ƴan baiwa ne? Me ake ciki ne kwana biyu?

26/07/2025

Kai tsaye labaran dare 26/7/2025

26/07/2025

Kai tsaye labaran rana 26/7/2025

26/07/2025

Labaran abubuwan da ke faruwa a duniya a taƙaice 26/7/2025

25/07/2025

Shaye-shaye - Ku matso mu tattauna 08096399266, 0706085911

Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani manomi mai suna Gabriel Vendefan ta hanyar sare masa kai a lokacin da ya ke tsaka da ...
25/07/2025

Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani manomi mai suna Gabriel Vendefan ta hanyar sare masa kai a lokacin da ya ke tsaka da aiki a gonarsa a kauyen Uikpam da ke karamar hukumar Guma ta Jihar. Maharan sun hallaka manomin ne a jiya Alhamis. Mazauna yankin sun bayyana cewa a baya-bayan nan ne al’ummar yankin ke fuskantar barazana daga ‘yan bindiga, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin barin gonakinsu....

Wasu ‘yan bindiga sun hallaka wani manomi mai suna Gabriel Vendefan ta hanyar sare masa kai a lokacin da ya ke tsaka da aiki a gonarsa a kauyen Uikpam da ke karamar hukumar Guma ta Jihar. Mah…

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga kamfanonin samar da wutar lantarki GenCos da su kara baiwa gwamnatin taray...
25/07/2025

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga kamfanonin samar da wutar lantarki GenCos da su kara baiwa gwamnatin tarayya lokaci don kammala tantancewa da kuma tantance basuss**an da aka dade ana binta. Shugaban ya bayyana hakan ne a yau Juma'a, a wata ganawa da ya yi da mambobin kungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki a Abuja. Shugaban ya kuma tabbatar musu da kudirin gwamnatinsa na magance matsalolin da ake fuskanta a bangaren wutar....

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga kamfanonin samar da wutar lantarki GenCos da su kara baiwa gwamnatin tarayya lokaci don kammala tantancewa da kuma tantance basuss**an da aka dade ana …

Jami'an sojin runduna ta 3 na Operation Safe Haven sun kubtar da wani yaro dan shekara 12 da aka sace a karamar hukumar ...
25/07/2025

Jami'an sojin runduna ta 3 na Operation Safe Haven sun kubtar da wani yaro dan shekara 12 da aka sace a karamar hukumar Riyom ta jihar Filato. Mai magana da yawun rundunar Manjo Samson Zhakom ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a yau Juma’a. Kakakin ya bayyana cewa an kubtar da yaron ne bayan da sojoji s**a kai samame maboyar ‘yan ta’adda a karamar hukumar Riyom....

Jami’an sojin runduna ta 3 na Operation Safe Haven sun kubtar da wani yaro dan shekara 12 da aka sace a karamar hukumar Riyom ta jihar Filato. Mai magana da yawun rundunar Manjo Samson Zhakom…

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na kwaso 'yan Najeriya da s**a makale a Afirka ta Tsakiya zuwa gida Najeriya. Ma’a...
25/07/2025

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na kwaso 'yan Najeriya da s**a makale a Afirka ta Tsakiya zuwa gida Najeriya. Ma’aikatar harkokin kasashen waje ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Juma’a a Abuja. Ma'aikatar ta bayyana hakan ne biyo bayan bullar wani faifan bidiyo da ya nuna yadda aka yi watsi da mutanen da ke cikin mawuyacin hali a yankin Bambari mai tazarar kilomita 850 daga babban birnin kasar Bangui....

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na kwaso ‘yan Najeriya da s**a makale a Afirka ta Tsakiya zuwa gida Najeriya. Ma’aikatar harkokin kasashen waje ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa…

25/07/2025

Ku matso mu tattauna 08096399266, 07060859911

Akalla fasinjoji 14 da s**a hada da mata da yara ne s**a rasa rayukansu a wani hari da aka kai a jihar Filato. Rahotanni...
25/07/2025

Akalla fasinjoji 14 da s**a hada da mata da yara ne s**a rasa rayukansu a wani hari da aka kai a jihar Filato. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin jiya Alhamis, a lokacin da fasinjojin ke dawowa daga kasuwar mako-mako ta Bokkos. Rahotannin sun kara da cewa ‘yan bindigan sun hallaka mutanen ne bayan yi musu kwanton bauna daga bisani kuma s**a bude musu wuta....

Akalla fasinjoji 14 da s**a hada da mata da yara ne s**a rasa rayukansu a wani hari da aka kai a jihar Filato. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin jiya Alhamis, a lokacin da f…

Gwamnatin Jihar Rivers ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi aikin magance rikicin manoma da makiyaya a fadin Jihar. Sak...
25/07/2025

Gwamnatin Jihar Rivers ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi aikin magance rikicin manoma da makiyaya a fadin Jihar. Sakataren gwamnatin Jihar Ibibia Worika ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce sasanta tsakanin manoma da makiyaya ya zama dole duba da yadda rikice-rikicen da ke faruwa a tsakaninsu na haifar da asarar rayuka,gidaje da kuma durkusar da harkokin tattalin arziki....

Gwamnatin Jihar Rivers ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi aikin magance rikicin manoma da makiyaya a fadin Jihar. Sakataren gwamnatin Jihar Ibibia Worika ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce sasa…

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Matashiya TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Matashiya TV:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share