Madogara TV/Radio

  • Home
  • Madogara TV/Radio

Madogara TV/Radio Kafar watsa labarai ce mai zaman kanta da aka samar domin yada labarai da rahotanni na gaskiya. 08148279729
(2)

Kafar watsa labarai mai hasko labarai masu amfanarwa.

16/08/2025

Tattaunawa: Alhaji Sa’idu Mustapha, daya daga cikin Dattawan Basawa ya yi mana Karin haske dangane da zaben cike gurbi dake gudana a mazabar Basawa dake karamar hukumar Sabon Garin Zariya ta jihar Kaduna.

Ga abin da yake cewa:

Zaɓen cike gurbi a jihar Kaduna: an riƙa rabon naira dubu 5 ana dangwala ƙuri'aA ci gaba da kaɗa ƙuri'a a zaɓen cike gur...
16/08/2025

Zaɓen cike gurbi a jihar Kaduna: an riƙa rabon naira dubu 5 ana dangwala ƙuri'a

A ci gaba da kaɗa ƙuri'a a zaɓen cike gurbi dake gudana a mazaɓar Basawa dake ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna, rahotanni sun yi nuni da cewa ana siyan ƙuri'u akan naira dubu 5 har zuwa naira dubu goma.

Mata da dama sun shaida ma wakilinmu cewa; su dai sun karɓi naira dubu biyar (naira dubu 5) sun dangwala wa wata jam'iyya, saboda a cewarsu ko ba su karɓi kuɗin ba, an kammala zaɓe.

Kazalika masu sanya ido kan zaɓen sun shaidawa wakilinmu cewa akwai wuraren da naira dubu goma (10,000) aka riƙa rabawa.

Har wala yau wani matashi ya ce mana shima an masa alƙawarin kuɗi, kuma ya dangwala amma ya ji wayam har yanzu ba a ba shi kuɗin ba.

16/08/2025

ZAƁEN CIKE GURBI A JIHAR KADUNA: Tsohon ɗan majalisar tarayya mai wakilar ƙananan hukumomin Giwa da birnin Gwari a ƙarƙashin jam'iyyar APC, Shehu Balarabe Baƙauye ya yi mana ƙarin haske dangane da zaɓen dake gudana a mazaɓar Basawa dake ƙaramar Hukumar Sabon Gari, inda ya ce ganin yadda zaɓen ke gudana yana tabbacin APC za ta lashe zaɓen.

Zaben cike gurbi dake gudana a mazaɓar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. Wakilinmu ya labarto mana...
16/08/2025

Zaben cike gurbi dake gudana a mazaɓar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. Wakilinmu ya labarto mana cewa zaɓen na gudana cikin lumana.

Sai dai wasu sun yi zargi wata jam'iyya da siyan duk ƙuri'a ɗaya akan naira dubu biyar (N5000). A yayin da wasu s**a yi ƙorafin cewa an ce za a ba su kuɗi idan s**a yi zaɓen, amma har yanzu shiru ba a ba su kuɗin ba bayan sun dangwala.

Zaben Cike Gurbi: Na ji dadin yadda ‘yan jam’iyyar APC s**a fito, muna fatan lashe zaben, in ji Alhaji Sani SASA yayin a...
16/08/2025

Zaben Cike Gurbi: Na ji dadin yadda ‘yan jam’iyyar APC s**a fito, muna fatan lashe zaben, in ji Alhaji Sani SAS

A yayin aka soma zaben cike gurbi na dan majalisar jiha na mazabar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna a ranar Asaba, daya daga cikin jigon jam’iyyar APC a karamar hukumar Sabon Gari ya jinjinawa ‘ya’yan jam’iyyar.

Alhaji Muhammad Sani SAS, mashawarci na musamman ga shugaban karamar hukumar Sabon Gari, Hon. Jamilu Albani ya nuna jindadinsa bisa yadda ‘ya’yan jam’iyyar APC s**a fito kwansu da kwarkwatansu wajen kadawa jam’iyyarsu kuri’a a zaben cike gurbin da yake gudana.

Alhaji Sani ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da manema labarai a lokacin da yake zagayawa domin ganewa idonsa yadda zaben ke gudana.

A bisa haka ne, ya yi fatan cewa jam’iyyarsu ne za ta yi; “nasara a wannan zabe da ikon Allah”, in ji shi.

“wannan zabe ana gudanar da shi cikin lumana ba tare da tashin hankali ba, ga mutane sun fito sosai suna gudanar da zaben su”, ya tabbatar.

“Fatan mu kuma APC ce za ta yi nasara, ko yanzu aka tsaida kada kuri’a za mu ci zabe”, ya tabbatar.

ASUU ta ce ba ta son bashin gwamnati, A Biya Malamai Hakkokinsu da aka rike
16/08/2025

ASUU ta ce ba ta son bashin gwamnati, A Biya Malamai Hakkokinsu da aka rike

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai
16/08/2025

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

ADC ta zargi APC da shirin tafka maguɗi a zaɓen cike gurbi na KadunaKafin zaɓen cike gurbi da za a gudanar a gobe, rnana...
15/08/2025

ADC ta zargi APC da shirin tafka maguɗi a zaɓen cike gurbi na Kaduna

Kafin zaɓen cike gurbi da za a gudanar a gobe, rnanar Asabar a majalisun tarayya da na jiha a Jihar Kaduna, jam’iyyar adawa ta African ADC ta zargi jam’iyyar mai mulki ta APC da daukar ’yan daba da kuma karɓar biliyoyin naira daga cikin jihar da wajen ta domin yin magudi.

Zaɓen cike gurbin zai gudana ne a mazaɓar tarayya ta Chikun/Kajuru da mazaɓar tarayya ta Zaria/Kewaye, da kuma mazaɓar majalisar jiha ta Basawa.

Waɗannan zarge-zargen na ADC sun haifar da musayar maganganu tsakaninta da gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar APC.

Kwamishinan ƴaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki da ya mayar da martani yana cewa zarge-zargen na ADC “ba su da tushe kuma abin dariya ne.”

Mintuna 42 da s**a wuceHezbollah ta gargaɗi gwamnatin Lebanon kan jefa ƙasar ''yaƙin basasa''Jagoran ƙungiyar Hezbollah ...
15/08/2025

Mintuna 42 da s**a wuceHezbollah ta gargaɗi gwamnatin Lebanon kan jefa ƙasar ''yaƙin basasa''

Jagoran ƙungiyar Hezbollah ya gargaɗi gwamnatin Lebanon kan cewa matsa wa ƙungiyar ta ajiye makamanta nan da ƙarshen shekara, zai iya jefa ƙasar cikin yaƙin basasa.

Naim Qassem ya ce shirin, wanda ya biyo bayan matsin lamba daga Amurka, kamar miƙa wa Isra'ila Lebanon ne.

Kafin yaƙin da aka yi tsakanin Hezbollah da Isra'ila a bara, ana hasashen ƙungiyar mai goyon bayan Iran na da makaman da s**a fi na sojin Lebanon.

Duk da tsagaita wutar da aka yi a watan Nuwamba, Isra'ila ta ce za ta ci gaba da kai hari kan Hezbollah har sai ta ajiye makamanta baki ɗaya.

Dokokin hana zancen dare da aka kafa a wata unguwa a KanoAl'ummar unguwar Sharada da ke cikin ƙaramar hukumar Birni a ji...
15/08/2025

Dokokin hana zancen dare da aka kafa a wata unguwa a Kano

Al'ummar unguwar Sharada da ke cikin ƙaramar hukumar Birni a jihar Kano, sun bijiro da wasu dokoki 29 domin tsaftace halayyar mutane da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.

Daga ciki dokokin akwai dokar hana zance ko hirar dare tsakanin sauraryi da budurwa da ma hana zance a cikin mota sannan ka da masoya su wuce ƙarfe 10 dare suna zance.

Wannan matakin, a cewar mahukuntan yankin, ya fito ne sakamakon damuwar da ake fuskanta kan taɓarɓarewar tarbiyya da ƙaruwar matsalolin tsaro, da kuma rashin bin ƙa'idojin al'ada a tsakanin matasa masu neman aure.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, tare da sauran mambobin Tawagar Sadarwa ta Ƙasa, sun ziyarci aiki...
15/08/2025

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, tare da sauran mambobin Tawagar Sadarwa ta Ƙasa, sun ziyarci aikin gina babbar gadar sama mai tsawo a Eke-Obinagu Junction, a kan hanyar Enugu zuwa Abakaliki, da kuma aikin gina mahaɗar hanya ta Abakpa Junction Interchange, wanda ake sa ran zai rage cunkoson ababen hawa a kan titin Enugu-Onitsha Expressway da titin Enugu-Abakaliki.

15/08/2025

Babban Labari: Ƴanbindiga sun yi garkuwa da matafiya 11 a Kamaru.

Wace hanya kuke ganin za'a matsalar tsaro?

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madogara TV/Radio posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Madogara TV/Radio:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share