Dimokuradiyya

  • Home
  • Dimokuradiyya

Dimokuradiyya Dimokuradiyya Adon Kasa. Youtube Channel: Dimokuradiyya TV An kafa Jaridar Dimokuraɗiyya ne Domin Tabbatar Da Mulkin da Jama'a s**a zaɓa da kansu Dan su Amfana.
(3)

Jarida ce da a ka kafa domin samar da labarai da dumi-dumin su, dambarwar siyasa, binkicen kwakwaf, da Nishadi, domin tabbatar da mulkin da jama'a s**a zaba don su amfana.

A wani al’amari mai ban mamaki gabanin zaben kananan hukumomi a jihar Ribas, a ranar 30 ga watan Agustan 2025, jam’iyyar...
03/08/2025

A wani al’amari mai ban mamaki gabanin zaben kananan hukumomi a jihar Ribas, a ranar 30 ga watan Agustan 2025, jam’iyyar APC da PDP sun hada kai don samar da ƴan takarar shugaban kasa na bai daya a fadin kananan hukumomin 23.

Ka daina hana Tinubu aiki, kaje ka nemi aikin yi - APC ga El-Rufa'i Jam'iyyar APC ta buƙaci tsohon Gwamnan Jihar Kaduna ...
03/08/2025

Ka daina hana Tinubu aiki, kaje ka nemi aikin yi - APC ga El-Rufa'i

Jam'iyyar APC ta buƙaci tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma jagora a jam'iyyar haɗaka ta ADC Mallam Nasir El-Rufa'i, da ya daina gangamin yaƙin neman zaɓe, tare da jiran shekarar 2027 kafin yin yaƙi da jam'iyya mai mulki.

Sakataren jam'iyyar APC na ƙasa Sanata Ajibola Basiru ya yi wannan kiran a ranar Lahadi a lokacin da yake jawabi ga Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya.

Basiru yana mai da jawabi ne ga wasu kalaman da El-Rufa'i a ranar Asabar a jihar Sokoto, inda a wurin El-Rufa'i ya gargadi ƴan Najeriya da kada su zaɓi APC a zaɓen Shugaban ƙasa, inda yace ƙasar zai yi wahala ta sake haƙurin shekara hudu a ƙarƙashin mulkin Tinubu.

Wa'adi ɗaya kaɗai zan yi idan aka zaɓe ni Shugaban Ƙasa - Peter ObiƊan Takarar Shugaban ƙasa na jam'iyar LP a shekarar  ...
03/08/2025

Wa'adi ɗaya kaɗai zan yi idan aka zaɓe ni Shugaban Ƙasa - Peter Obi

Ɗan Takarar Shugaban ƙasa na jam'iyar LP a shekarar 2023 Peter Obi ya jaddada cewa yayi alƙawarin yin wa'adi ɗaya, yana mai jaddada cewa shekara huɗu zai yi idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasa a 2027.

Obi ya bayyana haka a a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X q ranar Lahadi, yana mai jaddada cewa zai yi adalci a shugabancin sa.

Da yake bada misali kan shugabannin da s**a yi wa'adi ɗaya kuma s**a kawo wa'adi mai kyau, Obi ya bada misali ga tsohon Shugaban ƙasar Amurika Abraham Lincoln da John F. Kennedy da kuma shugaban ƙasar Afrika ta kudu Nelson Mandela.

An ba Gwamnan Naija awa 48 ya buɗe gidan rediyon da ya kulle ko ya fuskanci fushin dokaƘungiyar kare haƙƙin bil'adama SE...
03/08/2025

An ba Gwamnan Naija awa 48 ya buɗe gidan rediyon da ya kulle ko ya fuskanci fushin doka

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama SERAP ta baiwa Gwamnan jihar Naija Umar Bago awa 48, inda take neman ya cire dokar da gwamnatin sa ta ɗauka na kulle gidan rediyon Badeggi FM, gidan rediyon ƴan kasuwa da ke Minna.

A wata buɗaɗɗiyar takarda da ta fitar mai kwanan watan 2 ga Agusta, Mataimakin Daraktan SERAP Kolawale Oluwadare, ƙungiyar ta nuna kulle gidan rediyon a matsayin karya doka, tana kira ga gwamnan da ya maido wa hukumar lasisinta gami da fasa rushe ta.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci Gwamnan da ya kawo ƙarshen kai farmaki ga Sha'aibu Badeggi, mai mallakin gidan rediyon mai mita 90.1 da sauran Ma'aikatan hukumar.

INEC ta gargaɗi al'umma kan sayar da ƙuri'un su a zaɓen Gwamnan OsunHukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta yi kiran ƙar...
03/08/2025

INEC ta gargaɗi al'umma kan sayar da ƙuri'un su a zaɓen Gwamnan Osun

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta yi kiran ƙarin haɗin gwiwa da dukkanin masu ruwa da tsaki domin magance damfarar ƙuri'u a zaɓukan da za'a gudanar a faɗin ƙasar.

Kwamishinan zaɓe na Jihar Osun Mutiu Agboke ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga Manema labarai a ranar Lahadi, inda ya bayyana rashin jindadi kan yawaitar matsalar ta'addanci a rana da bayan ranar zaɓe.

Ya yi kira ga al'umma da su tashi tsaye domin yin abinda ya dace domin ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya.

03/08/2025

Shugaban Hafsoshin Tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa dakarun tsaron Najeriya na samun gagarumar nasara wajen kakkabe manyan yan ta’adda da suke addabar jihohin Arewacin Najeriya.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su cigaba da basu cikakken haɗin kai tare da gargaɗin masu taimakawa ƴan ta’adda da abinci, mashin, kayan gyara da mai, da su dakata da wannan aiki ko su fuskanci hukunci iri ɗaya da ƴan ta’addan.

🎥Saurari cikakkiyar tattaunawar.

Sojojin Najeriya sun yi ajalin ƴan ta'adda, sun ƙwato mak**ai A ƙoƙarin ta na magance ta'addanci a Najeriya, Rundunar So...
03/08/2025

Sojojin Najeriya sun yi ajalin ƴan ta'adda, sun ƙwato mak**ai

A ƙoƙarin ta na magance ta'addanci a Najeriya, Rundunar Sojin Najeriya ta hallaka ƴan ta'adda da dama tare da k**a guda 4.

A wani samame da ta kai tsakanin 30 ga watan Yuli zuwa 2 ga watan Agustan 2025 a fadin kasar, ta kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su da kamo mak**ai da sauran kayayyakin ta'addanci.

Rundunar sojin dai sun kai samamen a jihohin Borno da Taraba da jihar Delta da Ondo da sauran jihohi

APC,  ADC, Ko PDP wa kuke ganin zai lashe zaɓen 2027?
03/08/2025

APC, ADC, Ko PDP wa kuke ganin zai lashe zaɓen 2027?

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya raba kayan agaji ga gidaje 500 da ambaliyar ruwa ta af...
03/08/2025

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya raba kayan agaji ga gidaje 500 da ambaliyar ruwa ta afkawa a jihar Adamawa a ranar Lahadin da ta gabata.

GWAMNAN JIHAR KADUNA SANATA UBA SANI YA RABA TAKI TIRELA 400 KYAUTA GA MANOMAN JIHAR A KALLA DUBU 100,000.Gwamna Uba San...
03/08/2025

GWAMNAN JIHAR KADUNA SANATA UBA SANI YA RABA TAKI TIRELA 400 KYAUTA GA MANOMAN JIHAR A KALLA DUBU 100,000.

Gwamna Uba Sani wanda ya bayyana hakan a lokacin rabon takin da aka gudanar a Kaduna a yau asabar, ya ce kowane wanda ya samu damar cin gajiyar shirin zai karbi buhu biyu na takin kyauta.

Jihar Kaduna ta kasance jiha daya tilo da kananan manoma ke karbar takin zamani da sauran muhimman kayan masarufi ba tare da tsada ba, zai zama abin alfahari da wannan manufa ta farko ta manoma, musamman ga al’ummominmu masu rauni da marasa galihu.

Ga manoman mu ‘yan kasuwa, wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen noma da sana’o’in noma, muna samar da taki buhu 10 ga kowane manomi akan ragin kashi 40 cikin 100 ma'ana za su samu akan farashin Naira N30,000 kan ko wane buhu, domin tallafawa samar da ayyukan yi, da daidaita farashin kayayyaki a kasuwannin bayan fage,” in ji Gwamna Sani.

Ya jaddada cewa, wannan matakin na kare manoma daga asara daga kwari da cututtuka ga amfanin gona, da kuma munanan yanayi masu alaka da sauyin yanayi.

Dalilin da ya sa muka ware biliyan 712 domin gyara filin jirgin saman LegasMinistan Jiragen sama Festus Keyamo ya bayyan...
03/08/2025

Dalilin da ya sa muka ware biliyan 712 domin gyara filin jirgin saman Legas

Ministan Jiragen sama Festus Keyamo ya bayyana cewa matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na kashe biliyan 712 domin gyara filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos, ya zama dole domin zamanantar da shi domin ya ɗauki fasinjojin da ake buƙata.

Keyamo ya bayyana haka a shafin sa na X a wata sanarwa da ya fitar kan ƙididdigar yadda za'a kashe kuɗin a filin jirgin saman, inda ya ce gyara filin jirgin za'a canja mashi tsari gaba ɗaya.

Keyamo yace an gina filin a shekarar 1979 wanda ya sanya ya tsofe saboda amfanin da ake da shi, inda za'a gyara komai a cikin sa.

Zaɓen 2027 zai zama mai haɗari da rashin tabbas - Mahdi Shehu Ɗan Gwagwarmaya Mahdi Shehu ya gargadi ƴan Najeriya cewa z...
03/08/2025

Zaɓen 2027 zai zama mai haɗari da rashin tabbas - Mahdi Shehu

Ɗan Gwagwarmaya Mahdi Shehu ya gargadi ƴan Najeriya cewa zaɓen 2027 zai zama mai haɗari da rikice-rikice da rashin tabbas.

A cikin wani rubutu da ya fitar a shafin sa na X a ranar Lahadi, ya bayyana yanayin yadda siyasar ta maida hankali a matsayin mai haɗari da kuma rashin tabbas.

Shehu yace haɗuwar ƴan siyasa zai maida yanayin mai tashin hankali, inda ya bayyana cewa, waɗanda s**a kasance abokan gaba yanzu sun haɗe domin samun mulki, kuma yana cewa ƴan siyasa kada su yi tunanin wani abu da ba faɗa ba.

Address

No. 218 Mogadishu Layout Kaduna City Center Ahmadu Bello Way Kaduna

800273

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dimokuradiyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dimokuradiyya:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share