21/07/2025
GWANIN BURGEWA: Al’mansoor Gusau Ya Sami Damar Wakiltar Najeriya a Taron Kasa da Kasa a Beijing
Al’mansoor Gusau, ɗan Najeriya kuma mai fafutukar cigaban al’umma, ya samu damar halartar taron bita na kasa da kasa (International Seminar) a Beijing, babban birnin kasar China. Taron ya gudana ne ƙarƙashin shirin AIBO, wanda ke karkashin Ma’aikatar Kasuwanci ta Jamhuriyar Jama’ar China.
Wannan damar wakiltar Najeriya a matakin duniya, a cewar Al’mansoor, wata babbar girmamawa ce da za ta ba shi damar koyon sabbin dabaru, musayar ra’ayoyi tare da gina alaka da wakilai daga sassa daban-daban na duniya domin amfanin ƙasa.
Ya bayyana godiyarsa ga Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar (Marafan Sokoto) da kuma Hon. (Dr.) Bello Muhammad Matawalle bisa tallafi da goyon bayan da s**a ba shi domin cimma wannan nasara.
A ƙarshe, ya roki addu’o’in ‘yan Najeriya, tare da fatan Allah ya sanya wannan tafiya ta haifar da alheri ga shi, al’ummar Zamfara da Najeriya baki ɗaya.